ADDINI (BAUTA) DA MAGUZANCI (MARASA ADDINI)

Book in text:

 

ADDINI (BAUTA) DA MAGUZANCI (MARASA ADDINI)
العبودية واللادينية بلغة الهوسا

 

Mawallafi
Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha
د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة


Fassara
European Islamic Research Center (EIRC)
المركز الأوروبي للدراسات الإسلامية
& Hashim Muhammad Sani

Wanda ya bibiyi fassara

Faiz Shuaib Adam


../../../../../../../Documents/MY%20SITES%20&%20PROJECTS/PROJECTS%20&%20SITES/ISLAML 
www.islamland.com

 

 

../../../../../../../Documents/MY%20SITES%20&%20PROJECTS/PROJECTS%20&%20SITES/ISLAMLAND/profil

 

 

ADDINI (BAUTA) DA MAGUZANCI (MARASA ADDINI)
 

GABATARWA:

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya aiko da Muhammad me gargadi da bishara, da kuma kira zuwa ga Allah da iznin sa da fitala me haskakawa, ya daukaka sahabban say a basu falala me girma, tsira da amincin Allah su tabbata ga Muhammad da iyalensa da sahabban sa aminci me tarin nunki da yawa. Bayan haka:

Hakika na karanta wannan littafi na dakta Abdurrahman dan Abdulkarim al shaihah, kuma naji dadin dukkanin abunda aka rubuta acikin sa layi bayan layi saboda kasancewar sa yana maganin mafi hadarin matsalar zamani wanda aka fi sani da nesanta daga ibada, wannan nisantar kuwa yanada dalilai da rassa da wanda yafi nesa, daga cikin su akwai wanda nisanta ne na karyata samuwan Allah kamar yadda abun yake cikin kungiyar mutanen da aka fi sani da suna "la diniyya" watan babu addini da " la adriyya" watan bamusan komai ba game da Allah da samuwar duniya da abunda ke cikinta da akidar " la rububiyyati" watan babu Allah wanda yayi halittu kuma yake renon su, daga cikin su akwai nesanta daga addini saboda al'ada yadda mutane ke wayan gari babu abunda suka sa agaba sai tara dukiya da alfahari da yawan yara suna masu damuwa da aiwatar da sha'awar su da sakaci wurin kusantar Ubangiji.

Dangane da nesantar akidar " la diniyya" ya hadu da wasu daga cikin mabiyan sa da yawa wanda muka tattauna dasu kuma na bayyanar masu da cewa lallai wannan akida ta ladiniyya addinice a karon kanta, sun ki amsan dukkanin addinai gabaki dayan su saboda kudurcewar su cewa dukkanin su babu wani dalili a bayyane da yace ayi su, sai dai sunyi imani da samuwan Ubangiji na wannan duniya sai dai kuma yabar mutane baya tare dasu,[1] wannan sun samar ma kansu wani addini na musamman wanda ba addini bane na Allah, sannan kuma na samu cewa abunda sukayi tarayya dashi a tsakanin su shine fadin su cewa sun zo duniya daga wurin khalifa wand aba musulunci bace, da haka ne sukayi ma musulunci hukunci da cewa ba addini bane na gaskiya sakamakon karatun su akan addinin kiristanci.

            Shi kuma akidar " la adriyya" basu gasgata ba ko kuma karyata samuwan ikon Allah, suna masu fadin cewa bamu gani wani dalili ba da idanun mu wanda zasu tabbatar da haka, bazamu iya sanin hakikanin mafarin dan adam ba, amma sai dai sunyi imani kai tsaye da ingancin canzawan duniya ta hanyar canzawan zamani wanda ake kira da suna " addarawidiyya" wanda suke ikirarin cewa tun kafin shekaru miliyan dari shida mutum ya kasance biri, sannan suka sanya yakini game da imani da hakan koda kuwa dalilai na ilimi sun karyata hakan, hakika fashewar zamanin kambiriyan( wani fashewa ne da akayi a zamanin wanda mafiya yawan namomin daji suka bayyanu wanda zasu dau tawon lokaci basu bacewa sama da shekaru miliyan 20 zuwa 25) ya karyata haka da wasu daga cikin fannin ilimomi na kimiya kamar su ilimin kimiyyar halittu na doron kasa wanda ba mutane ba da ilimin hayayyafa da ilimin tsoffan dabbobi na duniya, wanda suka tabbatar da cewa lallai bishiya danada nau'o'i masu banbanta da junan su sannan akwai nau'o'i wanda wanda suke karewa baki daya bawai canzawa sukeyi ba, kuma lallai cancanzawan yana cikin nau'in bishiyan ne kata bawai daga wani nau'in yake ban a daban kamar yadda bakteriya yake cancanzawa daga wannan dabba zuwa zuwa dabba wanda wannan cancanzawan da yakeyi yananan dai akan sunan san a bakteriya, sannan kuma bazaka taba gani ba har Abadan cewa kifi ya canza daga kifi ya koma wata dabba wacce take rayuwa a wajen ruwa, kuma hakika an ambaci cancanzawa na halitta cikin alkur'ani tun shekaru dubu daya da dari hudu na hijira cikin fadin Allag madaukai cewa ( kuma hakika mun halicce mu masu caccanzawa (14)) domin ya tabbatar mana da bin abu daki da daki, kamar yadda yaro yake zama babban mutum daki da daki, kamar yadda yaron zaki yake fitar da hakoran fida masu karfi daki bayan daki, binciken darawin bai zama ilimi ba, bazata iya amsan gyararrraki ba ko kuma gwaji ko kuma ta zama me amsar maimaici ta yadda zata iya shiga karkashin manhaji na ilimi. Duk wanda yake cewa babu wani addini, sannan duniyar wasu tsari ne na dokoki ke tafiyar da ita sai muce masa wanene ya rubuta wannan dokoki yadda duniyar zata kasance, dokoki da tsari ba komai bane face siffatawa, dokoki basa halattan komai sannan bazasu iya tara dukiya ba daga ilimin lissafi, babu wani cin karo tsakanin imani da Allah da kuma bayanun duniya ta hanyar tsarin ilimin kimiyya da fasaha, har Abadan tsari ko kuma doka bazai taba halitta ba.

Kira daga zuciya domin dawowa zuwa ga addinin Allah:

Akwai wanda ya karyata bautan Allah yana me cewa, ance azabar lahira anayinta ne ga mutumin da ya sabawa Ubangiji duniya shin wannan Magana beci karo ba da siffar Allah ta rahama? Sai mu bashi amsa da cewa kamar yadda kake azabtar da duk wanda yayima ta'adi cikin iyakokinka da abubuwan da ka mallaka na ababen duniya, shin baka tsoratarwa da kuma kai mutum kotu kasa akulleshi na tsawon wani lokaci sakamakon abunda ya aikata na laifi?! Shin ka taba karantawa a wani rana cewa kofofin rahama wanda aka budewa ko wani me tuba na hakika! To wallahi babu wanda zai halaka a cikin wuta sai me girman kai da bijirewa, shine wanda yaki bautawa Allah me rahama ya kuma ki amsan dukkanin alherai baki dayan su, ko kana cewa ne cinye kananan kifi da manyan kifi keyi zaliumci ne sai muce maka da manyan kifi basa cinye kananan da duniya ta cika da kifi da kasuwanni sannan kuma da tsarin yanayi da duwatsu sun lallace da doron kasa, komai yana tafiya ne da hikima wacce ba'asan iyakarta ba sai wanda ya halicci duniya da halittu baki dayan su, ka koma ga Ubangijin k aka amshi nasiyya ta da nake maka daga cikin zuciya ta, bazaka taba kamo tsayin dutse ba sannan kuma bazaka fasa kasa ba da takunka domin tsananin karfin ka, kasan girman Allah me rahma wanda ya halicci duniya da rayuwar lahira, kabi hanyar gaskiya hanyar addinin muslunci wanda yake cikamakon addinai wanda sukazo daga Allah, me yuwa ranan bijiro da ayyuka zaka hadu da sakamako me kyau cikakke daga Allah me rahama, shine ya shigar da kai aljanna madawwamiya cikin rayuwa me dadi, kada kace ka wadatu da bin addini idan ka rike ginshikai na dabi'u, shin dukkanin hankula ne sukayi ittafi akan rarrabe ayyukan alheri daga ayyukan ta'addanci ko kuma hankula sun samu sabani akan haka gwargwadon banbance banbance na zamani da garuruwa wurin sanin gaskiya daga al'adu batattu, shin ka taba gani ba acikin addinai ba dokoki na ginshikin halaye na kwarai, shin kanason bin abunda zuciyar ka ke raya maka ne da barin bin hukunce hukuncen Allah? Me yasa kake biyayya ga dokoki wanda aka wajabta maka su daga majalisai masu kirkiran dokoki, wanda zai iya zama ya daurema waninka gindi wurin aikata aikin ta'addanci, ina rantsuwa da Allah alfasha be yaduba a doron kasa da take hakkokn mutane face domin barin shari'ar Allah da akayi, ina me rantsuwa da Allah da za'a ba marasa addini dama da iko da sun rusa dukkanin wuraren bauta da masallatai da ginin coci, ka tuna abunda ya faru ga masu addinai na kuntata masu da akayi da kuma daidaita su a lokacin shuyu'iyya, kada kayi inkarin falalar Allah akanka da inkarin hakkokin sa na Allantaka, kada kace lallai Allah masani kuma me bada labara ya manta damu ko kuma yayi nisa ga dan adam[2], ka manta ne a lokacin rashin lagiyan ka wanda yake baka lafiya ya kuma yaye maka rashin lafiya masu cutarwa, wanda yake amsa maka addu'o'in ka kuma ya yaye maka damuwar ka, ya kuma azurta ka da wurin zama me kyau ya kuma baka mata da zuri'a na gari, kuma da zai jarabeka da wani abu zakaga cewa hakan alheri ne gareka da yan adam, ka bautawa ubangijinka wanda ya halicci rana da wata da taurari masu haske, ya kuma sanya su suna masu tasbihin dukannin su cikin jujjuyawan da sukeyi, rana bazata iya riske wata ba haka kuma babu wani rigegeniya tsakanin sararen sammai, ubangijin ka wanda ya halicci kassai ya kuma sanya duwatsu a cikinta domin su danneta su kara mata nauyi kada ta rika kadawa da mutanen kanta, ya kuma halicci kogi wanda ruwan cikinsa me dandanon gishiri ne da kuma kogi wanda ruwa cikin sa me dandanon dadi ne domin mu rika shansa cikin natsuwa, duk zakayi inkarin wannan abubuwa dukan su kace addinin ka hankali zaka rika bi, bah aka bane ina rantsuwa da ubangijin ka'aba lallai acikin addinin musulunci akwai amfani da hankali.

 

                                                            AHMAD AL-'AMIR

                                     

 

 

Da sunan Allah me rahma me jin kai

            Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga manzon Allah da iyalan sa da sahabbansa baki daya.

Ka rika kallon musulunci da manhajin sa ne kada ka rika kallon musulmi da halayansa da ayyukan sa

Bauta wani abune na fidira wanda Allah ya halicci mutun dashi wanda bazayyiwu ba a raba mutane dashi baki daya ba, mutum dole ka sameshi cikin daya daga abubuwa biyu ta bangaren bauta babu na ukun s kodai mutum ya zama me bautan Allah shi kadai dayi masa biyayya a gareshi sai ya samu kwanciyar hankali da natsuwa zuciyar sa, Allah madaukaki yace: " kace Allah nake bauta mawa shi kadai yake nufa da addini na (14) ku bautawa duk abunda kuka ga dama koma bayan sa, kace lallai masu asara wanda sukayi asarar kawunan su da iyalan su ranan tashin alkiyama to lallai wannan shine asara bayyananne (15) sunada inuwa na wuta daga saman su da kasansu, da wannan ne Allah yake tsoratar da bayinsa dashi, yaku bayina kuji tsoro na (16) suratu zumar

Ko kuma ya zama me bautan wasu alloli batattu nason zuciyan sa ko kuma gumaka ko dukkanin wani abun da ake bauta masa da sunan bauta ko dukiya ko kuma kundin tsarin mulki ko wasu mutane sai zuciyar sa ta sangarce ya kasa samun kwanciyar hankali da natsuwar zuciya, sai yayi asarar duniyar sa da lahiran sa, Allah madaukaki yace: " shin bakaga wanda ya riki son zuciyar sa ba ta zaman masa abun bautar sa sai Allah ya batar dashi akan ilimi ya kuma shafe masa jinsa da zuciyar say a sanyawa ganin sa shamaki wanene zai iya shiryar dashi koma bayan Allah shin bazakuyi tunani ba da tuna hakan" suratul jasiya ayata 23.

Sayyid kudub Allah ya masa rahama yana cewa: babu makawa dole sai da bauta! Idan ba'a bautama Allah ba shi kadai za'a bautawa wanin Allah… Ita bautan Allah shi kadai tama mayar da mutane su zama masu yanci da daraja da daukaka… ita kuma bauta ga wanin allah tana cin yancin mutane ne da karamar su da falalar su. Sannan kuma taci dukiyoyin su da maslahar su ta kayayyakin duniya daga karshe.

Bata a halin kaskanta rai da biyayya wacce babu soyayya acikinta wacce ta hada bawa da ubangidan sa, irin wannan bauta abun kimace ga zukatan mutane sannan kuma kunnuwa basason jinta, ita kuma bauta sabanin wannan wanda ta gabata ta kunshi karama da daukaka da yanci a lokacin da akeyinta ga mahaliccin duniya da abunda ke cikinta, hakika musulunci yazo da yanci na asali wanda ake samunta ta hanyar bauta ga Allah shi kadai, wannan bauta wacce take tsara rayuwa baki dayanta babu zalunci ko kuma cin amana a tattare da ita, Allah madaukaki yace: " lallai Allah yana umurtan ku da ku mayar da amana ga masu ita kuma idan zakuyi hukunci tsakanin mutane kuyi hukunci na adalci" suratun nisa'i ayata 58.

Babu cin dukiyan mutane da barna ko kuma sata ko fince ko cin riba, Allah madaukaki yana cewa: " yaku wanda sukayi imani kada ku rika cin dukiyoyin ku a tsakanin ku da barna sai dai idan kasuwanci ne wacce akwai yarda a tsakanin ku" suratun nisa'i ayata 29.

Babu keta mutuncin mutane da zubzr da jinanen su Allah madaukaki yana cewa: " wanda basa kiran Allah tare da wani abun bauta na daban sannan kuma basa kishe ran da Allah ya haramta kashewa sai da gaskiya saannan kuma basa aikata zina duk wanda ya aikata hakan zai tarar da sakamakon sa " suratul furkan ayata 68                                     

Zaka rika biyan hakkoki a cikinta kamar yadda Allah yayi umurni da hakan cikin fadin sa cewa: " ku bautawa Allah kada ku mashi tarayya da wani abu sannan kuma iyaye ku kyautata masu da yan uwanku da marayu da miskinai da makwabta cikin yan uwan ku da makwabta na zaman takewa da aboki makusanci da matafiyi da abubuwan da kuka mallaka na bayi, lallai Allah bayason marowaci me yawan alfahari" suratun nisa'i ayata 36

Ana yafewa me laifi acikinta da kuma kau da kai ga mai kuskure kuma yafiya da fagara ne ya cikata, kamar yadda Allah yayi umurni da haka yace: " ka rika yafiya da umurni da kyakyawan aiki sannan kuma ka kawar dakai daga jahilai" suratul a'araf ayata 199.

Lallai mutum cikin rayuwar mu ta yau yana son yanci budaddiya wacce ba'a masa iyaka da komai ba ya aikata abunda yake so da barin abunda bayaso ya aikata sabanin musulmi wanda bayason yanci irin wannan yanason yanci ne wacce zata kasance cikin bautan Allah madaukaki wanda sune sukafi cancanta da hakan saboda irin wannan bauta itace wacce take canza su zuwa ga cikakken yanci na hakika wacce babu wanda zai zama yanada iko akansu, mutum bazai taba samun wannan yanci ba face ta hanyar bauta ta gaskiya wacce manzannin Allah suka zo da ita wanda ake aiko su lokaci bayan lokaci me tsayi domin su sabantama mutane addinin su kuma su mayar dasu zuwa ga ubangijin su mahaliccin su kuma kada ya zama suna da hanzari ga Allah bayan hakan, Allah madaukaki yace: " hakika mun aika manzo ga ko wace al'umma da cewa su bautawa Allah sannan kuma su nisanci dagutai daga cikin su akwai wanda Allah ya shiryar dasu sannan kuma daga cikin su alkwai wanda bata ya tabbata akan su, kuyi tafiya cikin kasa ku kalli yadda karshen masu karyata manzanni ya kasance" suratun nahli ayata 36.

Lallai yanci a mahangar kasashen turawa a wannan zamani tamu fitana ne da hayaniya wanda me kudi yake zalumtar talaka sannan me karfi ya zalumci mara karfi da keta mutuncin mutane a cikinta da cin dukiyan mutane da kasha rayuka da salwantar da hakkoki da wajibobi wannan itace yancin dabbobi da hukuncin namukan daji wanda Allah ya zargi duk wani wanda yaki bauta masa ya kuma tafiyar da rayuwan sa yadda zuciyar sa keso da biyema sha'awar sa, allah madaukaki yana cewa yana me bayanin haka: " hakika mun halittama jahannama mutane da aljanu dayawa, suna da zuciya wanda basa tunani da ita kuma suna da idanuwa wanda basa gani dasu, sannan suna da kunnuwa wanda basa ji dasu, wa'innan kamar dabbobi suke koma kace sunfi dabbbobi bacewa kuma wannan sune rafkanannu" suratul a'araf ayata 179.

Lallai matsalolin duniya wacce take fuskata ayau na zalumci da yaki da karayan tattalin arziki da zaman takewa da matsalolin siyasa babban dalilin daya jawo su shine nisantar bautan Allah da akayi na hakika wanda ya shar'anta hukunce hukunce aciki wanda zasu gyara rayuwan mutum da al'umma, da riko da hakan ne da aiki dashi kuma rayuwan dan adam ke kyau duniya da lahira sannan kuma rashin aiki da ita da wasu suke yi yake haifar masu da matsaloli da annoba, sai dai sun canza abunda yafi alheri da abu makaskanci ta hanyar samar da dokoki da kundun tsarin mulki na mutum wanda kura kuranta sukafi dai dai dinta yawa wanda an gina su ne akan son zuciyan wani mutum da yanayin siyasa wanda yakai su ga hakan, Allah yayi gaskiya cikin fadin sa cewa: " ku saurara kuji me halitta yasan abunda ya halitta kuma shi mai tausayi ne me bada labara" suratul mulk ayata 14.

Lokacin da bautan musulman farko yakasance ga Allah cikin dukkanin bangarorin rayuwan sun a siyasa da zamantakewar su da halayen su da kasuwancin su sai suka suka mallaki duniya baki daya hukuncin su ya kasance mafi alheri ga mutane baki daya babu zalumci da dagawa ko cin hakkokin mutane ko sace arzikin kasa, ya kasance wand aba musulmai bama suna fifita hukuncin musulmai akan hukuncin wasu masu addinai na daban saboda abunda suka gani na adalcin haka, sabanin halin mafiya yawan musulman wannan zamani namu wanda sukayi imani da wani sashi na alkur'ani suka kafurce ma wani sashi, suna bautama Allah cikin abunda suke su ya dace da sha'awar ran su sannan kuma suna bijirema dukkanin abunda ya sabama hakan, sai makiyar su sukayi amfani da haka suka shugabantar masu da mutum me bin son zuciyar sa da rauni imani da son duniya wanda suka samu daman mallake su da amsu mulkin mallaka da wulakanta su, Allah yayi gaskiya cikin fadin sa yana me bayyana wannan hali da cewa: " haka ya kasance ne saboda lallai Allah baya canza wa mutuwa wani hali na ni'ima da suke ciki har sai sun canza halayen su, lallai Allah me ji ne kuma masani" suratul anfal ayata 53.

Hakika mnanzon Allah s.a.w ya tsawatar dasu akan haka inda yace: " wani hali kuke ciki idan abubuwa biyar suka faru a tsakanin ku? Ina me neman tsarin Allah da kada hakan ya riske ku kuna raye….. shuwagabannin su bazasu rika yin hukunci ba bada abunda Allah ya saukar ba face Allah ya daura masu makiyan su wanda zasu rika kwace abun hannun su, basu canza hukunci ba da littafin Allah da sunnar manzon sa face Allah ya sanya kiiyayya a tsakanin su suta azabtar da juna a tsakanin su"[3] hadisi ne ingantacce baihaki da hakim ne suka rawaito shi kuma albani ya inganta shi cikin littafin sahihul targib wattarhib.

Wannan shine halin da al'ummar musulmai zata kasance aciki duk lokacin da suka bar bautan Allah, Allah ne abun neman taimako.

 

Yadda alkur'ani ya kunshi bayanin Halittan duniya da abunda ya kunsa a cikin sa:

Daga cikin abunda hankalin mutum ya damu dashi wurin tunani cikin dukkanin zamani shine bayanin halitta da wanda ya samar da halittan wannan duniya da abunda ke cikin ta wanda aka samar da sakamako na karshe wanda hankali baya amsan hakan saboda kasancewar basusan gaskiyar asalin hakan ba wanda babu wanda zai sanin hakan sai wanda ya samar da halittan duniyar da abunda ke cikinta, alkur'ani yazo da bayanai na hankali wanda dan adam zaiji natsuwa cikin ayoyin alkur'ani wanda suka kunshi wannan batu yana mai bada amsoshin tambayoyin tunanin dan adam akan haka da kuma bayanin halittan farko a cikin duniya da kuma dalilin halittan sa da samar dashi da karshen sa da makomar sa.

 

Farkon halittan dan adam:

ya dace ace farkon wannan babi mu bude shi da fadin Allah madaukaki: " shine farko da karshe da zahiri da badini kuma shine masani ga dukkan komai" suratul hadid ayata 3.

Da kuma fadinsa madaukaki game da kansa cewa: " kace shine Allah shi kadai (1) Allah shine wanda ake nufi da bukata (2) be Haifa ba kuma ba'a haifeshi ba (3) kuma babu wani tamkar a gareshi (4)"

Kuma hakika an tambayi manzon Allah Muhammad s.a.w akan hakikanin halitta da samar dashi lokacin da wasu mutane daga yamen sukazo wurin sa sai sukace masa: munzo wurink ane domin mu samu fahimtar addnin, zamu tambaye ka game dabatun halitta me ya fara kasance wa, sainyace masu: " ya kasane Allah ne sannan kuma kafin sa babu wani halitta, al'arshin say a kasance akan ruwa, sa'annan ya halicci sammai da kassai, sai ya rubuta a lauhil mahafuz duk abun da zai gudana" sahihul buhari, Allah madaukaki yace: " shin wanda suka kafurta basu gani ba cewa sammai da kassai sun kasance a hade sai muka raba su, muka sanya rayuwan komai ya zama daga rayuwa shin bazasuyi imani ba" suratul anbiya'i ayata 30.

            Allah ya halacci duniya sama da kasa kuma sun kasance a hade farkon yanayi, wani akan wani, sai ya raba tsakanin sama da kasa, ya sanya sammai guda bakwai da kassai bakwai suma, ya kuma raba tsakanin saman duniya da kasa da iska, ya sanya ta zama me zubar da ruwa kasa tana fitar da tsirrai, Allah madaukaki yace: " wanda ya kirkiri halittan sama da kasa, idan ya hukunta al'amari ce masa kawai yakeyi kasance sai yakasance" suratul bakara ayata 117. Sa'annan ya halicci Adam baban mutane a cikin aljanna ya sanya mala'iku suyi masa sujjada baki dayan su kuma sukayi sai shedan baban shedanu kadai yaki yi masa sujjadan da aka urumuce sa dashi yayi girman kai daganan ya kulla gaba da hassada ga annabi Adam wanda Allah ya karrama shi da fifitashi akan sa, ya kasance wannan itace farkon adawa tsakanin dan Adam da Iblis baban shedanu, Allah madaukaki yace: " a lokacin da Ubangijinka yace ma nala'iku zan halicci mutum dana tabo (71) idan y agama halittan san a hura masa rai daga gare ni ku fadi kuyi masa sujjada (72) sai mala'iku dukkanin su suka fadi sukayi masa sujjada (73) sai Iblis ne kadai yayi girman kai kuma ya kasance daga cikin kafirai (74) sai Allah yace masa ya kai Iblis me yahanaka yin sujjada ga abunda na halitta da hannuwa na? kayi girman kai ne ko kuma ka sance daga cikin madaukaka ne? (75) sai Iblis yace ni nafi wannan alheri ka halicce ni ne daga wuta shi kuma ka halicce sa ne daga tabo (76) sai Allah yace ma Iblis fita daga cikin wannan aljanna kai korarre ne daga rahamata (77) kuma la'anata ta tabbata akan ka har zuwa ranan tashin alkiyama (78) sai Iblis yace ya Ubangiji n aka sauraramun da rain a har zuwa ranan tashin alkiyama (79) sai Allah yace masa kana cikin wanda aka saurara masu (80) har zuwa wata rana sananniya (81) sai Iblis yace ina rantsuwa da buwayar ka sai na dilmiyar dasu baki dayan su (82) sai dai bayinka daga cikin su tsarkakakku (83) sai Allah yace ina rntsuwa da gaskiya da fadin cewa (84) sai na cika wutan jahannama dakai da duk wani wanda yabi ka baki dayan ku (85) suratu saad.

            Daganan sai Allah ya halittama Adam matansa hauwa'u amincin Allah ya tabbata a gare su domin ya samu natsuwa zuwa gareta kuma ta zama me dauke masa kewa da saduwa domin su kasance farkon tsatson dangantakan mutum, Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani kuji storon Ubangijin mu wanda ya halicce ku daga mutum daya kuma ya halitta daga wannan mutum matar sa, sa'annan ya yada daga tsakanin su mutane maza da mata, kuji tsoron Allah wanda kuke rokon sa bukatun ku kuma kuke sada dangantakar ku domin sa, lallai Allah ya kasance me bibiyan ku a ko wani lokaci" suratun nisa'i ayata 1.

            Aljanna ta zama gidan zaman su kuma ubangijin su ya masu bayani cewa lallai Iblis makiyin su ne saboda haka su kiyaye sa, Allah madaukaki yace: " sai mukace ya Adam lallai wannan makiyin ka ne da matar ka saboda haka kada ya fitar daku daga aljanna sai ka wahalu (117) lallai a cikin ta bazaka ji yunwa ba kuma bazakayi tsiraici ba (118) kuma bazaka ji kishin ruwa ba acikinta ko yin zufa (119)" suratu daha.

            Kuma ubangijin su ya umurce su da ci da morewa da dukkanin wasu abubuwa na ni'ima na cikin aljanna sai wata bishiya guda daya kadai ya hanasu kusantar ta da kuma cinta, Allah madaukaki yace: " sai kuma mukace ya kai Adam ka zauna cikin aljanna da matar ka kuma kuci duk wani abu da kuke so cikin abubuwan cikin ta amma kada ku kusance wannan bishiya sai ku kasance cikin azzalumai" suratul bakara ayata 35.

Sai Iblis ya samu dama da makircin da da yaudaran sa da kawata abubuwan san a fitar da baban mu Adam Amkncin Allah yatabbata agare shi da matar sa daga cikin aljanna bayan ya sanya masu wasiwasin cin wannan bishiyar da ubangijin su ya hanasu cinta, Allah madaukaki yace: " sai shedan yayi masa wasiwasi yace masa ya Adam shin bazan nuna maka wata bishiya ba wanda idan kacita zaka dawwama cikin wannan aljanna da mulki wanda bazai taba karewa ba (120) sai sukaci wannan bishiya nan take sai al'aurar su ta bayya suka rika tsintar ganyayyakin bishiyoyin aljanna suna rufe al'aurar su, Adam ya sabama ubangijin sa sai rayuwan sa da yakeyi cikin aljanna na jin dadi ya lallace (121) sa'annan ubangijin say a zabe sa ya yafe masa kuma ya shiryar dashi (122)" suratu daha.

            Ukubar da akayi ma Adam da matar sa bayan sun sabama Allah da cin wannan bishiya shine fitar dasu daga aljanna da kuma saukar dasu zuwa doron kasa wanda ubangijin su ya halicce ta tun tuni domin ta zama wurin rayuwar su da yaran su kuma ta zama gida na jarabawa, Allah madaukaki yace: " sai mukace ku sauka daga cikin ta baki daya, idan shiriya yazo maku daga gare ni duk wanda ya bi shiriyata to babu tsoro a garesu kuma bazasuyi bakin ciki ba (38) wanda kuma suka kafirta zuka karyata ayoyina wa'innan sune yan wuta suna masu dawwama acikin ta (39) suratul bakara.

Daga lokacin da aka fitar dasu daga aljanna da kuma saukar dasu zuwa duniya sai kiyayya ta fara sai Iblis ya fara aiwatar da tsare tsaren sa wanda yayi alkawari ga Adam da yaran sa bayan sun sauko duniya, Allah madaukaki yace: " Allah yace ya Iblis me yasa baka kasance ba cikin masu sujjada (32) sai Iblis yace bazan kasance me sujjada bag a abunda ka halitta daga tabo (33) sai Allah yace masa fita daga cikin wannan aljanna kai jefaffene daga rahamata (34) kuma tsinuwa ta ta tabbata akanka har zuwa rananr tashin alkiyama (35) sai Iblis yace ya Ubangijina ka sauraramun zuwa ranan tashin alkiyama mana (36) sai Allah yace masa jeka kana cikin wanda aka sauraramawa (37) zuwa ranan alkiyama sananne (38) sai Iblis yace ya Ubangijina tunda ka batar dani sai na rika kawata masu abubuwa na sabo a duniya sannan kuma sai na batar dasu baki dayan su (39) sai bayin ka wanda suka kasance tsarkakakku (40) sai Allah yace wannan itace hanya wanda nake tsaye akanta (41) lallai bayina baka da wani iko akan su sai wanda ya bika cikin batattu (42) kuma lallai wutar jahannama itace alkawari a garesu baki dayan su (43) suratul hijri.

            Mutane sun kasance farkon halitta al'umma daya bayan sunyi yawa sai suka bazama cikin kasa domin neman rufin asiri da neman hanyoyin arziki, Allah madaukaki yace: " mutane sun kasance al'umma daya sai Allah ya aiko annabawa masu bushara da gargadi ya kuma saukar da musu da littafi da gaskiya domin yayi hukunci a tsakanin mutane cikin abunda suka samu sabani akan sa" suratul bakara ayata 213.

            Sai rarrabuwa ta samu da yaduwa cikin fadin kasa sakamakon wannan yawa, ya kasance cikin adalcin Allah shine ya aiko da manzanni ga wannan mutane wanda suka bazu a doron suna masu bushara da gargadi a gare su domin su dawo masu da akidar su sahihiya da addinin sun a asali kuma domin su zama hujja agare su, Allah madaukaki yace: " manzanni masu bushara da gargadi domin kada mutane su zama suna da hujja akan Allah bayan aiko da manzanni, Allah ya kasance mabuwayi me hikima)" suratun nisa'i ayata 165.

            Duk wanda yayima wannan annabawa da manzanni biyayya cikin abunda sukazo dashi daga wurin Allah zai shiga aljanna, wanda kuma ya saba masu yayi girman kai cikin abunda suka zo dashi na gaskiya zai shiga wuta, allah madaukaki yace: " yaku bani Adam idan Annabawa suka zo maku daga cikin ku suna masu karanta maku ayoyi na, duk wanda yayi takawa ya kuma gyara to babu tsoro a garesu kuma bazasuyi bakin ciki ba ( 35) wanda suka karyata ayoyi na suka kuma yi girman kai a gareta wannan sune yan wuta suna masu dawwama a cikin ta (36) suratul a'araf.

            Allah madauki yaka cewa har wayau: " wanda suka kafurce ma ubangijin su sunada azabar wutan jahannama, tur da wannan makowar (6) idan aka jefa su cikin ta zakaji ihun su kamar dan kwayar abu cikin ruwa me yawa (7) kamar zata daidaita su saboda tsananin azabar ta, duk lokacin da aka jefa mutum sai masu gadinta su tambayesu cewa me gargadi bezo maku bane (8) sai suce hakika me gargadi yazo mana sai muka karyata shi mukace Allah be saukar da komai ba kodai baku kasance ba face cikin bata me girma ( 9) kuma suka ce da mun kasance munaji ko muna tunani da bamu kasance cikin yan wutan sa'ir ba (10) sunyi ikirari da zunuban su boni ya tabbata ga mutanen wutan sa'ir (11) lallai wanda suke jin tsoron ubangijin su cikin boyayyen wuri (gaibu) suna da lada da gafara me girma (12) suratul mulku.

            Annabawa amincin Allah ya kara tabbata a garesu sun kasance suna tunatar da mutanen su kiyayyar Iblis akansu na ganin ya canza su daga hanya madaidaiciya wanda Allah ya yrdan masu da ita ya kuma bayyana masu ita ta hanyar annabawan sa da manzannin sa, yana batar dasu ne ta hanyar sanyasu bin son zuciyar su da sha'awar zuciyoyin su da kuma kawata masu bata, Allah madaukaki yace: " yaku bani Adam kada shedan ya fitineku kamar yadda ya fitar da iyayen ku daga aljanna ya cire masu tufafin su domin ya bayyanar masu da al'aurar su, lallai yana ganin ku shi da jama'ar sa ta yadda bakwa ganin sa, lallai mun sanya shedanu su zama waliyyai ga wanda basa imani (27) suratul a'araf.

 

HIKIMAR HALITTAN MUTUM:

a hankalce da dabi'a an sani cewa dan adam baya lalata shekarun sa da lokutan sa da kokarin sa da kudin sa wurin kirkira ko kuma samar da wani abu face sai da hadifin jawoma kansa wata fa'ida ko kuma dan kawar da wata cuta ga kansa, wannan shine abunda kowa ya sani kuma muke gani duk wata kirkire kirkire ta dan adam yana yin sa ne domin tabbatar da wata maslaha ba tare da dub aba zuwa ga cewa wannan maslahar me kyau ce ko kuma mara kyau bace, haka shima Allah madaukaki wanda shine yake da masalai mafiya dacewa da daukaka be halicci wata halitta ba kawai domin wasa kuma be barsu bah aka kawai kara zube, Allah madaukaki yace: " shin kuna tsammani ne mun halicce ku ne kawai domin wasa sannan kuma bazaku dawo ba zuwa gare mu? (115) Allah sarki na gaskiya ya daukaka da tsarkaka daga haka, babu wani abun bauta sai shi, ubangijin al'arshi alkarim (116) suratul muminun.

            Be halicci wannan duniya ba da abun dake cikin sa ba domin wasa da barkwanci, Allah madaukakinya tsarkaku daga yin haka face ya halicce su ne domin wata hikima kokoluwa Allah madaukaki yace: " kuma bamu hakicci sama da kasa ba da abunda ke cikin su domin wasa ba (16) da munso yin wasa ne da hakan da mun rike hakan daga wurin mu da mun kasance masu aikata haka (17) suratul anbiya'i.

            Kuma Allah be halicci mutum ba wanda ya daukaka shi akan dukkanin halittu ba khalifa a a doron kasa ba face domin ya tsayu wurin aikata wajibobin wadda aka kayyade mashi su wanda aka halicce sa domin su, Allah ya abayyana hakan cikin fadin sa cewa: " ban halicci mutum da aljani ba face dan su bautamun (56) bana butakar arziki daga wurin su sannan kuma bana bukatar su ciyar dani 957) lallai Allah shine azurtawa ma'abocin karfi me tsanani" suratu zariyat.

            Ya halicce su sannan kuma ya tanadar masu da dukkanin abunda suke bukata na rayuwan su ya kuma aiko masu da manzanni domin suyi rayuwa irin wacce yake so ba yadda suke so bas u, rayuwa wacce ta dace da shari'ar sa da manhajin sa wanda ya yardan masu dashi- Allah shine ma'abocin kololuwan misali- mutum baya yarda wani mutum dan uwan sa ya gindaya masa sharudda hakanan cikin tafiyar da rayuwan sa cikin abubda beda mallakin komai akai, saboda haka Allah yana halittan abunda yaso kuma ya aikata abunda yaso, Allah madaukaki yace: " ubangijin ka yana halittan abunda yaso ya kuma zabi wanda yaso, basu ke da zabi ba, Allah madaukaki da buwaya ne dangane da abunda suke masa shirka" suratu kasas ayata 68.

            Wannan shine hadafin na halittan wannan duniya da abunda ke cikinta na abubuwa da halittun wanda ake gani da wanda ba'a gani domin mutum ya tabbatar da bauta ga Allah a tsakanin su, sannan kuma yayi amfani da dukkanin abunda ke cikin ta domin ya masa jagora wurin sanin Allah da kuma taimaka masa akan bautan Allah, Allah be halicci sub a domin ya rika samun Karin karfi dasu ko kuma su rika jawo masa wani amfani ba ko kuma kawar masa da wani cutarwa ba, sune ma suke da bukatawa gareshi, ya kasance mawadaci daga garesu kamar yadda Allah ya bada labarin haka cikin fadin sa cewa: " yaku mutane kune fakirai zuwa ga Allah, shi Allah shine mawadaci me godiya (15) idan yaso zai tafiyar daku ya zo da wasu halittu sababbi (16) wannan ba wani abu bane mabuwayi agun Allah (17) suratu fadir.

            Duk wanda ya tabbatar da bauta a gare shi ya rabautu da abunda ya masa alkawari na ni'ima dawwamamme ta har Abadan, duk kuma wanda ya kasance bawan kansa da son zuciyar sa da shedan to yana cikin azabar wuta madawwamiya har Abadan, Allah madaukaki yace: " lallai wanda suka kafirta daga cikin ma'abota littafi da mushrikai suna cikin wutan jahannama suna masu dawwama acikinta, wannan sune mafiya sharrin halittu (6) lallai wanda kuma sukayi imani sannan kuma suka aikata ayyuka na kwarai wannan sune mafiya alherin halittu (7) sakamakon su a wurin ubangijin su shine aljanna wanda koramu suke gudana a karkashinta suna masu dawwama acikinta har Abadan, Allah ya yarda dasu sannan suma sun yarda dashi, wannan shine sakamokon wanda yaji tsoron ubangijin sa (8) suratul bayyinah.

 

MATAKAN HALITTAN JINSIN MUTUM:

Alkur'ani ya ambaci matakai na halittan mutum yadda Allah madaukaki yake cewa: " shine wanda ya kawata halittan komai, sannan ya kirkiri halittan mutum ne daga tabo (7) sa'annan ya sanya tsatson sa na asalin sa ya kasance daga wani ruwa wulakantacce (8) sa'annan ya daidaita halittan say a kuma hura masa rai daga ransa, ya kuma sanya maku ji da gani da tunani, kadan ne masu godiya akan haka (9) suratul sajada.

            Halittan mutum be kasance ba kamar yadda wasu suke ikirari cewa ya sau ne daga canzawar wata halitta ta daban, Allah madaukaki yace: " hakika mun halicci mutum cikin sura mafi kyawu" suratu tin ayata 4.

Sannan ya sanya halittan mutum yaci gaba da kasancewa mataki bayan mataki har zuwa dawwamar sa a aljanna ko kuma a wuta, hakika alkur'ani ya sawwara hakan cikin matakai na ban mamaki da burgewa takaitattu wanda malamai suka kasa wasafta rayuwan mutum cikin hikima daga farkon sa har zuwa karshen sa dukda dunbin ilimin da aka basu a cikin kalmomi kididdigaggu, cikin wasiftawa me fasaha da hikima wanda yake nuna gaskiyar wannan alkur'ani da abunda ya zo dashi, fadin Allah madaukaki cewa: " hakika mun halicci mutum daga ruwan maniyyin adam wanda aka halicce sa daga tabo (12)sa'annan muka sanya shi ya zama gudan maniyyi a wani wuri na musamman ke bantacce (13) sa'annan muka sanya wannan gudan miniyya ya zama gudan jinni sa'annan muka sanya wannan gudan jinni ya koma tsoka muka kara sanya wannan tsoka ta koma kasha sai muka rufe wannan kasha da nama daganan kuma muka kirkiri halittan sa zuwa wani fasali na daban, mulki da isa da daukaka ya tabbata ga Allah mafi kyawun me halittu (14) sa'annan lallai kun kasance bayan haka zaku mutu (15) sa'annan lallai ranan alkiyama za'a tashe ku ( 16) suratul muminun.

Wannan matakan kuwa sune kamar haka:

 1. Samar da mutum daga rashin sa:

farkon mutum babu shi sai Allah ya samar dashi daga rashin sa wanda acikin haka kuwa akawai dalilai cikakkun akan ikon tayar da mutane bayan mutuwar su, saboda duk wanda ya samar da mutum daga rashin sa lallai yanada ikon dawowa dashi bayan ya mutu ya dadaddage hakan ma yafi zama sauki akan yadda ya samar dashi daga rashin sa, Allah madaukaki yace: " shin labara yazo ma mutum na wasu tsayin lokuta wanda babu wani abmaton sa a wannan lokaci (1) hakika lallai mun halicci mutum daga gudan maniyyi wanda muka cudanya shi da maniyyin mace dana miji domin mujarabashi sai muka sanyashi ya zama me ji da gani (2) suratul insan.

 

 1.  Rayuwa a cikin mahaifiyar sa:

a wannan mataki mutum yana bin wani canze canze da matakai har sai angama cika halittan sa sannan a hura masa rai wanda zata motsa shi ya fito cikin siffar sa wacce Allah ya halicce sa akansa kamar yadda Allah ya bayyana cikin ayar da ta gabata, Allah madaukaki yace: " yana halittan ku acikin mahaifiyar ku halitta bayan halitta mataki bayan mataki cikin duhu guda uku, wancan shine ubangijin ku shine me cikakken mulki babu wani abun bauta sai shi kadai, to dan me kuke bautawa tare dasu abubuwan a tare? (6) suratu zumar.

Hakika Allah ya tanadar ma mutum wasu abubuwa wanda zasu taimaka masu wurin rayuwa a cikin mahifiyar sa kamar kafofin nunfashi da na abinci da sauran abubuwa na girman sa wanda zasu hanashi girma, Allah madaukaki yace: " ashe bamu halicce ku ba daga wani ruwa wulakantacce (20) sai muka sanya shi a wani wuri kebantace (21) har zuwa wani lokaci sananne (22) sa'annan muka kaddara rayuwan sa, madalla da masu kaddarawa hakan (23) suratul mursalat.

 

 1. Rayuwar sa a doron duniya:

Wannan itace mataki ta daukan nauyi na aikata ayyukan wajibobi wanda aka daura masa da kuma masa jarabawa ta yadda Allah madaukaki ya halittama mutum wasu gabbai na ji da gani da hankali wanda zai iya fayyace gaskiya da karya ta hanyar su da kuma sanin abubuwa masu amfani da masu cutar wa, Allah madaukaki yace: " Allah ya fitar daku daga cikin mahaifiyar ku baku san komai ba sai ya sanya maku ci da gani da tunani koda zaku gode masha (78) suratun nahli.

            Ya haliccesa cikin sura me kyau ya kuma sanya masa wasu gabbai ajikin sa wanda yake amfani dasu wurin cin amfanin alheran wannan duniya ya kuma halitta masa wasu abubuwa cikin jikin sa wanda zasu gina masa jiki, Allah madaukaki yace: " shin baku gani ba cewa lallai Allah ya hore maku dukkanin abubuwan da suke cikin sammai da kassai ya kuma cika maku ni'imomin sa akanku na bayyane da na boye, daga cikin mutuane akwai wanda suke jayayya da Allah ba tare da ilimi ba ko wata dalili ko littafi me haske (20)" suratu lukman.

            Kuma kasancewar Allah be halicce sub a face don su bauta masa ya kasance daga cikin tausayin say a aiko masu da manzanni ya kuma saukar masu da littattafai domin su bayyana masu yadda zasu bauta masa su kuma masu jagoranci zuwa ga hanyar gaskiya domin su bi wannan hanyar da kuma nuna masu hanyar sharri domin su guje shi, Allah madakaki yace: " bamu aiko da manzanni ba face dan su zama masu bushara da gargadi, duk wanda yayi imani kuma ya gyara to babu tsoro akan su kuma bazasuyi bakin ciki ba (48) suratul an'am.

            Ya kuma halittama mutum wannan duniya da abunda ke cikinta ya kuma sawwake masa amfani dasu domin ya raya ta da shuka da noma da sana'a da dukkaknin wani hanyar rayuwa domin ya more mata ya kuma zama ya taimaka masa wurin bautan Allah da kadaita shi, Allah madaukaki yace: " shine wanda yasanya maku abubuwan da suke cikin kasa sawwake a gare ku, kuyi tafiya a doronta kuma kuci daga cikin arzikinta, kuma a gare shi zaku koma (15) suratul mulku.

            Sannnan kuma domin duniya da abunda ke cikinta su kasance wuri yalwatacce domin mutum ya rika tunanin da izina cikin ikon mahaliccin sa sai hakan ya kara masa imani da gasgatawa, Allah madaukaki yace: " lallai acikin halittan sammai da kassai da jujjuyawan dare da rana da jirgin ruwan da yake tafiya a kan teku da abun da zai amfanar da mutane da abunda Allah ya saukar daga sama na ruwa wanda ya raya kasa dashi bayan kekashewarta da abunda ya watsa akanta na dukkanin ababen dake tafiya akanta da tafiyar da iska da girgije wanda yake kai komo tsakanin sama da kasa akwai ayoyi ga mutane masu hankali (164) suratul bakara.

 

Dalilan hankali wanda suke nuni akan lallai za'a tayar da mutane bayan mutuwar su a cikin alkur'ani:

Duba da cewa maganar tayar da mutane bayan mutuwa wacce ta girgiza da shagaltar da kwakwalen mutane, sai wanda imani bai shiga zuciyar sa ba yayi inkarin haka, alkur'ani ya bayyana cewa lallai wannan batu ba sabon abu bane hakan ya dade tun fil azal,sai Allah madaukaki yace: " wanda suka kafirta sunyi zaton cewa lallai fa baza'a tayar dasu ba bayan mutuwar su, kace masu bah aka bane ina rantsuwa da ubangijina sai an tayar dasu sannan kuma za'a baku labarin abunda kuka aikata hakan abune mai sauki agun Allah (7) suratul tagabun.

            Hakika hujjojin da wanda suka karyata tayar da mutane bayan mutuwar su suke nema agun annabawan su wanda zai tabbatar masu da hakan abune wanda yake nuna girman kan su da alfahari idan bah aka bas u kalli yanayin halittan kawunan su kawai ya ishesu, Allah madaukaki yace: " idan ana karanta masu ayoyin mu bayyanannu basu da wani hujja sai fadin su cewa ku zo mana da iyayeyn mu idan kun kasance masu gaskiya (25) suratul jasiya.

            Kasancewar karyata tayar da mutane bayan mutawar su hanya ce ta wasiwasi wanda shedan ke bi wurin canza mutane daga imanin su ya kasance dayawa daga cikin ayoyin alkur'ani suna kara tabbatar da hakikanin kasancewar Allah da ikon sa akan tayar da mutane sai su karama mutum kaimi wurin tunani akan asalin sa, Allah madaukaki yace: " mutum yana cewa yanzu idan mun mutu za'a tayar damu kuma darayukan mu (66) shin mutum bazai tuna ba cewa lallai mun halicce sa gabanin rashin kasancewar sa a bakin komai ba (67).

             A cikin tunanin mutum da hankalin sa ya sani cewa duk wanda ya iya kirkiran wani abu to lallai yana da ikon iya kirkiran wanin sa- Allah shine mafi kyawun wurin kololuwan buga misali- wanda ya samar da mutum bayan babu shi yana da ikon ya sake tayar dashi ya dawo dashi bayan ya kasance mutum, Allah madaukaki yace: " shine wanda ya fara kirkiran halitta sa'annan zai dawo da ita wanda dawowa da itan yafi masa sauki akan kirkiranta, shine wanda yake da kololuwa wurin buga misali a sammai da kassai kuma shine mabuwayi me hikima (27) suratul rum.

            Ayoyin alkur'ani sun iya su gamsar ga duk mutumin daya bashi da tsaurin riko na addini da hukuncin hankalin sa da zurfi wurin bin fidirar sada kuma nisantar da ita daga abubuwa masu tasiri na waje daga cikin wannan ayoyi akwai:

 • Tunanin asalin mutum da samuwar sat un farko duk wanda ya samu ikon halitta tun farko yanada ikon dawowa da ita, Allah madaukaki yace: " yanzu mutum baya ganin cewa lallai mu muka halicce sa daga maniyyi sai gashi ya zama me jayayya bayyananne (77) yana buga mana misali bayan ya manta halittan sa, yana cewa wanene zai raya kasha bayan ya dagwargwaje (78) kace masa wanda ya kirkira halittansa a farkon al'amari shine wanda zai rayashi bawan dagwar gwajewar sa, kum ya kasance masani game da kowace halitta (79) suratu yasin.
 • Tunana akan matakai na halittan mutum, Allah madaukaki yace: " mutum yana tunani cewa za'a barsa ne kara zube (36) ashe be kasance ba guda bane daga maniyyi wanda aka kiyaye (37) sa'annan ya zama gudan jinni sai aka halicce sa aka kuma daidaita shi (38) sai ya sanya ya zama mace dana miji (39) shin wanda yayi haka bashi da ikon ya tayar da matattu (40) suratul kiyama.
 • Tunani akan raya kasa kesashishiya ta yadda Allah ya fitar da tsirai daga gareta bayan ta kasance babu komai akanta babu wani alamar rayuwa tattare da ita, Allah madaukaki yana cewa: " daga cikin ayoyin sa zakaga kasa kesashashiya idan muka saukar da ruwa akanta sai kaga ta kunbura ta ta fashe ta fitar da tsirrai, lallai wannan wanda ya rayata zai tayar da matattu, lallai ya kasance me iko akan komai (39) suratu fussilat.
 • Tunanin cikin halittan wannan duniya da abunda ya kunsa wanda yafi girma ga al'amarin halittan mutum duk wanda ya halicce sa lallai bazai gazaba wurin tashin wanda suka mutu wanda idan basu wuce girman kwayar zarraba daga gareshi, Allah madaukaki yace: " shin basu gani ba cewa lallai Allah wanda ya halicci sammai d kassai wanda bai gajiba wurin halittan su cewa bashi da iko wurin tayar da matattu tabbas shi me iko ne akan komai (33) suratul ahkaf.
 • Tunanin baccin mutum da tashin cewa hakan mutuwa ce karama wacce rayuwa ke zuwa bayanta, idan haka ne mutuwar mutum itace mutuwa babba wacce itama rayuwa zai biyo bayanta, Allah madaukaki yace: " Allah shine wanda yake kasha rayuka da kuma wanda bata mutu ba a lokacin baccin ta, sai ya rike ran da aka rubuta mata mutuwa sai ya sake sauran rayukan zuwa wani lokaci sananne, lallai acikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani (42)" suratul zumar.

Sa'annan Allah ya bayyana wa masu karyata tashi bayan mutuwa wani abu na daban wanda zasu rika fankama shi wanda shine cikakken ikon sa wacce babu wani abu da zai gagareta wurin tayar da mutane baki dayan su bayan mutuwar su tun daga kan annabi Adam har zuwa tashin alkiyama acikin keftawan ido da umurni guda daya, al'amarin say a kasance idan yana son abu ya kasance ce masa yake kawai kasance sai ya kasance, Allah shine yake da mafi kololuwan misali, acikin rayuwan mu tayau zakaga ewa kana da iko da dan kwayar abu ka haskaka bigari guda daya baki dayan sa, Allah madaukaki yace: " halittan ku da tayar daku bai kasance ba sai kamar tayar darai guda daya ce, lallai Allah me ji ne kuma me gani (28) suratul lukman.

Ayoyin alkur'ani dukkanin su abun tunani ne akan su da lura da izina dasu kuma Allah yayi gaskiya day ace: " hakika mun saukake alkur'ani domin ayi zikiro dashi shin akwai me wa'aztuwa da hakan (40)" suratul kamar.

 

 1. Rayuwar barzakhiyya:

itace rayuwar da kowa zayyita bayan mutuwa kafin ayi tashin alkiyama, mutuwa ba ita bace karshen rayuwan mutum za'a iya cewa ita farkon rayuwan mutum na hakika, yadda daganan ne mutum zai koma wata sabuwar rayuwa ta daban wacce ake kira da suna rayuwar barzakhiyya har zuwa lokacin da Allah zayyi umur ni da tashin duniya daganan ne babu wani abun da zai saura sai abunda Allah yaso ya saura, Allah madaukaki yace: " sai ayi busa cikin kaho sai duk abunda suke sammai da kassai su suma sai abunda Allah yaga daman tsayawar su, sa'annan kuma sai akara yin wata busar ta daban sai kagansu tsatsaye suna jira (68) suratul zumar.

 A cikin wannan mataki mutum zai kasance matacce a duniya rayayye a wata duniya ta daban ko cikin azaba ko kuma cikin ni'ima gwargwadon ayyukan sa a duniya, kuma hakika Allah ya bayyana hakan cikin fadin sa agame da fir'auna da mutanen sa wanda suka karyata sakon Allah aka nutsar dasu cikin ruwa: " wuta itace za'a rika bijiro ma da ita safiya da maraice ranan alkiyama kuma ace ku shigar da mutanen fir'auna a zaba me tsanani (46)" suratul gafir.

Bayan haka kuma sai ayi busa cikin kaho karo na biyu ( busar tayar da mutane) dumin tanar da tashin alkiyama da tayar da mutane zuwa ga hisabi sai mutane su dimauci saboda abunda sukeji da gani na tsanani, Allah madaukaki yace: " yaku mutane kuji tsoron Allah ubangijin ku lallai girgizan tashin alkima abu ne babba (1) ranar da zaku ganta kowace uwa tane jifar da abun renon ta sannan zakaga ko wace me ciki tana haifar da abunda ke cikinta zakaga mutane cikin maye amma bam aye bace kawai azabar Allah ce me tsanani (2) suratul hajj.

Daganan ne tsarin duniya zai gushe baki dayan sa rana da kasa da taurari da hanyoyin cikin ta, Allah madaukaki yace: " idan rana tayi duhu aka jefar da ita (1) kuma idan taurari suka fado sukayi duhu suma (2) kuma idan aka nade duwatsu (3) kuma idan aka aka bar rakumar masu ciki wanda suka shiga watannin haihuwar su aka gudu (4) kuma idan aka tattara dukkanin halittu (5) kuma idan koguna suka kafe suka bushe (6) kuma idan aka hada mutane na kwarai da junan su sannan mabarnata da junan su suma (7) kuma idan aka tambayi yarinyar da aka birne ta da ranta (8) cewa akan wani laifi aka kasha ki (9) kuma idan aka baje littattafai aka ba kowa littafin sa a hannun sa (10) kuma idan aka yaye sama aka nadeta (11) kuma idan aka rura wutar jahimu (12) kuma idan aka kusanto da aljanna ga mutanen ta (13)" suratu takwir.

 

 1. HISABI:

Allah zai tayar da dukkanin halittun sa mutane da tsuntsaye da dabbobi sai ya tara su domin masu hukunci a tsakanin su a farfajiyar ranan kiyama domin a ciki masu hisabin su agaban me adalci baza'a zalumci mutane ba da komai, Allah madaukaki yace: " zamu shinfida mizanin awo na gaskiya ranar alkiya kuma baza'a zalumci rai da komai ba, idan ya kasance tazo mana da kwatankwacin abun cikin kwalln dabino na aiki ne zamu auna shi ya ishemu muyi mata hasabi akan sa (47)" suratul anbiya'i.

            Za'ayima ko wace al'umma hisabi da shari'ar da Allah ya aiko masu dashi ta bakin manzon sa, sai asakama mumini a kuma hukunta wanda ya karyata, Allah madaukaki yace: " a ranar da zamu kira ko wace al'umma da shugabanta duk wanda muka bashi littafin sa da hannun dama to wannan sune wanda zasu rika karanta littafin su kuma baza'a zalumce suba da kwatan kwacin tsilin abun kan kwallon dabino (71) wanda kuma ya kasance makaho a wannan duniya to a lahira ma zai kasance makaho kuma zai zai bace hanya (72)" suratul isra'i.

            Sai Allah ya sakawa mutane zalumcin su a tsakanin su, kamar yadda Muhammad manzon Alllah s.a.w ya bayyana haka cikin fadin sa cewa: " shin kun san wanene fallasashe? Sai suka ce: fallasashe a cikin mu shine wanda bashi dirhami ko kuwa kaya, sai yace masu: lallai fallasashe cikin al'ummata shine wanda zaizo ranar alkiyama da salla da azumi da zakka, amma zai zo ya zagi wancan yayima wancan kazafi ya kuma ci kudin wancan ya zubar da jinin wancan ya duki wancan, sai aba wancan cikin ladar sa da wancan idan ladan suka kare kafin agama biyan su sai a dauko zunuban su a daura masa daganan sai a jefa shi cikin wuta" sahihu muslim

            Daga cikin cikan adalcin Allah shine madaukaki shine dabbobi da sauran halittu suma za'a masu hukunci a tsakanin su, saboda haka ne aka kira wannan rana ranan hukunci, manzon Allah s.a.w yana cewa: " tabbas za'a mayar da hakkoki zuwa ga masu ita hatta akuya mara kaho zata rama tunkurin ta da akuya me kaho yayi mata" sahihu muslim.

            Idan aka gama hukunci tsakanin dabbobi sai allah yace masu ku zama kasa, a wannan lokaci ne kafiri zai ce kaice na dana zama kasa nima bayan yaga abunda ya tabbatar da halakar sa dashi, Allah madaukaki yace: " lallai muna maku gargadi game da azaba wacce take kusa a ranar da mutum zai duba abunda ya aiwatar da hannuwan sa sai kafiri yace kaice na dana zama kasa nima (40) suratun naba'i.

            Bayan haka sai mutane su kaso gida biyu wanda babu na ukun su, yan aljanna da ni'ima da yan wuta da jahim zuwa rayuwa ta har Abadan wannan shine asara ga mutanen da suka karyata manzanni batattu, saboda haka ne mutum sai yayi aiki yayi tunani domin gujewa wannan asara, Allah madaukaki yace: " a ranar tashin alkiya ranar ne za'a rabu (14) wanda sukayi imani kuma suka aikata ayyuka na kwarai suna cikin aljanna ana masu ni'ima (15) wanda kuma suka kafirta suka kuma karyata ayoyin mu da haduwar lahira wannan suna cikin azaba tsundum (16)" suratu rum.

 

 1. GIDAN LAHIRA:

muminan da suka gasgata manzannin su kuma suka raya lokutan su cikin biyayya ga Allah kuma sukabi umurnin sa sannan kuma suka nesanci abubuwan dayayi hani dasu zasu shiga aljanna ma'anbociya ni'ima wacce take cike da bubuwan na ni'ima wanda ido baitaba ganin suba sannan kunne bait aba jin suba zuciya ma bata taba tunanin suba zasu tabbata cikin wannan rayuwa har abada kamar yadda Allah ya fad cewa: " a cikinta suna da abubuwan da duk sukayi marmari suna masu dawwama acikinta, ya kasance alkawari akan ubangijin ka abun tambaya (16) suratul furkan.

Zasu rika ci da sha a cikinta basazu yi datti ba ko wari sannan kuma bazasu rika yin fitsari ba da bayan gida da majina ba, abun da sukaci zai rika fita ne ta hanyar gyatsa da zufa me kamshi kamar miski, babu rashin lafiya ko annoba, me kira zai kirasu yana ce masu ku zauna a cikinta kuna masu lafiya bazakuyi rashin lafiya ba har Abadan sannan zaku rayu babu mutuwa a cikinta har Abadan sannan zaku kasance samari a cikinta har Abadan bazaku tsufa ba, kuma za'a ta baku ni'ima a cikinta bazaku taba shan wahala ba har Abadan, kamar yadda manzon Allah s.a.w ya bada labara. Muslim ne ya rawaito hadisin.

Su kuma kafirai wanda suka rika karyata wa da jayayya da manzannin su da abunda sukazo dashi suna cikin wuta zasu dawwama acikinta, Allah madaukaki yana cewa: " wanda suka kafirta suna da wutan jahannama bazasu mutu ba a cikinta sannan kuma baza'a sassauta masu abazarta ba, da haka ne muke sakama duk wanda ya kafurta (36) zasu rika ihu a cikinta suna cewa ya ubangijin mu ka fitar damu zamuyi aikin kwarai ba irin wanda muka aikata ba abaya, shin bamu rayaku ba tsawon lokaci da wanda zayyi tunani yakeyin tunani a ciki sannan kuma masu gargadi sun zo maku, ku dandana azzalumai basu da wani mataimaki (37)" suratu fadir. Suna cikin azaba wacce bata yankewa, Allah madaukaki yace: " lallai wanda suka kafirta da ayoyin mu da annu zamu jiyar dasu wuta, duk lokacin da fatarsu ta zagwanye da wuta zamu sake masu wata fatar sabuwa domin su dandani azaba, lallai Allah ya kasance mabuwayi me hikima (56)" suratun nsa'i.

Abincin su a cikinta shine kaya wacce ake kira da suna (dari'u) itace mafiya muni cikin nau'o'in kaya, Allah madaukaki yace: " basu da wani abinci face kayar dari'u, bata sanya kiba sannan kuma bata gusar da yunwa (6)" suratul jasiya.

Da kuma bishiyar zakkum wacce take fita daga cikin wutan hajim wacce da za'a saukar da reshenta guda daya duniya da ta bata masu kayayyakin rayuwan s, Allah madaukaki yace: " lallai bishiyan zakkum, abincin masu sabo ne kafirai, kamar mai ce wacce take zagwanyar da kayan ciki saboda zafinta" (suratul dukkan ayata 43-46).

Ruwan kurji da zufa da jinin dake fita daga namar su shine abinshan yan wuta, Allah madaukaki yana cewa: " basu da wani mai taimakon a ranan ko abincin sai ruwan kurji babu wanda ke cin wannan abinci sai kafirai (suratu hakkah ayata 35-37).

Ruwan shansu kuma shine ruwa me tsanannin zafi wanda yake tsunka hanji da zagwanye fatar jikin su, Allah madaukaki yace: " za'a shayar dasu da ruwa me tsananin zafi wanda zai tsunka masu makoshin su" suratu Muhammad ayata 15.

Tufafin su kuwa a cikin wuta anyi shi ne da dalma na wuta an dinka masu shi kamar yadda Allah ya bayyana haka cikin fadin sa: " wanda suka kafirta an dinka masu kaya daga wuta, za'a rika zuba masu ruwa me tsananin zafi daga kawunan su (19) zata rika tsuntsunka masu kayan cikin su da zagwanar masu da fatar jikin su (20) sannan kuma suna da kuraku na karfe (21) duk lokacin da suka so fita daga cikinta saboda tsananin bakin ciki sai a dawo dasu ace masu ku dandani azabar wutar da kuke karyatawa (22)" suratul hajji.

Daganan ne rayuwan ta hakika zata fara a gidan da ake dawwama da tabbata har Abadan babu mutuwa, manzon Allah s.a.w yace: " idan aka shigar da yan aljanna cikin aljanna, aka shigar da yan wuta cikin wuta sai me kira yayi kira yace: yaku mutanen aljanna ku dawwama acikinta babu mutuwa, yaku mutanen wuta ku dawwama acikin ta kuma babu mutuwa" sahihul buhari, sannan kuma tirmizi ya rawaito shi da Ibn hibban kuma wannan lafazin nashi ne.

Mutum me hankali shine wanda yake aiki tukuru domin ya tsira a wannan rana sai ya fara yima kansa hisabi yaga cewa yana kan tafarki na gaskiya da addinin na gaskiya ko kuma a'a?, Allah madaukaki yace: " lallai Allah baya zalumtar mutane da komai sai dai mutane su suke zalumtar kawunan su (44)" suratu yunus.

BUKATAR BAWA GA ALLAN DA YAKE BAUTAMAWA.

Mutum yana da bukata ga abunda yake bauta mawa wanda suke sadaukar masa da rayukan su da jikin su gareshi, kamar yadda gangan jiki yake da bukata na abubuwan da zasu taimaka masa na rayuwa kamar ci da shah aka rai take da bukata ga mahalicci wanda zasu bauta mishi da kuma mika masa bukatun su zuwa gare shi da kankantar da kawunan su a gaban sa suna masu jin natsuwa da aminci a hannun sa, mutum ba tare da bautan Allah ba kamar dabba ne basu da wani abu muhimmi daya wuce farjin su da cikin su wanda wannan abun anan suke karar da rayukan su akai, Allah madaukaki yace: " lallai Allah zai shigar da wanda sukayi imani kuma suka aikata aiki na kwarai aljanna wanda koramu suke gudana a karkashin ta, wanda suka kafirta suna jin dadi da cin abinci kamar yadda dabbobi suke cin abinci, wuta itace makomar su (12) suratu Muhammad.

            Rashin ta zai sa rayuwar mutane ya zama kamar na dabbobin daji yadda me karfi zai zalumci mara karfi me kudi yaci hakkin talaka sannan kuma baza'a rika tausayin yara ba da girmama manya, baza'a rika taimakon mara lafiya ba ko kuma gajiyayye rayuwa ce wacce zata kasance na kudi ko sakayya komai anayin sa ne bisa maslaha da kuma arziki kawai.

            Lallai rai mutum an halicce ta ne akan fidiran gasgata wa da kuma sanin akwai mahaliccinta da wannan duniya, wacce zata bauta masa wanda hakan malamai suke kiran sa da suna (sha'awa da yunwar addini) Allah madaukaki yace: " ka tsayar da fuskarka ga addini mikakke fidirace wacce Allah ya halicci mutane akanta babu canji da halittan Allah wannan shine addini tsayayye amma dayawa cikin mutane basu sani ba (30)" suratul rum.

Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " babu wani yaro da ake haifan sa face ana haifansa ne akan fidira iyayensa sune suke mayar dashi bayahude ko kuma kiristan ko kuma me bautan wuta" sahihul buhari.

            Dan adam koda kuwa ya canza akan wannan fidirar da Allah ya halicce sa da akai zakaga cewa wannan fidira tana nemar wani karfi da iko wanda zata rika nufar sa dashi lokacin neman biyan bukatarta da halin kunci, wannan kuma shine abun da ake lura dashi daga mutanen da suka gabace mu wanda suka rike wasu abubuwan bauta na taurari ko bishiya ko kuma duwatsu, wannan shawa'a da kwadayi kuwa tana tare da kowani mutum sai dai daga cikin su akwai wanda yake inkarinta saboda girman kai da tsaurin kai, sannan daga cikin su akwai wanda ake tabbatar da hakan kuma yayi imani, wannan hali na sha'awar da kwadayi yana karuwa ne a lokacin da mutum yake hali da damuwa kamar idan mutum bashi da lafiya ko kuma wani abun mummuna ya same shi, zaka ganshi yanajin yana fadin ya Allah ko kuma yana daga kansa zuwa sama yana me tabbatar da samuwar wani karfi ko iko wanda ya gagara wanda zai yaye masa wannan hali da yake ciki, lallai Allah yayi gaskiya cikin fadin sa cewa: " idan wata cuta ta samu mutane sai su kira ubangijin su, suna masu sakankancewa a gareshi sa'annan idan wata rahama ta samesu daga gareshi sai kaga sun koma suna masa tarayya (33)" suratul rum.

            Hakama a lokacin da wani tsanani ya sauka ko kuma wani mummunan abun sai gaskiya ta bayyana kuma kasakancin abubuwan da ake bautamawa koma bayan Allah ya bayyana sai tsarkake Allah ya samu shi kadai da rokon Allah na gaskiya shi ke da mallakar komai kuma shine me iko akan yaye wannan cuta da damuwa ko kuma tsanani, hakika alkur'ani ya suranta wannan yanayi da fadin sa cewa: " idan wani cuta ta samu mutane sai ya kira mu a kwance ko a tsaye ko a zaune amma idan muka yaye masa wannan cuta da damuwa nashi sai ya koma kamar bai taba rokon mu ba akan wata damuwa da cuta data same shi" suratu yunus ayata 13.

            Ko kuma a lokacin da aka mamaye mutum da wani abun da baya so wanda bashi da wani mafita sai wannan karfi na boye wanda yake jinsa a cikin zuciyar sa cewa lallai akwaita tananan kuma zata iya tsiratar dashi, Allah madaukaki yace: " shune wanda yake tsare ku cikin ruwa da waje, har idan kun kasance cikin jirgin ruwa kuna da tafiya da iska tafiya ta daidai sukayi murna da ita sai iska me karfi da tsanani tazo ma wannan jirgin ruwa sai kuma igiyan ruwa ta tazo masu ta ko ina idan suka tabbatar da cewa zata halakar dasu sai su kira Allah shi kadai suna masu tsarkake shi da addini cewa idan ya tsiratar damu daga wannan yanayi zamu zama cikin masu gode masa (22)" suratu yunus.

            Hakika al'ummar da suka gabace mu sun kasance suna rikan gumaka a matsayin abun bauta koma bayan Allah saboda wannan sha'awa da kwadayi da suke dashi na addini wanda Allah ya dora mutane akan sa baki daya, a lokacin da addinin da aka saukar dasu daga sama na gaskiya wacce zasu kosar da wannan fidira ta bauta da aka halicci mutum da ita suka boye masu, sai wannan sha'awar ta mutum ya fara neman wani abun bauta wanda zai kosar dashi hakan sai su dimauce su bace wurin neman abun bauta sai su rike wasu halittun irin su a matsayin abun bauta, Allah yayi gaskiya cikin fadin sa: " lallai abunda kuke kira koma bayan Allah bayi irinku, ku kirasu mugani sai su amsa maku idan kun kasance masu gaskiya (194) suratul a'araf.

            Abun takaicin da damuwa shine wannan abun bautan duk wani hankali da fidira me kyau yana kore su baya yarda dasu irin su duwatsu da bishiya da taurari da dabbobi da farji…. Da dai sauran su, daga cikin abun damuwar shine cikin masu bautan irin wannan abubuwa akwai mutane wanda suke da matsayi babba a ilimi da karantar wa da kuma wayewa sannan kasashe wanda ilimin su yakai wani mataki babba suna ginuwa akan su, Allah yayi gaskiya cikin fadin sa cewa: " sun san zahiri na rayuwan duniya amma kuma game da rayuwan lahiran su gafalallu ne akai (7)" suratul rum.

            Sayyid khudub Allah ya masa rahama yana cewa: mutane basu mallaki su rayu ba ta tare da addini ba! Babu makawa ga mutane daga addini. Wanda ba bautawa Allah shi kadai zasu fada cikin sharrin bautawa wanin Allah; cikin ko wani bangare na rayuwan duniya!

Zasu fada da kawunan su cikin kasakancin son zuciyar su da sha'awar sub a tare da wani iyaka ba ko doka. Daga nan kuma sai su rasa kimar su da daraja da mutum su koma duniyar dabbobi: " wanda suka kafurta suna jin dadi da cin abinci kamar yadda dabbobi ke cin abinci, wuta itace makomar su (12)" suratu Muhammad.

Babu asarar da mutum zayyi da ta wuce yayi asarar kimar sa da darajar sa ta mutum, daganan sai ya koma duniya da rayuwan dabbobi, wannan shine abunda ke faru da zarar mutum ya canza ya bar bautan Allah shi kadai ya koma bautan zuciyar sa da sha'awarsa.

Sa'annan kuma sai su fada cikin mafi sharrin nau'o'I na bautan bayi….. zasu fada cikin sharrin nau'o'in bautan shuwagabanni da sarakuna wanda zasu rika juya su akan dokoki da hukunce hukunce irin nasu wanda suka kirkiro da kansu, bashi da wani ka'ida ko hadafi sai kiyaye maslahar wanda suka kirkiri wannan dokoki da hukunce hukunce ko yaransa masu zuwa bayan sa.

Wannan abu zai kaimu zuwa ga sanin matsayin tsarkake bauta da addini wurin kare rayukan mutane da mutuncin su da dukiyar su, wanda dukkanin wannan abubuwa suke wayi gari basu da wani kariya a lokacin da mutane ke bautama mutane irin su.

DALILAI NA HANKULA WANDA SUKE NUNA KADAITUWAR ALLAH:

Jirgin ruwa zai nutse idan aka samu matuka biyu a lokaci daya, jagorancin yana tarwatsewa idan aka samu shuwagabanni biyu a lokaci daya, kasuwanci yana karye wa idan aka samu mutum biyu kowa yana son samun iko da isa da dukiyar, to idan haka ne ya kake gani ace wannan duniya me girman gaske wanda da za'a samu wani kwayar zarra daga cikinta ya lalace da ta fadi ta nemi gyara da ace akwai wani allah na dabanbayan Allah da an samu sa'insa da jayayya wanda zai haifar barna, Allah yayi gaskiya lokacin da yace: " da ace akwai wani allah acikin sama da kasa bayan Allah da sun lalace, tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin al'arshi daga abunda suke siffatawa (22)" suratul anbiya'i.

            Daga cikin dabi'ar masu tarayya na kamfani ko kuma kungiya shine zakaga suna rigegeniya a tsakanin su wurin samun iko ya zama shine me bada umurni da yanke hukunci a kamfanin ko kuma kungiyar wanda hakan yake bata aiki kuma wannan rigegeniyar shine sababin samun sabani, Allah madaukaki yace: " Allah be rike wani yaro ba kuma babu wani allah a tare dashi, da ace akwai wani allan a tare dashi da ko wani allah ya tafi da abunda ya halitta kuma da wani sashi ya nemi iko akan sashi, tsarki ya tabbata ga Allah daga abunda suke siffatawa (91)" suratul muminun.

            Ko kuma kamar yada sarakunan duniya suke aikatawa tsakanin sun a yaki da fada kowa daga cikin su yana son kawar da mulkin dayan ya zama cewa shi kadai ne sarki, Allah madaukaki yace: " kace da ace akwai wani allah a tare dashi kamar yadda suke cewa da kuwa sun nemi kawar da ikon me al'arshi (42)" suratul isra'i.

            Sayyid kudub Allah ya masa rahama yana cewa fadin Allah cikin wannan aya {Allah be rike wani yaro ba kuma babu wani allah atare dashi} …. Daga nan ne sai yazo da dalili wanda zai kore da'awar su da kuma sawwara ikidar su ta shirka na shashanci da kuma rashin yuwuwar hakan da cewa: {da ko wani allah ya tafi da abunda ya halitta} watan kowa ya rike abunda ya halitta ya zama yanada iko dashi ya juya shi yadda yake so, sai ya zama cewa ko wani bangare a duniya ko kuma ko wani bangare a cikin halittu yanada dokoki nashi na daban wanda baza'a samu wani doka day aba wanda zai rika jujjuya duniya. {da wani sashi ya nemi iko da wani sashi} watan da ya nemi samun galaba akansa wanda zai kwace masa ikonsa na tafiyar da nashi duniyar wanda babu wani doka guda daya da yake tafiyar dashi, dukkanan wannan surori babu su a duniya, wanda kasancewar duniya abu guda yake nuna cewa mahaliccin sa daya ne, sannan samun tsari daya a duniya shima yana tabbatar da cewa me tafitar da duniya daya ne. kowani bangare na duniya yana hade ne da sauran babu cin karo ko kuma sabani a tsakanin su…. {tsarki ya tabbata ga Allah daga abunda suke siffatawa}.

 

 

BAUTA A MUSULUNCI

Musulunci shine addinin dukkanin annabawan Allah da manzannin sa saboda hakikanin musulunci shine mika wuya ga Allah da jayuwa a gareshi da masa biyayya da kuma tsarkakeshi daga shirka( masa tarayya da wani cikin bauta), bauta itace kololuwan matsayi gwargwadon bautan ka ga Allah gwargwadon yancin ka, sannan kuma gwargwadon kaskantanka a gareshi gwargwadon izzar ka a duniya, gwargwadon yardan ka dashi gwargwadon natsuwarka da samun sukuni dakwanciyar hankali, Allah ya sanya ta ta zama daukaka ga Annabawa da manzannin sa gabaki dayansu tun daga kan Nuhu amincin Allah ya tabbata a gareshi har zuwa karshensu kuma cikamakon su Muhammad s.a.w, Allah madaukaki yace: " hakika kalmarmu ta gabata ga bayin mu manzanni (171) cewa lallai sune masu samun taimako da nasara (172) kuma lallai rundunar mu sune masuyin galaba (173)" suratul saffat.

            Bautan Allah itace shari'ar manzanni baki dayansu ba'a aiko sub a sai domin su tabbatar da ita, Allah madaukaki yace yana mai Magana da manzonsa Muhammad s.a.w: " ya shar'anta maku cikin addini irin abunda yayi wasaici ga Nuhu da abunda mukayi wahayi a gareka da abunda mukayi wasaici ga Ibrahim da Musa da Isa cewa su tsaida addini kada su rarrabu a cikin sa, yayima mushirakai girma wannan abunda kake kiransu zuwa gareshi, Allah shine yake zabin wanda yakeso kuma ya shiryar da wanda ga wanda ya cancanci haka zuwa gareshi (13)" suratu shura.

Daga cikin abunda zai nuna girman matsayin ta shine zaman manzon Allah s.a.w a makka shawon shekaru goma sha uku yana kiran mutane zuwa ga tabbatar da wannan bautar kawai ita kadai ga Allah da kuma gyara masu akidar su wanda aka canza masu ita na bautan gumaka ya kasance yana bi wuraren zaman su da wuraren taruwan su yana ce masu: " yaku mutane kuce la'ilaha illah zaku rabauta" sahihu Ibn Hibban da sihahul siratun nabawiyya na Albany.

Hakan ya kasance ne saboda kasancewar bautan Allah itace tushe da kaida wanda shari'a zata samu da farilloli a cikinta, rashinta kuma dukkanin farilloli da shari'u da ayyukan alherai da dukkanin wani aiki da akayi domin neman kusanci zuwa ga Allah zai kasance bashi da wani kima kamar yayi ne bushashe wanda iska zai watsar da ita kamar yadda Allah madaukaki ya bayyana haka ga manzon sa Muhammad s.a.w: " hakika munyi wahayi gareka ga wanda suka gabace ka da cewa idan kayi shirka ayyukan su zasu lallace kuma zaka kasance cikin masu asara (65) Allah ne kadai zaka bautamawa ka kuma kasance cikin masu godiya (66).

Wannan itace manhajin manzon Allah s.a.w da sahabban sa a lokacin da yake aikan su zuwa wasu wurare domin yin da'awa da yada addinin Allah, ya kasance umurnin da yake masu shine ya kasance farkon abunda zasu fara dashi shine tabbatar da bautan Allah shi kadai, yace ga Mu'azu dan Jabal Allah yakara masa yarda a lokacin da ya aike sa zuwa yeman: " lallai zaka je wurin mutane ma'abota littafi idan ka isa garesu ka kirasu zuwa ga shaidawa babun abun bautawa bisa cancanta sai Allah sannan kuma Muhammad manzon Allah ne, idan sunyi maka biyayya akan haka sai ka fada masu cewa lallai Allah ya wajabta masu salloli biyar a ko wani rana, idan suka maka biyayya akan wannan sai ka fada masu cewa lallai Allah ya wajabta masu zakka za'a rika amsa daga cikin dukiyar su anabawa talakawan su, idan suka maka biyayya akan haka to kashedin ka da dukiyoyin su masu daraja da soyuwa a garesu, kaji tsoron addu'ar wanda aka zalumta domin kuwa bata da wani shamaki tsakanin ta da Allah" sahihul buhari.

Allah madaukaki ya umurce mu da mu bauta masa shi kadai sannan kuma mu nuisance dukkanin bautan wani abunda bashi ba, kuma ya kasance son zuciyar mu yana bin abunda ya umurce mu dashi ya kuma shar'anta mana cikin al'amarin duniya da lahira ba yadace ba da abunda mutane suka shar'anta man aba, da wannan takatsantsan din ne zuciyar mutum zata gyaru, Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani kuji tsoron Allah sannan kuma ku kasance tare da mutane masu gaskiya (119) suratul tauba.

Kuma zai gyara tsakanin mutum da al'ummar sa, manzon Allah s.a.w yace: " shin nabaku labarin su wanene muminai? Duk wanda mutane suka amince masa akan dukiyoyin su da rayukan su, shi kuma musulmi shine wanda mutane suka kubuta daga sharrin harshen sa da hannun sa, shi kuma mujahidi shine wanda ya yaki zuciyar sa wurin yima Allah biyayya, shi kuma muhajir shine wanda ya kauracema zunubai kanana da manya. Ahmad ne ya rawaito hadisin sannan kuma Albany ya ingantashi cikin silsilatul sahiha.

Bautan Allah ta kunshi dukkanin abunda da yayi umurni dashi da abunda ya hana wanda suke dukushe sha'awar mutum wanda yake lallata duniya da abunda cikin sa hakan a tsakin mutane ne, Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani kada sashin ku ya rika yima sashi isgilanci watakila sunfi su alheri, sannan kuma kada mata su rika yima mata yan uwansu isgilanci suma kila sunfi su alheri, kada ku rika jefan kawunan ku da munanan mu'amala da kuma sunayen banza, tur da sunain fasikanci bayan imani, duk wanda be tubaba to wannan sune azzalumai (11) yaku wanda sukayi imani ku nisanci dayawa cikin zato domin lallai wasu daga cikin zato zunubi ne, kada ku rika bin diddigin juna kada kuma ku rikayin giba da gulman junan ku, shin ko dayan ku yana son yaci naman mushin dan uwansa ne saboda haka ku nisanci haka, kuma kuji tsoron allah lallai Allah me yawan amsan tuba ne kuma me rahama (12) suratul hujurat.

Ko kuma a tsakanin zaman takewar al'umma, Allah madaukaki yace: " ku bautawa Allah kuma kada ku hadashi da wani abu cikin bauta sannan kuma iayayen ku ku kyautata masu da yan uwanku makusanta da marayu da miskinai da makwabci dan uwa da makwabci na gefen gida da abokanan zama na gefen mutum da matafiyi da abunda kuka mallaka na bayi, lallai Allah bayason me yawon rowa da alfahari (36) suratun nisa'i.

Ko kuma a tsakanin mahalli, Allah madaukaki yace: " kada kuyi barna a cikin kasa bayan gyaruwanta ku kuma rika kiransa kuna tsakanin kwadayi da tsoro, lallai rahamar Allah tana kusa ga dukkanin masu kyautatawa (56)" suratul a'araf.

Ko kuma a bangaren arzikin kasa, Allah madaukaki yace: " kada ku rika cin dukiyoyin ku a tsakanin ku da barna kuna kaiwa wuraren mahukunta domin su baku dama naci dokiyan mutane da barna alhali kuna sane (188)" suratul bakara.

Ayayin da mukayi dubi da hankulan mu badason zuciyar mu ba zamu samu yakinin cewa lallai bautan Allah a cikinta rayuwan dan adam yake ginuwa, domin bautan Allah tana kira ne zuwa ga kiyaye wannan duniya ta hanyar kiyaye abubuwan da zasu tabbatar da wanzuwar ta, bata tabbatar da lalata mutum kansa ko kuma al'umma ko kasa, tana yada halaye ne na kwarai da mafiya kyawun dabi'u kamar yadda manzon Allah s.a.w ya fadi cewa: " lallai an aiko ni ne domin na cike kyawawan dabi'u" sahihul buhari cikin littafin adabul mufrid da kuma Ahmad da Hakim.

Har wayau tana yada so da kauna da rahama da aminci da adalci da tsarki da biyan amana, da cika alkawari, da bayar da kyauta da nuna kyawawan halaye ga makwabci da marayu da miskinai da matafiyi da mabukaci, da tausayi da jin kai da biyayya ga iyaye da sadar da zumunci da kyautatawa makwabci da saukakewa da son alheri ga wani…. Zuwa karshe ba wannan bane kadai hatta kyakyawan mu'amala ga dabbobi da kyautata masu yana daga cikin sakamakon bautan Allah kamar yadda manzon Allah s.a.w ya fadi cewa: " cikin shayar da ko wani hanta me rai akwai lada" buhari ne ya rawaito shi.

Da nisantar munanan dabi'u da haramta dukkanin abubuwan da ta sanadiyyar su ayyukan barna zai yado a tsakanin al'umma kamar zalumci da sata da karya da algushi da boye kayan masarufi domin suyi tsada da riba, da sabama iyaye da kasha rai wacce Allah ya haramta da cin dukiyar marayu da zina da luwadi da shedar karya da saba alkawari da yanke zuminci da rashawa da almubazaranci da tuye ma'auni da girman kai da gulma da annamimanci da kirkiran karya…. da sauran ayyuka da maganganu da halaye munana wanda yaduwar su ke haifar da fasadi ga tsarin zamanta kewar mutane da kawo masu barazana ga zaman lafiyar su da raba kawunan su. Allah madaukaki yace: " kace masu kuzo zan karanta maku abunda ubangijinku ya haramta maku cewa kada kuyi masa tarayya da wani abu cikin bauta sannan kuma iyay ku kyautata masu kuma kada ku kashe yaranku domin tsoron talauci, mune muke azurta ku dasu yaran, kuma kada ku kusanci alfasha abunda ya bayyana dana boye, kuma kada ku kasha ran da Allah ya haramta kashewa sai da gaskiya, da haka ne ake maku wasaici dashi ko da zaku hankalta (151) kada ku kusanci dukiyar marayu sai da abunda yafi kyau da dacewa har sai sun girma sun mallaki hankulan su, kuma ku cika ma'auni da abun sikeli da gaskiya, bama daurawa wata rai wani face abunda zata iya dauka, idan zakuyi Magana kuyi adalci koda kuwa akan yan uwanku ne, kuma ku cika alkawarin Allah, da haka ne ake maku wasaici koda zakuyi tunani (152)" suratul an'am.

Wannan itace sakon sa s.a.w hatta g mutanen da suka cucar dashi kuma suka fitar dashi daga garin sa suka shirya kashe shi, yafiya da tausasa masu, wannan kuma itace manhajin sa wanda ya bayyana ma sahabbansa lokacin da suka nemi da yayi addu'a akan mushrikai wanda suka cutar dashi kuma suka fitar dashi daga garin sa kuma suka yi hubbasa wurin fitar dasu yace: " lallai ni ba'a aiko niba domin na kasance me tsinuwa an aiko ni ne domin na kasance me tausayi da jin kai" sahihu muslim.

Bauta a musulunci baya takaitu bane kawai akan salla da zakka da azumi da makamantan su bane kadai bauta itace sallamawa Allah da kuma mika wuya gareshi da jayuwa zuwa gareshi da amsa masa kira wurin aikata abunda yayi umurni a aikata da barin abunda yayi hani da yin dukkanin nau'ukan bauta gareshi saboda kasancewar sa ma'abocin kamala kai tsaye wanda bata da wani nakasu ta dukkanin bangarorin nakasa hakan yana sanya ayi masa bauat shi kadai, Allah madaukai yana fadi game dakansa: " bashi da abun kwatanta misali dashi, shi kuma me ji ne kuma me gani" suratu shura ayata 11.

Saboda haka akwia wasu ayyuka wanda basa haduwa da hakikanin bautan Allah sannan kuma suna fitar da bawa daga siffansa na kasancewa me bautan Allah saboda bautan da yakeyima wanin Allah, bazai zama musulmi ba koda kuwa yayi ikirarin musulunci, kamar aiki da bukaye da sihiri da neman tabarruki da kaburburan salihan bayi da bishiya da duwatsu dayin ruku'u da sujjada da dawafi a gefen wannan kaburburan da kuma yin wani aiki domin sun a neman kusanci a garesu kamar yanka da bakance da bayar da sadaka ga masu ziyarar kaburburan su da kuma girmamasu saboda yin imanin cewa mutanen cikin ta bayin Allah ne na kwarai kuma zasu iya amfanar da mutum wani abu ko kuma su cutar dashi da wani abu ko kuma suna iko da shugabantar duniya, abunda basu sani ba cewa da ace zusu iya amfanar da wani da kawunan su suka amfanar, daga cikin wannan ayyukan da imani akwai abubuwan da sukelalata wannan bauta suke kuma gurbata siffanta yake kuma sanya musulmi cikin hadari a addinin sa, kamar rataya laya da kambu da makamantan su da niyyar cewa suna kawar ma mutum da wani bala'i, da rataya layun domin maganin bakan baki, saboda haka ne manzon Allah s.a.w ya tsawatar akan wannan abu tsawatarwa me tsanani yace: " ku saurara kuji lallai mutanen da suka gabace ku sun kasance sune rikan kaburburan annabawan su da salihan bayi a matsayin masallatai, ku saurara kuji kada ku riki kabarina ya koma masallaci lallai ni na hanaku haka" sahihu muslim.

Manzon Allah s.a.w ya kasance yana umurtan sahabban sa da su ajiyesa a matsayin da Allah ya ajiyesa kada su rika girmamashi wanda ya wuce gona da iri saboda tsoron kada al'ummar sa su fada cikin irin abunda sauran al'ummar da suka gabace su suka fada ciki: " kada ku rika kuranta ni kamar yadda nasara suke kuranta isa dan Maryam, ni bawan Allah ne, ku rika cemun bawan Allah da manzon sa" buhari ne ya rawaito hadisin.

Sheikh Abdullahi Ababil Allah yayi masa rahama yana cewa: addini gabaki dayansa yana cikin ibada ne, idan mutum yasan haka ya kuma yasan hakikanin ma'anar Allah cewa shine abun bauta ya kuma san hakikanin bauta zai bayyanar masa cewa lallai duk wanda ya sanya wani abu na ibada ga wanin Allah, to hakika yafa bauta wannan abu kuma ya mayar dashi Allah koda kuwa sunan ba'a kiransa da sunan allah hakan bazai canza hakikanin ma'anar allah ba sannan hukunsa bazai gushe ba, a lokacin da Adiyyi dan Hatim yazo wurin manzon Allah s.a.w yana kirista sai yaji manzon Allah s.a.w yana karanta wannan aya: sun rike malaman su da fastocinsu sun koma masu ubangiyansu koma bayan Allah da masihi dan Maryam, kuma ba'a umurce sub a sai su bautama Allah daya babu abun bautawa da gaskiya bisa cancanta sais hi, tsarki ya tabbatar masa daga abunda suke masa shirka dashi, sai Adiyyi yace: sai yace masa: mufa ba bauta masu mukeyi ba, sai manzon Allah yace masa: shin basa haramta maku abunda Allah ya halatta maku sai ku halatta hakan?, su kuma haramta maku abunda Allah ya halatta sai ku haramta hakan?, sai Adiyyi yace masa haka ne, sai manzon Allah s.a.w yace: " wannan itace bautar tasu". Buhari ne ya rawaito hadisin cikin littafin tarikh da tirmizi cikin sunan da dabari cikin mu'ujamul kabir kuma albani ya inganta shi.

Da ace akwai wani wanda yake da ikon yanyo alheri ko kuma kawar da sharri a cikin mutane da manzannin Allah da annabawan sa su sukafi cancanta da hakan sai dai wannan abun a wurin Allah kadai yake, hakika manzon Allah s.a.w ya barrantar da kansa da cewa bashi da wani tsimi ko dabara wurin samarma kansa da wani alheri ko kuma kawar ma da kansa wani cucarwa, Allah madaukaki yace: " kace masu bani da ikon mallakama kaina wani alheri ko kuma kawar mata da wani sharri sai abunda Allah cikin haka, da ace nasan gaibu kuwa dana yawaita aikin alheri kuma da wani cucarwa be same ni ba, ni bakomai bane face me gargadi da bishara ga mutane masu imani (188)" suratul a'araf.

Haka kuma ya tarranta kansa da mallakar wani iko ko dabara na jawoma wani alheri ko kuma kawar masa da wani sharri, Allah madaukaki yace: " kace masu lallai ni ubangijina kadai nake kira kuma bana masa shirka da kowa (20) kace masu lallai ni ban mallaki cucarwa ba a gareku ko kuma shiriya (21) kace masu ni babu wanda ya isa ya tsiratar dani a wurin Allah kuma bani da wani mataimaki ko majinbincin al'amura a gabansa (22)" suratul jin.

Saurara kaji maganar sayyid Khudub dayayi me matukar kayu lokacin da yace: lallai addini ga wanin Allah cikin imanin ta da sawwa ma'anarta cikin kogin wahami da tatsuniyoyi da labaran kanzon kure gewacce bata karewa, irin wacce zaman jahiliyya suka rikayi na bautan gumaka mabanbanta yanayi, da kuma gabatar da bakance da yanka na dukiyoyi wani lokaci ma na raya karkashin wannan kullin na kida gurbatacciya da ikida karkatacce, kuma mutane suna rayuwa da ita cikin tsoron allolin wahami mabanbanta, da masu gadin su da bokaye wanda suke alaka da wannan allolin! Da kuma masu sihiri wanda suke da alaka da aljanu! Da malamai da manyan mutane wanda sune masu sirruka! da… da…. da… daga cikin wahami wanda mutane basa gushewa acikin sa cikin tsoro da kusanta da kwadayi, har sai an sare kawunan su sannan kuma kkarin su ya rarrabu, kuma dukkanin damar su ya tafi ga wannan fage!

Lallai bautan Allah tana tankade dattin sha'awa ta dabbobi ta mayar dashi zuwa ga hanyar sa ta dabi'a wanda Allah yakeson ta akai, sai kasa ta rayu da kuma kiyaye wannan duniya daga abunda ke cikin san a wasanni, da kuma yin nisa ga bautan Allah ne alfasha yake ruruwa da sunan yanci, sannan kuma hakkoki suke wulakanta da sunan wayewa, da cin dukiyoyin mutane da barna da sunan kasuwanci me yanci, da bautar da mutane da sunan tsarin mutum, sannan kuma kabilanci da bangarenci ke yaduwa a tsakanin al'umma da yaduwar shirka da bautan gumaka, Allah yayi gaskiya cikin fadin cewa: " fasadi ya bayyana a doron kasa da cikin ruwa da abunda mutane suka kasance suna aikatawa da hannuwan su domin a dandana masu wasu daga cikin abunda suka aikata koda zasu dawo kan hanya (41)" suratul rum.

Sayyid Kudub yana cewa: " lallai bauta ga Allah tana yantar da mutum daga bautan wanin sa, sannan kuma tana fitar da mutane daga bautar bayin Allah zuwa ga bautan Allah shi kadai. Ka hada ne darajar mutum ke tabbata da yancin san a hakika, wannan yancin da wancan yancin wanda bazai taba yuwuwa bas u hadu ba a karkashin wata doka ta daban wacce ba dokatr musulunci ba wanda mutane zasu rika addinin dashi sashin su da sashin su da bauta, misali cikin masalanta sunada yawa…. Wannan bauta na kudurcewa ne, ko kuma na wasu alamomi ne, ko kuma na shari'o'i ne.. dukkanin su bauta ne, kuma wasunsu sunyi kama da wasunsu, tana mika wuya zuwa ga wanin Allah, ta hanyar mika mata wuya domin samun wani abu cikin al'amarin rayuwa ga wanin Allah.

A lokacin da bauta take kasancewa ga wanin Allah cikin wannan duniya tamu kamar yadda ake cewa (kundun tsarin mulki ko kuma dokokin mutane wacce bata kiyaye rafkanannu) rayuwa ce irin ta namomin daji me karfi yacinye mara karfi sannan kuma me kudi ya cinye duniyar talaka da yaduwar kurakurai domin samun wani abun duniya koda kuwa ta fuskar tsira ne ko kuma ta fuskar wani mutum na daban, ita bauta ga Allah bata tafiyar ga hakkoki kuma tana kiyaye hakkin rafkanannu da marasa galihu da tsofaffi kowa tana kiyaye masa hakkin sa da kuma kiyaye masu mutuncin su da kare masu dukiyoyin su da basu hakkokin su, masu rahama Allah yana masu rahama, kuji tausayin mutanen duniya sai wanda yake sama yaji tausayin ku, haka bautar Allah ya kewaye musulmi.

Musulunci yazo domin yantar da bautar da mutane da akeyi na aikin karfi ya kasance farkon abunda ya kwadaitar dashi akai yasanya shi ya zama kaffara na zunubai masu masu wanda mutum ke aikawata sanan kuma ya nemi a taimakama wanda yakeson ya siya kansa ya yantar da ita daga kangin bauta,Allah madaukaki yace: " wanda sukeson a rubuta yarjejeniya ta yantar dasu cikin abunda kuka mallaka na bayin ku to ku rubuta masu wannan yarjejeniyar ta yantar dasu idan kunsan alheri a tattare dasu, kuma ku basu daga cikin dukiyar Allah wanda ya baku" suratun nur ayata 33.

Haka musulunci tazo ne domin yantar da zuciyan mutane daga bautan wanin Allah da alakantuwa da wanin sa sai yakiyayeta daga kanzon kurege ya kuma kare su daga macuta da bokaye da dulal, hakan ya faru ne sabada abunda ya gina cikin zukatan su na sammawa da cewa lallai amfanar wa da cutatrwa fa a hannun Allah suke duk abunda yaso shike faruwa wanda kuma be so ba baya faruwa kuma lallai mutane dukkanun su suna karkashin ikonsa ne da ganin damar sa, Allah madaukaki yace: " babu wata musiba da zata samu mutum face da izinin Allah, duk wanda yayi imani da Allah zaai shiryar da zuciyar sa, Allah masani ne akan komai.

Musulmai sun banbanta cikin tabbatar da wannan bauta ga Allah kasancewar su mutane suma wasu abuwan da yake faruwa da dauran mutane yana faruwa dasu na galabar wasu daga cikin sha'awar su da makircin zuciya, sub a mala'iku bane sannan kuma ba ma'asumai bane wanda aka kiyaye su daga aikata laifi, Ibn Kayyim Allah ya masa rahama yana cewa: (daga cikin siffofin da bautan Allah ya banbanta dasu wacce duga dugai basa tabbata akansa dai dasu shine: kololuwan soyayya dare da kololuwan kaskantar dakai, wannan shine cikan bauta, sannan matsayin mutane na banbanta gwargwadon banbantansu ga wannan asalin guda biyu, duk wanda ya bayar da son sa da kankantar da kansa da jayuwar sag a wanin Allah, to hakika ya kwatantashi cikin tsarka kekken hakkin sa, wannan abu kuwa bazai taba yiwuwa ba wata addini tazo dashi cikin addinai… kuma daga cikin siffofin Allah wanda ya kebanta dashi shine sujjada, duk wanda yayi sujjjada ga wanin sa ko hakika ya kwatantashi da Allah mahalicci, daga cikin su kuma akwai tawakkali, duk wanda ya dogara ga wanin allah to hakika ya kwatantashi dashi, daga cikin su kuma akwai tuba, duk wanda ya tuba zuwa ga wanin Allah to hakika ya kwatantashi da Allah)[4].

 

 

ALAKA TAKAI TSAYE TSAKANIN BAWA DA UBANGIJIN SA:

Bauta ga Allah matsayi ce ga rai wacce ta take yantata daga bautan wanin Allah, da it ace aka samun ganawa kai tsaye tsakanin bawa da mahaliccinsa madaukaki, babu wani shamakiko kuma dan tsakiya tsakanin su, kofa tana bude a ko wani lokaci a ko wani wuri kuma cikin kowani yanayi, babu wani me tsaron kufar wanda zai bar wanda yakeso ya shiga ya kuma hana wanda yake so shiga, ka shigar d akanka cikin wannan kofa tunda haka ne ka kuma roki bukatunka da kuma shinfida kukenka da kuma neman taimakon sa akan biya maka su, ka tambaye sa duk abunda kake so ya kuma kwanta maka a rai, saboda kyautar sa bata da iyaka kamar yadda Allah madaukaki ya fada: " idan bayin na suna tambayanka game dani kace masu ina kusa dasu, ina amsa rokon duk wanda ya tambaye ni idan ya tabbaya, to su rokeni kuma suyi imani dani koda zasu shiryu (186)" suratul bakara.

Duk yadda zunubanka sukayi yawa, duk yadda kakai da aikata barna baka da bukatar wani ya zaman maka shamako dan tsakiya tsakanin ka da Allah domin neman gafaran sa, hanyar tsadarwa tsakanin ka da sama abude yake abunda akeso a gareka kawai shine gaskiya da ikhlasi game da hakan, Allah madaukaki yace: " duk wanda yake aikata sabo ko kuma yake zalumtar kansa sa'annan ya nemi gafarar Allah, to hakika zai samu Allah me yawan gafara ne da rahama (110)" suratun nisa'i.

Kuma duk yadda bukatunka suka yawaita da burukanka lallai shine wanda zai yaye maka su da addu'o'inka gareshi da neman bukatuwar ka da kaskantar da kanka a gabansa, Allah madaukaki yace: " ku kira ubangijin ku da rokonsa kuna masu Kankan dakai kuma a boye, lallai bayason masu wuce iyaka (55)" suratul a'araf.

Arzikinsa da yalwar sa basa karewa, sannan kuma kyautun sa basa yankewa, baya hana kowa hanawa daga falalar sa, sannan kuma baya hana kowa kyautar sa, Allah madaukaki yana cewa cikin hadisin kudusi: " yaku bayina! Hakika na haramta zalumci a gareni na kuma sanya shi haramun a tsakanin ku kada kuyi zalumci, yaku bayina! Lallai kuna sabo dare da rana kuma ina gafarta zunubbai baki dayan sa bana damuwa saboda haka ku roki gafarata zan gafarta maku, yaku bayina! Dukkanku masu yunwa ne sai wanda ya ciyar dashi, saboda haka ku nemi ciyarwa ta zan ciyar daku, yaku bayina! Cucarwan ku bazai isa gareni ba bare ku cucar dani haka kuma amfanarwan ku bazai isa gareni ba bare ku amfanar dani da wani abu, yaku bayina! Da ace farkon ku da karshen ku aljanunku da mutanen ku zasu hadu a zuciyar mutum mafi sabo da barna a cikin ku hakan bazai ragemun komai ba cikin mulki na kwatankwacin kwayar zarra, yaku bayina! Da ace farkon ku da karshen ku aljanunku da mutanen ku zasu hadu a wuri daya sais u rokeni dukkanin sun aba kowa abunda ya rokeni a cikin su hakan bazai ragemun komai ba cikin abunda yake wurina sai kamar yadda idan an tsoma allura cikin ruwan kogi aka cirota irin abunda zata rage cikin wannan ruwan kogi, yaku bayina! Lallai ayyukan ku ne yake dawo maku dasu, duk wanda ya samu alheri to ya gode mani wanda kuma ya samu wanin haka to kada ya zargi kowa sai kansa. Hadisi ne ingantacce, muslim ne ya rawaito shi.

Abun bauta na gaskiya bashi da bukatar a samu wani shamako dan tsakiya tsakanin sa da masu bauta masa, lallai yafi kowa sanin su da halin su yana jin maganganun su sannan kuma yasan sirrin su da abunda suka tattauna a tsakanin su cikin a kebance, kuma yawan bukatuwar su bazai hade masa ba tare da banbancin yarukan su da banbantan bukatuwar su, bashi da wata bukata na cewa sai wani ya mika masu bukatuwar su zuwa gareshi, Allah madaukaki yace: " ubangijin ku yace ku kirani zan amsa maku, lallai wanda suke girman kai game da kirana da rook n azan shigar dasu wutan jahannama suna kaskantattu (60)" suratu gafir.

Wannan shine abunda Allah ya bayyanawa bayin sa domin su guje yan fashi madamfara wanda suke son su shiga tsakanin Allah da bayin sa, Allah madaukaki yace: " ku saurara kuji ga Allah ne addini yake tsarkakakke wanda suka riki wanin sa waliyyai suna cewa bama bauta masu si dan su kusantar damu ga Allah kusa, lallai Allah zai masu hukunci a tsakanin su cikin abunda suka kasance na sabani a tsakanin su, lalli Allah baya shiryar da duk wanda ya kasance me yawan karya da kafirci (3)" suratul zumar.

 

 

SAKAMAKON BAUTAMA WANIN ALLAH:

Lallai dukkanin abunda al'ummonin duniya suke gani na rayuwa na birnin su dana kauyen su na abubuwan zalumci tsakanin su da kuma tarwatsewan iyalai da yaduwar munanan dabi'u da ywaitan shaye-shaye da kuma lalacewar shugabanci da tattalin arziki da siyasa, da kuma abunda duniya take cikin sa ayau na yake-yake da rurrusa garuruwa irin wanda muke ganin shi a duniyar mu ta yau lallai babban sababin sa shine nisantar bautan Allah na gaskiya wacce take umurni da dukkanin alheri take kuma yin hani daga dukkanin mummunan aiki da sharri, Allah yayi gaskiya cikin fadin sa cewa: " da ace gaskiya zatabi son zuciyar su to da sama da kasa sun lalace da abunda ke tsakanin su, hakika yazo masu ne da ambatonsu su kuma sun kasance masu kawar dakai game da ambaton nasu (71)" suratul muminun.

Musani cewa lallai tabbatar da bauta ga Allah kariya ne, duk yadda al'umma suka nesanci bautar Allah to zasu fada cikin munanan dabi'u da bata, sannan kuma duk yadda suka tabbatar da bauta ga Allah gwargwadon yadda za'a kiyaye su daga hakan kuma halinsu ya gyaru dana al'ummar su, Allah hyayi gaskiya cikin fadin sa cewa: " duk wanda yabi shiriyata to bazi taba bacewa ba kuma bazai ci wahala ba (123) wanda kuma ya bijirewa ambatona lallai zai rayu rayuwa na kunci sannan kuma zamu tashe shi ranan alkiyama makaho (124) sai yace ya ubangijina me yasa ka tasheni makaho alhali na ksance me gani a duniya (125)" suratu daha.

Sayyid khudub Allah ya masa rahama yana cewa: hakika anbada labarin cewa duk wanda suka kafircema daga bautan Allah shi kadai, suka bayar da dama da ayi masu shugabanci da hukunci bada shari'ar Allah ba, hakika a karshe sun fada cikin azabar bautan wanin Allah. Bauta wacce take cinye darajar mutum da karamar sa da yancin sa, duk yadda yanayin tsarin mulkin nasu kuwa ya banbanta, wacce wasunsu suke tunanin cewa zata lamince masu darajar sun a yan adam da yanci da kuma karamar su, hakika turawa sun kauracewa Allah cikin kauracewa cocinsu na mabarnata dagutai da sunan addini na wanda aka canza shi, sun kuma yima Allah madaukaki zanga zanga cikin zanga zangar su akan wannan cocuka wacce tayi kaca-kaca da martaban dan adam cikin karfin mallake shi da sukayi na zalumci! Sannan mutane suke tunanin cewa zasu samu yanci da daraja da karama da maslahar karkashin wannan dokoki na dimukradiyya, suka kuma rataye dukkanin burin sun a ladan lahira akan yanci da lamuni wanda kundin tsarin mulkin su ya shirya masu, da samar da yan majlisu, da yancin jaridu da fadin albarkacin baki, da lamuni na hukunce hukuncen ramuwa na shari'a, da yin shugabanci da ra'ayin wanda sukafi yawa… zuwa sauran bangarorin da wannan dokoki nasu ta shafa, ya karshen haka ta kasance? Karshenta ta kasance zalunci ne da dagawa wacce ake kira da suna << jari hujja>> zalumci wacce ta shafi dukkanin wannan lamuni, da abubuwan da aka tsara zuwa ga tsabar tsammani kawai! Dayawa sun fada cikin tarkon bautan kasakanci ga wasu dagutai marasa yawa wanda suka mallaki wannan jari hujja, sai ya mallaki mafiya yawan yan majalisu da wannan jari nashi! Da kundun tsarin mulkin wadda suka kirkiro! Da wannan yanci na fadin albarkacin baki! Da sauran lamunin da mutane sukayi zaton acan baya cewa zai lamunce masu daraja na dan adam da karama da yanci, wanda cikin nisantar Allah madaukaki!!!

Daga nan kuma sai wasu cikin mutane suka guduma wancan dokoki da tsarin mulki na mutane wanda ake zalumci a ciki << jari hujja>> da kuma << fifita wasu akan wasu>> zuwa ga dokoki na hadin gwewa tsakanin mutane! To mesuka aikata? Hakika sun canza addinin jari hujja zuwa ga addinin bautan kasa! Wacce take mallakan dukiya a hannun shugaba! Sa hakan ya zama yafi hatsari akan tsarin jari hujja! A cikin dukkanin halayen da yanayi da tsarin mutum dai ya bautawa mutum, sun biya dukiyoyin su da rayukan ga alloli mabanbanta cikin ko wani hali.

 

 

HANYA ZUWA GA BAUTAN ALLAH NA HAKIKA:

Lallai hanya na dabi'azuwa ga bautan Allah na hakika shine rashin hadashi da wani cikin zatin sa da sunayen sa da siffofin sa ko kuma cikin umurnin sa da hanin sa domin rayuwan ka ta kasance gabaki dayanta karkashin abubuwan da Allah yake so, saboda bauta ta ginu ne akan so da jayuwa da kuma biyayya, Allah madaukaki yace: " kace lallai sallata za yanka ta da rayuwa ta da mutuwa ta ga Allah ne ubangijin talikai (162)" suratul an'am.

Idan aka rasa daya daga cikin hakabauta bata zama hakikani bag a Allah, Allah madaukaki yace: " daga cikin mutane akwai wanda suke rike koma bayan Allah alloli kishiyoyi suna sonsu kamar son da sukema Allah, wanda sukayi imani suna tsananin so ga Allah, da za'aga wanda sukayi zalumci a lokacin da zasuga azaba lallai karfi ga Allah yake baki dayanshi kuma lallai Allah me tsananin azaba ne" suratul bakara ayata 165.

Wannan shine abunda Allah ya halicci halittun sa akai baki dayan su, suna masa tasbihi da gode masa zuma jayuwa da dabi'ar su zuwa gare shi kamar yadda ya bada labarin haka madaukakin sarki cikin fadin sa cewa: " sammai guda bakwai da kasa da abunda ke tsakaninsu suna masu tasbihi ga Allah, babu wani halitta face yana yima Allah tasbihi sai dai bakwa fahimtar tasbihin su, lallai ya kasance me yawan hakuri me gafara (44)" suratul isra'i.

Tana masa bauta da kankai dakai a gareshi cikin son zuciyar ta ko kuma ta dole, Allah madaukaki yace: " ga Allah ne dukkanin abunda suke cikin sammai da kasa suke sujjada a cikin son ransu ko kuma ta dole da kuma inuwar su safe da maraice ( 15)" suratul ra'ad.

Abun takaicin shine sauran halittu na dabbobi da tsuntsaye suna jayuwa zuwa ga fidirar su ta halitta suna kin yin shirka da bautawa wanin Allah, Sulaiman dan Dawud Allah ya bashi mulki irin wanda ba'a taba bama wani taliki ba irinsa, Allah ya mallaka masa iska da aljanu, Allah madaukaki yace: " mun mallakawa sulaiman iska me saurin tafiyan wata daya safe da maraice, muka kuma narkar masa da dalma, daga cikin aljanu akwai masu aiki a karkashin sa da izinin ubangijin sa, duk wanda ya kangare cikinsu daga umurnin mu zamu dandana masa azaba da wutan sa'ir (12) suna masa aikin da yake so na gina masallaci da mutum butumi na dabbobi da mutane da gilasai da tukwane manya, kuyi aiki yaku iyalan gidan dawud domin godiya, kadan ne cikin bayina suke da godiya (13)" suratu saba'i.

Kuma Allah ya bashi har wayau fahimtar yarukan kwari da maganar tsuntsaye, Allah madaukaki yace: " sai sulaima ya gaji dawud, sai yace yaku mutane lallai an sanar damu maganar tsuntsaye kuma anbamu komai, lallai wannan falalce bayyananne (16)" suratun namli.

Annabi sulaiman ya kasance me matukar kwadayi na ganin be rasa daya daga cikin rundunan sa da abubuwan da suke karkashin kulawarsa wanda suke yawo a doron kasa gabas da yamma suna zuwa masa da labarinta, Allah madaukaki yace: " mun hadama sulaiman rundununsa daga mutane da aljanu da tsuntsaye daki bayan daki (17)" suratun namli.

Wata rana ya rasasu bega wani tsuntsu ba alhuda-huda a majalisar sa sai yayi inkarin fashin san a rashin zuwan sa yayi alkawarin zai azabtar dashi akan fashinsa indai babu wani uzirin daya jawo hakan, ana nan sai sagshinan yazo masa da labara me girma, sai yayi inkarin labarin be yarda dashi ba inda yake ce masa yaga wata sarauniya ta kasar saba'a da mutanenta suna yima Allah shirka, wannan shine abunda da sulaiman be yarda dashi ba kuma baya tabbatar dashi, Allah madaukaki yace: " sai ya rasa wani tsuntsu a cikin majalisan sa sai yace me yasa banga alhuda-huda bane ko dai ya kasance cikin masu fashi ne (20) sai na azabtar dashi azaba me tsanani ko kuma na yanka shi ko kuma yazomun da dalili bayyananne (21) bayan lokaci kadai sai gashinan yace masa naje wani wurin da baka taba zuwa ba sannan nazo maka da wani labara na gaskiya daga garin saba'a (22) lallai na samu wata mata wacce take mulkan su kuma anbata komai kuma tanada kujera me girma (23) na same ta da mutanen ta suna yima rama sujjada koma bayan Allah kuma shedan ya kawata masu ayyukansu sai ya kange su daga hanya kuma su ba shiryayyu bane (24) bazasuyi ma Allah sujjada ba wanda yake samar da ruwa daga sama ya fitar da tsirrai daga cikin kasa ya kuma san abunda suke boyewa da abunda suke bayyanawa (25) Allah shi kadai yake babu abun bauta da gaskiya bisa cancanta sais hi, ubangijin al'arshi me girma (26)" suratun namli.

 

 

KARADEWAN TAUHIDI GA DUNIYA BAKI DAYANTA:

Bautan Allah da kadaitashi shine kiran annabawa da manzanni baki dayan su wanda Allah madaukaki ya aiko su tun daga kan Adam amincin Allah ya tabbata a gareshi har zuwa kan cikamakon su karshen annabawa da manzanni Muhammad s.a.w, Allah madaukaki yace: " bamu aiki wani manzo ba gabanin ka face mun mashi wahayi cewa babu abun bauta dagaskiya bisa cancanta sai ni saboda haka ku bauta mun (25)" suratul anbiya'i.

Sayyid kudub Allah yayi masa rahama yana cewa: lallai tauhidin uhuhiyya da tauhidin rububiyya shine tauhidin da ya cancanci a aiko da dukkanin wannan manzanni domin sa, kuma ya cancanci yin dukkani kokari domin sa, sannan kuma wurin tabbatar dashi za'a dauki dukkanin wahalhalu da azaba a wannan duniya... badan Allah madaukaki yana da bukatar hakan ba, saboda shi madaukaki ya wadatu daga talikai. Sai dai rayuwan mutum baya gyaruwa tayi daidai da dan adam sai da wannan tauhidi wanda bashi da iyaka na tasiri cikin rayuwan mutum cikin dukkanin bangarorin rayuwa bai daya>>..

Bari mu duba mu gani farko zuwa ga tasirin tabbatar da wannan tauhidin akan wannan misali gamamme cikin kasancewar dan adam ta bangaren samuwar sa, da bukatuwar san a fidira, da kuma gina kansa a matsayin mutum.. tasirin tauhidi cikin sawwarawan sa … da kuma tasirin wannan sawwarawan cikin kasancewar sa dan adam, wannan sawwarawan yana kunsan abubuwa da dama akan gamammen wannan misali ta dukkanin ma'anar dake daukan gamewa, yana Magana da asalin san a kasancewa dan adam ta dukkanin bangarorin sa da gabbansa, sannan ya koma zuwa ga bangare daya wanda zayyi aii da ita, bangare da take neman komai, da kuma fuskantar ta da komai, bangare guda daya wanda kake fatar sa da kuma tsoron sa, kake kuma tsoron fushin ta, kake kuma neman yardan ta, bangare daya wacce ta mallaki komai, saboda itace ta halicci komai, ta kuma mallaki komai, take kuma jujjuya komai.

Haka kuma asalin mutum yana komawa ne zuwa ga asali daya, wacce take samun dukkanin surantawan ta da fahimtarta da darajarta da ma'auninta, take kuma samun amsa dukkanin addu'ar ta akan abunda yafi karfin ta na fuskantar duniya da rayuwa da mutum.

A lokacin da wannan asali suke haduwa, sannan kuma tunani da dabi'a suke haduwa, da sawwarawa da kuma amsa cikin sha'anin akida da tafarki. Da sha'anin mafara da koya. Da sha'anin rayuwa da mutuwa. Da sha'anin ayyuka da kai komo. Da sha'anin lafiya da arziki. Da sha'anin duniya da lahira. Kada ka rarrabu haka kuma kada ka fiskanci hanyoyi mabanbanta, kada kuma kabi hanyoyi mabanbanta ba tare da ittifaki ba!

Tare da abunda Allah ya banbanta su dashi na zabin da yayi masu da sako da kuma matsayin su a wurin Allah da son da yake masu sai dais u mutane ne ba'a bauta masu sannan kuma ba'a masu wani abu cikin bauta, Allah madaukaki yace: " be dace ba wani mutum Allah ya bashi littafi da hikima da annabta sai kuma yace ma mutane ku bautamun koma bayan Allah abunda ya dace yace masu shine ku zama malamai bayin Allah masu hakuri da abunda kuka kasance kuna koya na littafi da kuma haddacewa (79) baya umurtan ku da ku riki mala'iku da annabawa su zaman maku abun bauta, shin zai umurce ku ne da yin kafurci bayan kun kasance musulmai (80)" suratu al'imran.

Nuhu shine farkon manzon bayan Adam amincin Allah ya tabbata agaresu, ya zauna cikin mutanen sa shekaru dari tara da hasin yana da'awa wanda yayi amfani da dukkanin hanyoyin isar da sako na kwataitarwa da tsoratarwa, a tsirrance da kuma bayyane domin ya dawo da mutanen sa zuwa ga tauhida da bautan Allah shi kadai bayan shirka ta yadu a cikin su, Allah madaukaki yace: " hakika mun aiki Nuhu zuwa ga mutanen sa sai yace masu yaku mutane na ku bautawa Allah baku da wani abun bauta bayansa, lallai ni inaji maku tsoron azabar wata rana me girma (59)" suratul a'araf.

Daga nan kuma duk lokacin da mutum ya canza daga bautan Allah sai a aiko masu da manzanni da annabawa wanda zasu jaddada masu addininsu su mayar dasu kan tafarkin tauhidi da kuma tsira daga wuta, Allah madaukaki yace: " hakika mun aika da manzanni zuwa ga ko wace al'umma cewa su bautawa Allah sannan kuma su nisanci dagutai, daga cikin su akwai wanda Allah ya shiryar dashi kuma daga cikin su akwai wanda bata ta tabbata akansa, kuyi tafiya cikin kasa kuyi kallo yadda karshen masu karyata annabawa da manzanni ta kaya (36)" suratun nahli.

Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gareshi baban annabawa lokacin da ya same mutanen sa akan aikin shirka sai yayi mujadala dasu akan abunda suke bautamawa koma bayan Allah ya kuma buga masu misali na hankali wanda zai gamsar dasu akan batar da suke cikinta, Allah madaukaki yace: " a lokacin da Ibrahim yacema mahaifin sa azara yanzu zaka riki gumaka su a matsayin alla abun bauta, lallai ni inaganin ka da mutanen ka a cikin wata irin bata bayyananne (74) kuma haka ne muka nunama Ibrahim sirrukan cikin sammai da kasssai na halittu da hujjoji domin ya zama cikin masu yakini (75) a lokacin da dare ya lullube shi sai yaga tauraro sai yace wannan shine ubangiji na, alokacin daya bace kuma sai yace ni banason ubangiji me bacewa (76) a lokacin da kuma yaga wata ya fito sai yace wannan shine ubangijina, amma lokacin da yaga ya bace sai yace idan dai ubangijina be shiryar dani ba tabbas zan kasance cikin mutane batattu (77) a lokacin da yaga rana ta fito sai yace wannan itace ubangijina tama wannan tafi girma, a lokacin data bace sai yace yaku mjutane na lallai ni na barranta daga cikin shirkanku (78) lallai na mika fuska ta ga Allah wanda ya kirkiri sammai da kasa ine me barin shirka zuwa ga tauhidi kuma ban kasance cikin masu shirk aba (79)" suratul an'am.

Yakubu Allah ya kara masa yarda mahaifin bani isra'il baki dayan su ya kasance me kwadayin ganin akidar tauhidi ta daure da lamunin ganin ci gabanta bayan sa, ya kasance cikin wasiyyan da yayima yaransa a lokacin mutuwar lokacin me kunci da wahala wanda tunani ke da wahala inba abunda ya shafi rai ba kawai, ya kasance abunda yaba muhimmanci da burinsa shine daurewar tauhidi da ci gaban bautan Allah shi kadai, Allah madaukaki yace yana me bada labara game dashi cewa: " ko kun kasance masu shaida a lokacin da mutuwa ta zoma Yakubu lokacin daya cema yaransa me zaku bautamawa baya na, sai sukace zamu bautawa Allanka kuma Allan iyayenka Ibrahim da Isma'il da Ishak Allah daya kuma muma gareshi muke mike wuya (133)" suratyl bakara.

Annabin Allah Yusuf Amincin Allah ya tabbata agareshi bayan an kulleshi a kurkuku wahalar zaman gidan kurkuku da tsananin da rabuwa da mutane da kuma zafin zalumcin da akayi masa baisa ya manta da al'amarin da'awa ba zuga kadaita Allah da bauta masa a tsakanin mutanen da suke zama tare a kurkuku, Allah madaukaki yace: " yaku abokaina na zaman kurkuku shin alloli mabanbanta su sukafi alheri ko kuma Allah wanda yake shi kadai me iko akan komai (39) abunda kuke bautamawa koma bayan sa ba komai bane face sunaye wanda kuka radama suna ku da iyayenku wanda Allah be saukar da wani dalili ba akan haka, babu hukunci sai ga Allah, yayi umurni da kada abautawa kowa sais hi kadai wannan shine addini mikakke amma dayawa daga cikin mutane basu sani ba (40)" suratu yusuf.

Da kuma Annabin Allah musa amincin Allah ya tabbata a gareshi a lokacin da mutanen sa suka nema daga wurin sa bayan sun wuce wasu mutane wanda suke bauta gumaka da yasanya masu suma wani alla na gunki wanda zasu rika bautamawa suma Kaman wannan mutane, sai ya bayyana masu hakikanin wannan allolin da suke bautamawa koma bayan Allah, Allah madaukaki yace: " sai muka ketarar da bani isra'ila kogi sai suka riske wasu mutane suna bautan gumaka nasu, sai suka ce ya musa kasanya mana alla muma kamar yadda suke da alla, sai yace masu lallai ku mutane masu jahiltan al'amura (138) lallai wannan mutane halakakku ne akan abunda suke kuma batattune akan abuda suke aikatawa (139) sai yace yanzu wanin Allah ne zan sanya maku ya zama abun bauta agareku bayan ya daukaka ku akan talikai baki daya (140)" suratul a'araf.

A bayan sa kuma annabi Isa dan Maryam amincin Allah ya tabbata agareshi an aikeshi zuwa ga bani isra'il a lokacin da suka bace suka bar shari'ar musa amincin Allah ya tabbata agareshi suka koma yima Allah shirka da annabin Allah Uzairu, domin ya mayar dasu zuwa ga hanya mikakkiya, Allah madaukaki yace: " hakika wanda sukace lallai masihu dan Maryam Allah ne sun kafirta, sai masihu dan Maryam yace yaku bani isra'il ku bautawa Allah ubangijina daku hakika duk wanda yayi shirka da Allah to Allah ya haramta mashin aljanna sannan makuomar sa itace wuta, azzalumai basu da me taimako (72)" suratul ma'ida.

Cikamakon annabawa da manzanni Muhammad s.a.w an aikoshi ga mutanen da suka karkace daga addinin su mikakke suka bautawa bishiya da duwatsu, ya zauna a cikin su shekara goma sha daya yana bin wuraren tarukan su da wurin bukukuwar su yana kiran su yana cewa " kuce la'ilaha illah zaku rabauta ku tsira" Ibn hibban ne ya rawaito shi.

Wannan itace sakon da aka aiko da manzanni da ita domin tabbatar da bautan Allah, kuma wannan itace klamar da suke kiran mutanen su dace da ita cewa " yaku mutane na ku bautawa Allah baku da wani abun bauta bayan shi" suratu Hudu.

Sayyid kudub Allah ya masa rahama yana cewa: maganar gaskiya itace da ace hakikanin bauta itace kawai jin son bauta ba tare da aiki ba da hakan kawai be cancanci wannan manzanni da aka turo ba dayawa masu daraja da sakwanni, kuma da be cancanci dukkanin irin wannan wahalhalu ba wanda manzannin Allah sukayi akai ba kuma da bata cancanci dukkanin wannan azabar ba da tsanani wnada masu da'awa da muminai suka fuskanta a duniya! Lallai abunda ya cancanci wannan namjin kokari shine fitar da mutum daga rayuwa ta bautan mutane, da mayar dasu zuwa ga addinin bautan Allah shi kadai cikin dukkanin al'amura, da tsarin rayuwan su baki daya duniya da lahira.

 

 

FARKON FITOWAR SHIRKA A DORON KASA:

Farko mutum ya kasance ne akan addini ta fidira da tauhidi tun daga kan Adam amincin Allah ya tabbata agareshi shirka bata bayyana ba akan wannan doron kasa sai zuwa zamanin mutanen Nuhu Amincin Allah ya tabbata agareshi sakamakon wuce gona da sukayi wurin girmama bayin Allah salihai da waliyyai, hakika mutanen sun sunyi gum aka domin su rika tunantar dasu ibada irinta mutanen su salihai bayan tsawon zamani na jikokin su sai shedan yayi masu wasiwasi dacewa lallai iayayensu basu yi hotun sub a sun ajiyesu sai domin albarkansu da matsayin su, daganan sai mutanen da suka zo bayan su suka bauta masa, sai Allah madaukaki yace: " sai sukace kada kubar allolinku kuma kada kubar wadda da suwa'a da yagusa da nasra (23)" suratu Nuhu.

Ibn abbas kogin ilimin wannan al'umma kuma masanin fassarar alkur'ani Allah ya kara masu yarda yana cewa: wannan gumaka sunayen mutanen kwarai ne salihai na cikin mutanen Nuhu, bayan an halaka su sai shaidan yayi masu wahayi cewa suyi hotunansu su ajiye a wuraren zaman su sais u rika kiransu da sunayen su domin su rika tunawa dasu, sia suka aikata hakan amma ba'a bauta masu ba har sai da wannan mutane suka mutu aka kuma shafe ilimi akan asalin wannan hotuna kafin aka bauta masu koma bayan Allah. Buhari ne ya rawaito shi.

Samuwar shirka ne a duniya ga mabanbanta bauta yana daga cikin dalilai masu kwari akan bukatar mutum ga Allah wanda zai rika bauta mawa kasancewar farkon mutane akan tauhidi suke sai dai bayan tsawon lokaci da nisan su da annabawan su da manzannin su sai shedan ya kawata masu wasu ayyuka wanda suka kasance hanyar bautawa wani abu koma bayan Allah, bautan wani abu koma bayan Allah ya karkasu zuwa ga surori dayawa daga cikin su akwai:

Bautan waliyyai da bayin Allah na kwarai kamar yadda mutanen Nuhu suka aikata, Allah madaukaki yace: " sai sukace kada kubar allolinku kuma kada kubar wadda da suwa'a da yagusa da nasra (23)" suratu Nuhu.

 • Bautan duwatsu da bishiyoyi da mutum butumi da kuma gumaka: kamar yadda mutanen Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gareshi suka akata na sassaka dutse da katako su mayar dashi alla suna bauta masa koa bayan Allah, Allah madaukaki yace: " sai yace yanzu zaku rika bautamawa abunda kuka sassaka da hannun ku bayan Allah shine wanda ya halicce ku da abunda kuke aikatawa" (suratu safat ayata 95-96).
 • Bautan taurari da rana da wata kamar yadda mutanen sarauniyar saba'a na zamanin Sulaiman amincin Allah ya tabbata agareshi wanda alhuda huda ya bashi labara akai kamar yadda muka ambata a baya, Allah madaukaki yace: " na same ta da mutanen ta suna yima rana bautama koma bayan Allah kuma shedan ya kawata masu ayyukan su ya kange su daga hanya lallai su ba shiryayyu bane (24)" suratun namli.
 • Bautar mutum kamar yadda mutanen fir'auna suka aikata, Allah madaukaki yace: " fri'auna yace yaku taron mutane shin na sanar daku wani allah ne bayana, ya hamana hadamun tsani ka tayar mun dashi zuwa sama naje na tarar da Allamn Musa lallai ina tsammanin shi cikin makaryata (38)" suratul kasas.
 • Bautan dabbobi kamar yadda mutanen Musa amincin Allah ya tabbata agareshi sukayi, Allah madaukaki yace: " sai ya fitar masu da dan maraki wanda ya kera me yin sauti sai sukace wannan shine allanku da musa wanda ya manta ya fada maku hakan (88) shin basa ganin cewa baya amsa masu Magana sannan kuma baya cucar dasu komai ko kuma amfanar dasu da komai ba (89) kuma hakika Haruna yace masu gabanin haka yaku mutanena lallai an jarabe ku ne da wannan lallai ubangijin ku shine Allah me rahama saboda haka ku bini kuma kumin biyayya cikin umurni na (90) sai sukace bazamu daina bauta mas aba har sai musa yadawo (91)" suratu daha.
 • Bautan annabawa da manzanni kamar yadda yahudawa batattu da kiristoci suka aikata, Allah madaukaki yace: " yahudawa sunce Uzairu dan Allah ne, suma kiristoci suka ce mahihu dan Allah ne, wannan maganar su ce kawai da bakunan suna maganane irin maganar kafiran da suka gabace su, Allah ya tsine masu dan me suke bacewa hanyar gaskiya suke komawa hanyar karya (30)" suratu taubah.
 • Bautan bishiyoyi kamar yadda mutanen shu'aibu amincin Allah ya tabbata agareshi suka aikata, Allah madaukaki yace: " mutanen madyana sun karyata manzanni (176) lokacin da shu'aibu yace masu shin bazakuji tsoron Allah ba (177) lallai ni manzo ne zuwa gare ku amintacce (178) kuji tsoron Allah kumun biyayya (179)" suratul shu'ara'i.
 • Bautan duwatsu da bishiyoyi da mutum butumi da gumaka kamar yadda mushrikan larabawa suka aikata, Allah madaukaki yace: " shin bakuga lata ba da uzza (19) da mana na ukun su (20) shin ku kuke da mazaje shi kuma yake da mata (21) lallai kam wannan rabo ne na zalumci (22) basu kasance ba face sunane kawai wanda suka rada masu kuke kiransu dashi ku da iyayen ku wanda Allah be saukar da wani dalili ba akan haka, babu abubda suke bi illa kawai zato da son zuciyar su, kuma hakika shiriya yazo masu daga wurin ubangijin su (23) suratun najmi.

Kenan asalin dukkanin mutanen da suka gabata shine tauhidi fadawa cikin shirka ya samo asali ne daga girmama salihan bayin cikin su, sai suka riki hotunan su da sassaka su saboda tunawa dasu na abunda suka kasance a ciki na ayyuka na kwarai da dabi'u masu kyau, wannan shine abun da manzon Allah Muhammad s.a.w ya bayyana ma Ummu Habiba da Ummu salma lokacin da suka ambata mashi cocin da suka gani a kasar habasha wand aake kira mariya, a cikin su akwai hotuna, sai manzon Allah s.a.w yace: " wa'innan sun kasance idan wani mutumin kwarai cikin su yam utu sai su gina masallaci akan kabarin sa, sai kuma su yi masa wannan hoto, wannan sune mafiya sharrin mutane a wurin Allah ranan alkiyama" sahihu muslim.

 

 

SABABIN BAYYANAR BAUTAN WANIN ALLAH:

Allah madaukaki yayi bayanin cewa hanayar samun ilimi da sani shine ta hanyar ji da gani da hankali wanda ta hanyar su ne mutum yake iya riskan da sanin abunda yake faruwa kewaye dashi cikin wannan duniya, Allah madaukaki yace: " Allah shine wanda ya fitar daku daga cikin iyayen ku baku san komai bay a kuma sanya maku ji da gani da tunani koda zaku gode masa (78)" suratun nahli.

Wannann hanya ta karkashin ta ne mutum yake ji da gani sai yayi tunani, me hankali na gaskiya shine wanda zai jayu ta hanyoyin nan zuwa ga imani da mahaliccin sa da kuma hakikanin samuwar sa, Allah madaukaki yace: " kace kuyi dubi zuwa cikin abunda suke tsakanin sammai da kassai, ayyoyi da gargadi basa amfani ga mutanen da basa imani (101)" suratu Yunus.

Sayyid kudub Allah yayi masa rahama yana cewa: da ace mutum zeyi tunani cikin halittan sa da yanayin sa, da abunda aka sanya masa na gabbai da abubuwan jikinsa masu ji da gani da tabawa, da kuma irin damar da aka masa baiwa dashi da riskan abubuwa da ya tabbatar da akwai Allah, kuma da ya shiryu zuwa gareshi da wannan abubuwa na banmaki da mu'ujizozi wanda suke nuna akan cewa lallai Allah shine mahalicci shi kadai yake kuma. Babu wani mahaluki koma bayan Allah wanda yake da ikon kirkiran wannan halitta me gagara badu cikin karamin ta da babbanta. dauki wannan jin kawia shi kadai kace yaya yake aiki? Yaya yake jin sauti ya kuma san ma'anarta? Ko kuma wannan ganin shi kadai ya yake faruwa? Kuma yaya yake yako haske da yanayin abubuwa? Ko kuma wannan tunani kawai ya yake? Kuma ya yake riskan abubuwa? Kuma yaya yake kiyasta abubuwa da yanayi, da ma'anoni da ji da riskan abubuwa? Lallai sanin hakikanin dabi'ar wannan abubuwan masu ji da gani na jikin mutum da kuma yadda suke aiki yana cikin sanin mu'ujiza cikin ilimin duniyar mutum. To yaya kake ganin halittanta da duka tsarata cikin irin wannan yanayi me tsari wacce zata dace da dabi'ar wannan duniya wanda yake rayuwa acikinta, da ace za'a rasa wani bangare guda kawai na dabi'ar wannan duniya ko kuma mutum da an rasa sadarwa, kuma da ba'a iya riskan sauti ba ko kuma haske, sai dai iko me jujjuyawa wacce ta hada tsakanin dabi'ar duniya da mutum wanda yake rayuwa acikinta sai wannan sadarwan ya samu nasara sakamakon haka, sai dai mutum baya godema akan ni'ima: << kadan ne masu godiya>>.. godiya yana faraway ne da sanin wanda yabaka wanann ni'ima, da kuma yabonsa da siffofin sa, sannan bautan sa shi kadai shine Allah shi kadai wanda alamar sa cikin halittun sa take bada sheda akan kadaitakar sa.

Saboda haka ne mafiya yawan ayoyin kur'ani me girma suna yima mutum Magana ta wannan hanyoyi kuma take kwadaitar dashi akan tunani da cikin abunda wannan hanyoyi suke isar masa na iko me girma na abunda da suke zagayen san a halittu cikin wannan duniya domin ya bayyanan masa cewa lallai basu suka halitta kawunan su ba, Allah madaukaki yace: " ko shin an halicce su ne bada komai ba ko kuma sune sukayi halittan ( 35) ko su suka halicci sammai da kasa ko dai basa basa samun sakankancewa ne (36)" suratul dhur.

Wani lokaci Magana yana kasance wa ne ga ma'abota hankula wanda suke amfani da hankulansu wwurin neman gaskiya sais u rika izina da wannan duniya wanda ake ganinta akan cewa lallai akwai Allah wanda ya samar dasu sai su san cewa ko wani abu da aka kera fa dole ne ya zama akwai wanda ya kerata kuma ko wani halitta akwai wanda ya halicce ta kuma ko wani sababi akwai wanda ya jawo sa, Allah madaukaki yace: " lallai cikin halittan sammai da kasa da canzawar dare da rana da jirgin ruwan da yake tafiya cikin kogi da abunda mutane ke amfanuwa dashi da abunda Allah ya saukar daga sama na ruwa wanda yake raya kasa dashi bayan kekashewar sa kuma ya wasa a cikinta dukkanin halittun da suke tafiya a kanta da tafiyar da iska da hazo me yawo tsakanin sama da kasa akwai ayoyi ga mutane masu hankali (164)" suratul bakara.

Wani lokaci kuma ayoyin alkur'ani suna masu kwadaitar wa da zaburarwa game da tunani dabin daki daki cikin ayoyin Allah wanda ake ganin su kuma a ake tabawa ko kuma shaker su cikin wannan duniya, Allah madaukaki yace: " daga cikin ayoyin sa ya halicce ku daga kasa sai gashi kawai kun zama mutune kunata yaduwa (20) kuma daga cikin ayiyin say a halitta maku daga kawunan ku mataye domin ku samu natsuwa zuwa garesu kuma yasanya soyayya da tausayi a tsakanin ku, lallai cikin haka akwai ayoyi ga mutane masa tunani (21) kuma daga cikin ayoyin sa ya halitta sammai da kasa da kuma banbantan yarukan ku da launukan ku, lallai cikin haka akwai ayoyi ga mutane masana (22) kuma daga cikin ayoyin sa barcin ku da kukeyi da daddare da rana kuma ku nema daga cikin falalar sa, lallai cikin haka akwai ayoyi ga mutane da suke ji (23) kuma daga cikin ayoyin sa yake nuna maku walkiya domin tsoratarwa da kuma kwadayi sannan kuma yana saukar da ruwa daga sama sai ya raya kasa da shi bayan kekashewarta, lallai cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu hankali (24) kuma daga cikin ayoyin sa sama da kasa suka tsaya da umurnin sa, sa'annan kuma idan aka kiraku daga cikin kasa sai gashi kawai kuna fitowa (25)" suratul rum.

Wani lokaci kuma ayoyin alkur'ani suna umurni dayin amfani da gani da basira na abubuwan da suke kewaye da mutum, Allah madaukaki yace: " kace kuyi dubi zuwa ga abunda cikin sammai da kasa, ayoyi da gargadi basa amfani ga mutanen da basa imani (101)" suratu Yunus.

Wani lokacin kuma ayoyin suna umurni ne da lura da natsuwa wanda zasu kai mutum zuwa ga sani, Allah madaukaki yace: " ya halicci sammai ba tare da kuna ganin wani turaku ba wanda suka tokareta ba, ya kuma jefa cikin kasa abubuwa masu nauyi wanda suke hanata rawa daku sannan kuma ya watsa cikinta dukkanin wani abu dake tafiya a doron ta ya kuma saukar da ruwa daga sama sai ya tsirar da tsirrai masu kyawun gani a ido (10) wannan halittan Allah ce ku nuna mani abunda wanda bashi ba suka halitta, hakika azzalumai suna cikin bata bayyananne (11)" suratu lukman.

Wani lokacin kuma ayoyin suna umurni ne da sauraro da yin shiru na abunda za'a fada sannan ayi tunani da kuma amsan wannan Magana da bin abun kyawun sa, Allah madaukaki yace: " shine wanda ya sanya maku dare domin ku samu natuwa a cikin sa shi kuma rana me haske domin ku nemi abincin a cikinta lallai cikin haka akwai ayoyi ga mutanen da suka kasance masu ji (67)" suratu yunus.

Wani lokacin kuma ayoyin suna umurni ne da daukan izina daga abunda suke kewayen mutum yake kuma rayuwa a tsakiyar su kuma yake amfana daga sakamakon abunda suka samarwa, Allah madaukaki yace: " llalai kunada abun izina cikin dabbobi, muna shayar daku daga cikin abun cikinta na nono wanda ake samar dashi tsakanin kashin ta da jinni sai a samar da nono fari me dadi ga masu sha (66)" suratun nahli.

Ya kuma kara cewa gar wayau: " mun kuma aiko da iska me dauke da abubuwa daban daban sai muka kuma saukar da ruwa daga sama muka kuma shayar daku shi kuma baku kuke da arzikin sa ba (22)" suratul hijri.

Ya kuma kara fadi har wayau: " ya tafiyar da ruwa kala biyu a hade a lokaci daya (19) a tsakanin su akwai Katanga wanda yake hana daya shigewa cikin daya (20) da wani irin tarin ni'mar ubangijin ku ne kuke karyatawa (21)" suratul rahman.

Ya kuma kara fadi har ila yau: " a cikin kasa akwai garuruwa rayayyu da matattu wanda tsirai basa fita daga cikin su da lambuna na inabi da shuka da dabino masu rassa da marasa rassa wanda ake shayar dasu daga ruwa daya kuma muna daukaka wani akan wani wurin yaya, lallai cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu hankali (4)" suratul ra'ad.

Sai dai ina masu hankulan suke ne wanda suke tunani da daukan izina! Saboda haka ne Allah ya zargi mutanen da basa amfani da wannan gabbai nasu na ji da gani da hankali cikin alkur'ani wurin yin tunani da duba da lura ya siffatasu da kurame da bebaye da kuma makafi wanda wannan kafafe nasu da Allah ya halitta masu basa shiryar dasu zuwa ga gaskiya, Allah madaukaki yace: " hakika mun halittama wutan jahannama dayawa cikin mutane da aljanu, sunada zuciya amma basa tunani da ita haka kuma sunada idanuwa amma basa gani dasu kuma sunada kunnuwa amma basa ji dasu, wa'innan Kaman dabbobi suke koma sunfisu bacewa, kuma wa'innan sune rafkanannu (179)" suratul a'araf.

Hakika alkur'ani me girma ya bayyana manyan dalilan da suke dawo yaduwar bautan wanin Allah domin bayin sa ku sansu su kuma nuisance su kada su fada cikin su kamar yadda wasunsu suka fada:

 1. Koyi da bin iyaye kakanni ido rufe ba tare da tambayar sa dalilin sa ba na aikata haka (takalidanci) da binsu cikin ibadar su da al'adar su koda kuwa hakan ya kasance bata ne hankali baya karbansa kuma fidira ta daidai tana wurgi dashi ba tare da tabbatarwa ba ko kuma tambaya, Allah madaukaki ya aibanta mutanen da suke koyin iyayen su wanda basa amfani da hankalin su wurin neman gaskiya, Allah madaukaki yace: " idan akace masu kuzo zuwa ga abunda Allah ya saukar sai suce mu dai abunda muka samu iyayen mu akai ya ishemu, koda kuwa iyayen nasu basusan komai ba kuma basa shiryuwa (104) " suratul ma'ida.
 2. Makauniyar biyayya ga shuwagabannin addini batattu hakan na faruwa ne da amsar maganar su da bin ayyukan sub a tare da tankadewa ba da kuma tambayar dalili akan haka, Allah madaukaki yace: " sun rike malaman su da fastocin su abun bauta koma bayan Allah da masihi dan marya kuma ba'a umurce suba sai su bautama shi kadai wanda babu abun bauta da gaskiya bisa cancanta sais hi, tsarki ya tabbata a gareshi game da abunda suke masa shirka dasu (31)" suratul tauba.

Biyayyar da akayi umurni da ita itace cikin kyakyawan aik, ita kuma gaskiya ba'a gane ta da yawan mabiya ko kuma daukakan shuwagabannin ta, ita gaskiya ana gane ta ne da dalilai na ayoyi da hadisai, Allah madaukaki yace: " idan kabi mafiya yawan mutanen duniya zasu batar dakai hanyar Allah, ba komai suke bi face zato da kaddarawa kawai (116)" suratul an'am.

 1. Makauniyar biyayya ga shuwagabanni da masu mulki saboda samun shiga a wurin su da kwadayin abun hannun su na rayuwan duniya na dukiya da dabbobi da gonaki ko kuma kwadayin matsayi da shugabanci, llah madaukaki yace: " lallai Allah ya tsine ma kafirai kuma ya tanadar masu da wutan sa'ir (64) suna masu dawwama acikinta har Abadan bazasu samu me taimako ba ko majibincin al'amarin su ba acikin ta (65) a ranar da za'a kifa fuskokin su a wuta zasu rika cewa kaicammu da munyi wa Allah biyayya kuma da munyi wa manzon Allah biyayya (66) suna cewa ya ubangijin mu lallai munyi biyayya ne ga shwagabannin mu da manyan mu suka batar damu hanyar gaskiya (67) ya ubangijin mu ka nunnun ka masu azaba kuma ka tsine masu tsinuwa babba (68)" suratul ahazab.
 2. Bin son zuciya da abunda rai ke so na abunda shedan ke kawata da cusawa cikin zukatan sun a ganin kyawun ra'ayoyin su da kuma abunda yake karkata gareshi wanda zai cika biya masu bukatar sun a sha'awa da burukun su sais u canja ma'anar aya ko hadisi domin tabbatar da wannan abun da suke so ba tare da komawa zuwa ga ilimi ba ko kuma hankali, Allah madaukaki yace: " idan basu amsa maka ba ka sani cewa lallai son zuciyar su suke bi, wanene yafi bacewa akan mutumin dake bin son zuciyar sa ba tare da wani shiriya ba daga Allah, lallai Allah baya shiryar da mutane azzalumai (50)" suratul kasas.
 3. Girman kai da rudu zasusan ayoyin llah cikin wannan duniya da abunda suke nuni akai sai dai girman kai da rudu shi yake hanasu imani da Allah wanda ya halicce su kamar yadda fir'auna ya aikata ma Musa alokacin daya kirashi zuwa ga bautama Allah, Allah madaukaki yace: " sai fir'auna yace wanene kuma ubangijin talikai (23) sai annabi musa yace shine ubangijin sammai da kasa da abunda ke tsakanin sui dan kun kasance masu sakankancewa (24) sai fir'auna yacema na gefen sa bakwajin abunda yake fadi ne (25) sai annabi musa yace ubangijin ku da iyayen kun a farko (26) sai fir'auna yace lallai wannan manzon da aka aiko maku mahaukaci ne (27) sai annabi musa yace ubangijin mahudan rana da mafadan rana da abunda ke tsakanin su in kun kasance masu hankalta (28) sai fir'auna yace idan ka kuskura ka riki wani abun bauta bayan ni to lallai zan kulleka (29)" suratul shu'ara'i.

Wannan girman kan da rudu da ji dakai yana gushewa a halin rauni da hali na karancin dabara da iko kamar yadda ya gushema fir'auna lokacin da igiyar ruwa ya shanye shi ya nutse cikin ruwa dimuwar mutuwa tazo mishi sai ya koma zuwa ga fidirar sa wacce ta nuna mashi akwai Allah amma babu lokacin nadama, Allah madaukaki yace yana me bada labara akanshi: " sai muka ketarar da bani isra'ila rafi sai fir'auna ya biyo su da rundunar sa saboda zalumci da kiyayya, bayan ya nutse cikin ruwa sai yace nayi imani da cewa babu abun bautawa da gaskiya bisa cancanta sai wannan Allah wanda bani isra'ila sukayi imani dashi kuma nima nazama cikin musulmai (90) yanzu ne zakayi imani bayan ka saba a baya kuma ka kasance cikin masa barna (91) a yau ne zan tsiratar da gangar jikinka domin ka kasance aya ga mutanen da zasu zo bayan ka, kuma lallai dayawa cikin mutane masu rafkana ne daga ayoyin mu (92)" suratu yunus.

Ko kuma ya zama cewa inkarin da sukeyi da bautan Allah domin taurin kai ne sai ya zama suna mayar da gaskiya da yakanta da kuma jayayya da abubuwa na gaskiya wanda suke nuni akan samuwar Allah sai su doge cikin batar su da jahilcin su, allah madaukaki yace: " sun karyata ta kuma zukatansu ya natsu da ita saboda tsabar zalumci da girman kai ka kalla ka gani yaya karshen masu barna zai kasance (14)" suratun namli.

 1. Ko kuma saboda maslahar su ta kashin kansu wacce zasu samu karkashin sanya mutane bautan wanin Allah, wannan maslahar ta al'umma ce baki daya kamar samun shugabancin addini ko kuma siyasa cikin al'umma su rika jujjuya mutanen ciki dan samun maslahar su, ko kuma maslahar kudi wanda zasu rika tasa daga mabiyan su kamar yadda muke gani daga wurin shuwagabannin su da masu tsare addinan, Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani lallai dayawa daga cikin fastoci da fadoji suna cin kudin mutane ne kawai da barna kuma suna toshe mutane daga hanyar Allah, wanda suka mallaki dukiya na zinari da azurfa masu tarin hyawa kuma basa ciyar da ita a tafarkin Allah ka masu bishara da azaba me radadi (34)" suratul tauba.
 2. Tarin dukiya da ni'ima wacce take mantar da mutum mahaliccin sa: hakika zai iya kasancewa babban sababi wanda yake sanya mutum bautan wanin Allah shine tsoron da masu kudi sukeyi na gushewar ni'imar da suke ciki saboda bautan Allah zaisa su rasa dayawa daga cikin abunda suke ciki na tarin dukiya wacce aka ginata akan zalunci na cin dukiyoyin mutane da barna da riba da boye kaya sai sunyi tsada da agushi da makamantan su, Allah madaukaki yace: " bamu aika wani me gargadi ba zuwa ga wani gari face masu kudin cikinta sunce mu dai mun kafirta da abunda aka aiko ku dashi (34)" suratu saba'i.
 3. Hajilci: jahilci yana daga cikin yan adawar mutum wanda suke turashi ramin bata da duhu sai su jagoranci mutum kamar yadda ake jagorantar sanuwa sai suyi amfani da wannan hajilci wurin bautawa wanin Allah, Allah madaukaki yace: " kace masu yanzu wanin Allah kuke umurta na da na bautamawa yaku jahilai (64)" suratul zumar.
 4. Daskarewan hankali ta yadda bazasu rika tunani da itaba cikin ayoyin Allah wanda suke kewaye dasu ko kuma abunda suke nuni akai wanda zasu nuna masu hanya ta kwarai ta kuma tsiratar dasu cikin abun da suke ciki na bata rudani, Allah madaukaki yace: " lallai wanda sukafi jin tsoron Allah cikin bayin sa sune malamai, kuma lallai Allah mabuwayi ne kuma me gafara (28)" suratu fadir.
 5. Masu bautar da mutane ta hanyar mayar dasu bayi na mulkin mallaka wanda zasu rika masu aiki da karfin su wanda ta wannan hanyar ne zasu rika yada wayewar su ta bautan wanin Allah cikin mutane wanda zasu samu daman tabbatar da maslahar su da burin sun a mallake wannan mutane da kuma yada sharrin su, hakan yan afaruwa ne ta hanyar tsoratar dasu da abubuwa na wahala wanda zata nesantar dasu daga tunanin duniya da kuma aiki da abunda da suke fada masu sai su rika tafiyar dasu cikin rayuwa ta kanzon baka da rudani, Allah madaukaki yace: " sai mai mulki cikin mutanen fir'auna yace yanzu zaka bar musu da mutanen sa su rika barna a doron kasa bayan sun bar bauta maka da allarka, sai yace zamu rika kashe mazajen su muna barin matansu lallai mu masu karfi ne akan su (127)" suratul a'araf.

Sayyid kudub Allah yayi mashi rahama yana cewa: lallai wasu mutune a zamanin nan namu suna aiwatar da abubuwan jahiliyya wanda suke aikata su cikin wannan nau'o'i dayawa:

Wasunsu suna karyata Allah madaukaki, da kuma inkarin cewa akwai Allah… lallai wannan aikin hajiliyya ce ta bangaren imani da kuma sawwarawa, kamar mutanen shuyu'iyyin na cikin jahiliyya.

Wasun su kuma kuma suna kwatanta Allah da wani abubuwa na bauta, da kuma canza bautan Allah da alamomin su cikin addini da biyayya, kamar mutanen jahiliyya masu bautan gumaka cikin kabilar hunud da sauran su da kuma mutanen jahiliyya na yahudawa da kiristoci.

Wasun su kuma suna tabbatar da akwai Allah ta fuska na kwarai, da kuma bauta masa tare da canza wani abu me muni cikin sawwara abun da shedawa babu abun bautawa da gaskiya bisa cancanta kuma lallai Muhammad manzon Allah ne suka kunsa, tare da shirka cikin bautan su da biyayya. Kamar jahilan nan wanda suke kiran kansu da sunan <<musulmai>> suna tsammanin sun mika wuya da kuma sun samu siffan musulunci da hakkokin sa da zaran sun furta Kalmar shahada da kuma yin ayyukan bauta na wannan addini, tare da mummunan fahimtar su da ma'anar Kalmar shahadar kuma tare da mika wuyan su da bautama wanin Allah cikin mutane.

 

 

 

HATSARIN BAUTAN WANIN ALLAH:

Lallai dukkanin zunubai da sabo wanda bawa yake aikatawa ana gafarta su da yardan Allah da kuma kawar da kai akansu, Allah madaukaki yace: " kace yaku bayina wanda suka aikata barna akan kawunan su kada ku cire tsammani daga samun rahamar Allah, lallai Allah yana gafarta zunubai baki dayan su… (53)" suratul zumar.

Sai dai shirka kawai, lallai itace babbar zunubi wanda aka sabama Allah da ita a doron kasa saboda haka baya gafarta wa wanda yayi masa shirka kuma baya yin rahama ga wanda yake aikata shi, Allah madaukaki yace: " lallai Allah baya gafarta laifin shirkan da aka masa amma yana gafarta duk wani laifin da ba wannan ba gawanda yaso, duk wanda yayima Allah shirka to hakika ya bace bata me nisa (116)" suratun nisa'i.

Duk yadda zunubai sukayi yawa kuma ma'aunin wanda ya aikatasu nayi nauyi dasu amma ya riske Allah baya masa shirka da komai to lallai zai samu Allah me yawan gafara ne kuma me rahama kamar yadda Allah ya fada akansa cewa: " duk wanda ya aikata aikin kyakyawa yana da lada goma kwatankwacin wannan aiki kuma ina karawa akan haka, kuma duk wanda ya aikata mummunan aiki to sakamakon ta shine zunubi irinta ko kuma na yafe masa, koda mutum zai aikata aikin zunubi ne kwatankwacin girman kasa sai ya hadu da Allah baya masa shirka to Allah zai zo masa da gafara kwatankwacin wannan ayyuka nasa na zunubi" sahihu muslim.

Shirka it ace zunubin da ceto ayyukan kwarai na meyinta baya amfanansa komai yawan su, Allah madaukaki yace: " sai muka zo da abunda suka aikata na kwarai sai muka watsar dasu kamar bushashen yayi (23)" suratul furkan.

Sannan kuma makomar duk wanda ya mutu yana shirka shine haramun ne ya shiga aljanna zai dawwama acikin wuta, Allah madaukaki yace: " lallai wanda suka kafurta cikin ma'abota littafi da mushrikai suna cikin wutan jahannama zasu dawwama acikinta, kuma wa'innan sune mafiya sharrin halittu (6)" suratul bayyinah.

Lallai duk me nazari cikin duniyar mu tayau zai ga cewa bautan wanin Allah ya yadu, kuma daga cikin abun takaici da bakin cikin shine zakaga cewa dayawa daga cikin mutane masu ilimi suna alaka da bautan mahaluki irin su kamar kiristoci wanda suke ikirarin cewa masihi dan Allah ne da yahudawa wanda suma suke ikirarin cewa Uzairu dan Allah ne, Allah madaukaki yace: " yahudawa sunce Uzairu dan Allah ne haka kuma kiristoci suma sunce masihu dan Allah ne, wannan maganar su ce kawai da bakunan su, suna kwaikwayon maganar mutanen da suka kafirta gabanin su, Allah ya tsine masu, dan me yasa basa bin gaskiya suke karkata zuwa ga karya (30) sun riki fastocin su da fadojin su abun bauta da biyayya koma bayan Allah da misihu dan marya kuma ba'a umurce su ba sais u bautawa Allah shi kadai, babu wani abun bauta dagaskiya bisa cancanta sai shi, tsarki ya tabbata a bareshi daga abunda suke masa shirka dashi (31)" suratul tauba.

Zakaga wasu kuma suna bauta da girmama bishiya ko dutse ko kuma dabba, abun takaicin shine akwai dayawa daga cikin wanda suke ikirarin musulunci cikin musulmai wanda suke shirka cikin bautar su, suna kiran matattu cikin salihan bayi ko annabawa kuma suna kudurta cewa suna da iko cikin abunda babu me iko da hakan sai Allah, suna kuma neman taimako daga gare su, da neman agajin su domin biya masu bukatur su da yaye masu damuwan su na warkan da marasa lafiya ko kuma samun yara ko kuma sawwake wata bukatar su, suna dawafi a wurin kaburburan su suna neman tabarrakin su dayin yanka domin su, kuma suna kudurta cewa lallai suna fa amfanarwa ko kuma cucarwa, Allah kuma yana cewa: " wanene yafi bata akan mutumin da yake kiran wani abu koma bayan Allah wanda bazai taba amsa mashi ba har tashin alkiyama, kuma su gafalallu ne game da addu'o'in su (5)" suratul ahkaf.

Saboda haka ne musulunci ya haramta dukkanin wasu hanyoyi da dalilai wanda zasu alakanta mutum da wanin Allah kamar daura laya da kambu ko kuma rataya laya ko wani abu a gida da kudurta cewa suna jawo amfani ko kuma suna kawar da cucarwa da kuma kudurta cewa taurari da wata suna da tasiri cikin rayuwan mutum, da makamantan haka duk anyi haka ne domin toshe kafa wanda zata kai mutum zuwa ga shirka ga Allah da kuma yanke dukkanin wata hanyar da zata alakanta mutum ko kuma yin kawakkali ga wanin Allah, Allah madaukaki yace: " idan ka tambaye su cewa wanene ya halicci sammai da kasa dasannu zasu ce maka Allah ne, to kace masu shin kuna ganin cewa wannan abubuwan da kira koma bayan Allah idan Allah ya nufe da wani cuta zasu iya yaye itace ko kuma idan ya nufe ni da wata rahama zasu iya rikewa su hana samuwar wannan rahamar tashi, kace masu Allah ya wadatar mun, kuma a gunsa ne masu dogaro suke dogaro (38)" suratul zumar.

 

 

 

HAKIKANIN ABUN DA AKE BAUTAMAWA KOMA BAYAN ALLAH:

Lallai dukkanin abunda ake bautamawa koma bayana Allah na alloli bazasu iya halittan koda kuda ba koda kuwa zasu hadu ne dukan su akan haka ko kuma kwayan zarra bare ace zasu iya hukunta wani abu ko kuma su rika jujjaya duniya ko kuma su jawo wani amfani ko kawar da wata cucarwa, wannan Magana kuma tananna a matsanin kalu bane har zuwa ranan tashin duniya, Allah madaukaki yace: " yaku mutane an buga misali ku saurari kuji misalign, lallai wanda suke kiran wani abu koma bayan Allah basa taba iya halittan koda kuda ne sannan kuma da kuda zai kwace masu wani abu bazasu iya kwaton kayansu ba daga gareshi, tabbas da me neman da wanda ake nema agunsa duk sun samu rauni (73)" suratul hajj.

Alkur'ani ya bayyana cikin ayoyi masu yawa hakikanin haka na shirka sannan kuma tayi masu bautan haka Magana wanda suke zaton cewa arziki yana hannun su da taimakon su da rayuwan su da lafiyar su da rabasu da dukkanin abunda zai sa suna rokon su kuma da cewa su rika biyayan kawunan su cikin abunda suke ciki na bata da jahilci, banbanci ne mara misiltuwa tsakan mahalicci da wanda aka halitta, haka kuma akwai banbanci mara misiltuwa tsakanin mahalicci me karfi wanda komai ke hannun sa da ikon sa da kuma allaolin da aka halitta su masu raunin gaske wanda asalin su ya ginu ne akan dimuwa da kanzon kurege, misali mazauna yankin kasashen larabawa kafin zuwan musulunci sun kasance suna kera gumakan su daga komai harda sinadari makaskanci wasu suna kerawa ne da dabino idan sunji yunwa kuma basu samu abinci ba sais u cinye wannan gunki nasu, sahabi Abu Raja'a Allah ya kara masa yarda yana cewa: mun kasance muna bautan dutse sai muta hada sassan sa daga kasa daganan kuma muka zo da akuya muka yanka masa bayan haka kuma mukayi masa dawafi. Sahihul buhari.

Ma'abota hankula kuma da tunani suna gane kura kuran su sannan suna fatali da akidar su da zaran sun gane gaskiya, ga wannan sahabin me suna Rashid dan Abdu rabbahu assulami Allah ya kara masa yarda kafin musuluntar sa yaje gun gunkinsa kamar yadda ya saba domin neman kusanci zuwa gareshi kuma ya roke shi da neman wasu bukata a wurin sa, bayan yaje sai yaga dila yana fitsari akan wannan gunki sai ya tsaya yana mamaki da tunani daganan ya farka cikin abunda yake ciki na bata sai ya fadi wasu baituka yana ma wannan gunki isgilanci da cewa:

Ubangiji wanda dila yakema fitari akai*** hakika ya kaskanta duk wanda dila ya masa fitsari akai.

Da ace ubangijin zai iya hana wani abu na cucarwa akan sa*** babu alheri ga ubangijin da bukata yake cikin siffar sa.

Na barranta daga gumakan a duniya baki dayan su*** nayi imani da Allah me gagararre.

Abu nu"aim ya rawaito shi da suyudi cikin littafin kasa'isul kubura cikin siratun nabawiyya na Ibn kasir da kuma cikin littafin dala'ilun nubuwwa na Abi nu'aim al asbahani da kuma littafin subulul huda warrashad, fi sirati kairul ibad na Muhammd bn Yusuf assalihi ash-shami.

Wannan itace kwakwalwa me lafiya da fidira na kwarai wacce take komawa kan gaskiya da zarar ta bayyanan mata, dayawa cikin ayoyin alkur'ani suna Magana ne ga mutane masu irin wannan hankula me lafiya tana kuma umurtan su dayin tunani cikin hakikanin wannan abubuwan da suke bautamawa koma bayan Allah tana kuma zaburar dasu domin su tsira daga cikin wannan jahilci da dimuwa, duk wanda yake bautawa wanin Allah ya saurara da tunani ikin wannan ayoyi raunin allolin su zai bayyanan masa wanda suke bauta mawa kuma suka kasa amfanar da kawunan su to ina zasu iya amfanar da wanin su, sannan kuma abunda suke bautamawa basu da fiffofi masu yawa wanda suka zama wajibi a same su ga Allah wanda ya cancanci bauta, karshen wauta da jahilci shine ka riki abun bauta wanda baya iya amfanar dakai komai ko kuma cucar dakai da komai haka kuma baya iya kashe ka ko kuma rayaka haka kuma basa iya tayar da matattu, Allah madaukaki yace: " suna shirka da bautan abunda bazasu iya halittan komai sai dai su a halitta su (191) kuma basa iya taimakon su dakomai haka kuma basa iya taimakon kawunan su dakomai (192) idan ka kirasu zuwa ga shiriya bazasu biku ba, daya yake dacewa kun kirasu ko kuma kunyi shiru (193) lallai wanda suke bautama wanin Allah halittu irin su, to ki kirasu muji sais u amsa maku mugani idan kin kasance masu gaskiya (194) shin sunada kafa wanda suke tafiya da ita ko kuma suna da hannu wanda suke taba abu dashi ko kuma suna d aido ne wanda suke ganin abubuwa dashi ko kuma sunada kunne ne wanda sukejin Magana dashi, kace masu ku kira mataikamanku sai kumun makirci kada ku saurara mani (195) lallai majibincin al'amura na shine Allah wanda ya saukar da littafi kuma shine yake jibintar al'amuran salihai (196) abunda kuke bautamawa koma bayan Allah basa iya taimakon ku ko kuma taimakon kawunan su (197) idan ka kirasu zuwa ga shiriya basaji zaka gansu suna kallonka amma basa gani (198)" suratul a'araf.

 

Tana umurtan ma'abota wannan hankula me lafiya da nazari da tunani cikin abubuwan da suke cikin sammai da kasa da halittun da Allah ya halitta a cikin su ya kuma watsa halittu a cikin su masu tafiya aciki abunda zai gamsar da hankali me lafiya wajabcin bautan wanda ya samar dasu shi kadai ba tare da anyi masa tarayya ba, Allah madaukaki yace: " kace godiya ta tabbata ga Allah sannan kuma aminci ga bayina wanda na zabe su, shin Allah shine yafi alheri ko kuma abunda suke ma Allah shirka dashi (59) ko kuma wanda ya halicci sammai da kasa ya kuma saukar da ruwa daga sama sai ya raya gonaki dashi masa kyawun kallo wanda baku isa ku fitar da bishiyoyin sub a, shin akwai wani abun bauta ne tare da Allah, hakika sun kasance mutane marasa adalci (60) ko kuma wanda ya sanya kasa tabbatacciya gu daya ya kuma yansa koramu a tsakanin taya kuma sanya mata kayan nauyi wanda suka danneta ya kuma sanya takanga tsakanin ruwan rafi guda biyu mabanbanta ruwa, shin akwai wani abun bauta ne tare da Allah, hakika dayawan su basu sani ba (61) ko dai wanda yake yake amsa kiran wanda yake cikin kunci idan ya kirashi kuma yake yaye damuwa ya kuma sanya ku kalifofi abayan kasa, shin akwai wani abun bauta ne tare da Allah, kadan ne masu tunani (62) ko dai wanda yake shiryar daku cikin duhun dare cikin kasa da kogi da kuma wanda yake aiko da iska me bishara game da rahamar sa, shin akwai wani abun bauta ne tare da Allah, Allah ya tsarkaka daga abunda suke masa shirka dashi (63) ko dai wanda ya kirkiri halitta kuma zai sake maimaitata da kuma wanda yake azurta ku daga sama da kasa, shin akwai wani abun bauta ne tare da Allah, kace ku zo da naku hujjojin idan kun kasance masu gaskiya (64) kace babu wanda yasan abunda ke cikin sammai da kasa na gaibu sai Allah, kuma basu san lokacin da za'a tayar dasu ba (65)" suratun namli.

Ayoyin alkur'ani sunyi bayanin abunda ake bautamawa koma bayan ta fuska biyu:

 

Hakikanin abunda ake bautamawa koma bayan Allah a duniya:

Lallai ayoyin alkur'ani suna kore siffofi na cika wanda suka zama wajibi a samesu ga dukkanin Allah na gaskiya tattare ga wannan abubuwan da ake bautamawa koma bayan Allah cikin misali na hankali kamar haka:

 • Allah madaukaki masani ne akan komai kuma ya karade komai, Allah madaukaki yace: " wanda suka kafurta sunce tashin alkiyama bazata zo man aba kace masu a'a ina rantsuwa da ubangijina masanin gaibu sai ta zo maku babu abunda yake boye masa koda kwatankwacin kwayan zarra ne cikin sammai da kasa ko kuma abunda yake bekai wannan girma ba ko kuma wanda yafi shi girma face yana cikin littafi bayyananne (3)" suratu saba'a.

Wannan abubuwan da ake bautamawa suna da kasawa ta bangaren ilimi basusan komai ba daga bukatuwar mutane ko kuma halinsu, Allah madaukaki yace: " lallai abunda kuke bautamawa koma bayan Allah halittu ne irin ku, ku kira su mu gani sai su amsa maku idan kun kasance masu gaskiya (194)" suratul a'araf.

 • Allah madaukakin sarki me iko ne akan komai babu wani abu daya gagareshi cikin sammai da kasa, cucarwa da amfanar wa a hannun sa suke, Allah madaukaki yace: " shin basu gani ba cewa lallai Allah shine wand aya halicci sammai da kasa kuma yana da ikon kara halittan irin su ya kuma sanya masu lokaci wanda babu kokwanto acikin sa sai dai azzalumai sunki bauta masa sai dai kafurci (99)" suratul isra'i.

Wannan abubuwan da ake bautamawa koma bayan Allah sun kasa ta fuskar iko, basu da mallakin komai basa iya yawo wani amfani ko kuma kawar da wani cuca akan kawunan su ina ga wanin su, Allah madaukaki yace: " kace masu yanzu kuna bautama wasu abubuwa koma bayan Allah wanda basa iya cucar daku ko kuma amfanar daku da komai, lallai Allah shine meji kuma masani (76)" suratul ma'ida.

 • Allah madaukaki yana da mulki kai tsaye cikakke cikin sammai da kasa, Allah madaukaki yace: " ga Allah ne mulkin sammai da kasa yake, ranan tashin alkiyama rana ce wanda masu barna zasuyi asara (27)" suratul jasiya.

Wannan abubuwan bautan koma bayan Allah sun gaza ta fusakar mulki basu da iko warewa da mulkin komai cikin wannan duniya hasali ma sune ake mulka, Allah madaukaki yace: " kace masu ku kira abunda kuke tsammani koma bayan Allah, basu mallaki kwatankwacin kwayan zarri ba cikin sammai ko kuma a cikin kasa sannan kuma basa mallaki komai ba nasu nakan su ko kuma wanda suke da tarayya dashi, kuma basu da wani abu da zasu iya taimakon sa dashi (22)" suratu saba'a.

 • Allah madaukaki shien ya halicci komai ya kuma samar dashi daga rashin sa, Allah madauakaki yace: " wancan shine Allah ubangijinku babu abun bautawa da gaskiya bisa cancanta sais hi, shine mahaliccin komai ku bauta mashi, kuma shine wakili akan komai (102)" suratul an'am.

Wannan abubuwan bautan koma bayan Allah sun gaza da su halicci koda kwayan zarra ne, Allah madaukaki yace: " kace masu shin akwai wani cikin allolinku wanda ya kirkiri halitta sannan kuma zai kara maimaitata, kace masu Allah ne wanda ya kirkiri halitta kuma shine zai kara maimaitata, to dan me yasa suke karkata daga gaskiya su koma bin karya (34)" suratu yunus.

 • Allah madaukaki shine wanda yake jujjuya wannan duniya yake gudanar da ita karkashin tsarin da ya halicce su akai wanda baza sabawa akan haka, Allah nadaukaki yace: " lallai ubangijinku Allah shine wanda ya halicce sammai da kasa cikin kwanaki shida sannan ya daidaita akan al'arshin sa, shine yake jujjuya al'amura babu wani me cuto face da izinin sa, wannan shine Allah ubangijinku saboda haka ku bauta mashi, shin bazakuyi tunani ba (3)" suratu yunus.

Wannan abubuwan bautan koma bayan Allah sukan su jujjuya su akeyi saboda haka sun gaza wurin jujjuya komai cikin halittun Allah na daban, Allah madaukaki yace: " babu wani halitta cikin sammai da kasa face ta zoma Allha me rahma a matsayin me bauta (93)" suratu Maryam.

 • Allah madaukaki shine me azurtawa me karfi kuma mabuwayi yana kora arziki ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso, shine ya dauki nauyin azurta dukkanin halittu ya kuma tanadar masu hanyoyi wanda zasu rika isa zuwa ga haka, Allah madaukaki yace: " sau dayawa daga cikin dabbobi wanda bata iya mullakan abincinta Allah shine wanda yake azurtata daku baki daya, shi kuma me ji ne kuma me gani (60)" suratul ankabut.

Wannan abubuwan bautan koma bayan Allah sun gaza ta fusakar arziki basa iya jawo maku arziki ko kuma hanaku arziki, Allah madaukaki yace: " kace masu wanene yake azurtaku daga sama da kasa ko kuma wanene ya mallaki ji da gani kuma yake fitar da rayayye daga macacce ya kuma fitar da matacce daga rayayye kuma wanene yake jujjuya al'amura, da sannu zasu ce maka Allah ne, kace masu to dan me yasa bazakuji tsoron Allah ba kuyi takawawa (31)" suratu yunus.

 • Allah madaukaki shine rayayye rayuwa ta hakika baya mjutuwa kuma baya karewa taya hakan zai kasance dashi bayan shine ya halicci mutuwa tsarki ya tabbata agareshi, bashi da farko kuma bashi da katrshe kuma bashi da wani mataimaki wanda yake daukan nauyin al'amuran halittun sa, bazasu dawwa ba idan babu shi, Allah madaukaki yace: " shine rayayye babu abun bautawa da gaskiya bisa cancanta sai shi saboda haka ku bauta mashi shi kuna masu kadaitashi cikin bauta, godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai (65)" suratul gafir.

Wannan abubuwan bautan koma bayan Allah abunda samun sauran halittu na mutuwa da karewa suma yana samun su sunada farko kuma sunada karshe sun gaza tsayuwa a Karin kansu ina ga su tsayu ga al'amuran wasu, basusan yadda za'ayi dasu ba taya zasusan yadda za'ayi da wasun su, Allah madaukaki yace: " kada ba bautama Allah da wani abun bauta na daban, babu abun bautawa dagaskiya bisa cancanta sais hi, komai me halaka ne sais hi kadai zai saura shi ke da hukunci kuma wurin shi za'a koma (88)" suratul kasas.

 • Allah madaukaki shine me rayawa da kashewa, yana raya wanda yaso cikin halittun sa yakai shekarun da ya rubuta masa sannan yana kashe wanda yaso cikin halittun Sa lokacin haihuwar su ko kuma suna kanana, Allah madaukaki yace: " lallai shine shine me mulkin sammai da kasa yana rayawa da kuma kashewa, kuma baku da wani majibincin al'amura ko kuma mataimaki koma bayan sa (116)" suratu tauba.

Wannan abubuwan bautan koma bayan Allah basu da ikon komai cikin wannan facema basa iya hana kan su mutuwa, Allah madaukaki yace: " sun riki alloli abun bauta koma bayan Allah wanda basa halittan komai sai dais u aka halitta sannan kuma basa iya mallama kawunan su cucarwa ko kuma amfanarwa kuma basu mallaki mutuwa ba ko kuma rayuwa ko kuma tayarwa (3)" suratul furkan.

 •  Allah madaukaki shine wanda yake lura da arzikin dukkanin halittun sa wanda ake gani da wanda ba'a gani na mutane da dabbobi da tsuntsaye da kwari da sauran su, Allah madaukaki yace: " lallai Allah shine me azurtawa me karfi da yalwa (58)" suratul zariyat.

Wannan abubuwan bautan koma bayan Allah sun gaza ciyar da kansu taya zasu iya ciyar da wasu, Allah madaukaki yace: " lallai abunda kuke bautamawa koma bayan Allah gumaka ne kuma kuna kirkiran karya, lallai wanda kuke bautamawa koma bayan Allah basu azurta ku da komai ku nemi arziki a wurin Allah kuma ku bauta mashi kuma ku gode mashi, kuma gareshi zaku koma (17)' suratul ankabut.

 • Allah madaukaki meji ne kuma yana gani, yana jin addu'ar kuma yana amsama wanda yake cikin kunci ya kuma biya bukatan masu bukata yana kuma yaye damuwa ya kuma warkar da mara lafiya, Allah madaukaki yace: " ko wanene yake amsawa wanda yake cikin damuwa addu'ar sa idan ya roke sa kuma yake yaye damuwa kuma yasanya ku kalifofi a bayan kasa, shin akwai wani abaun bautane tare da Allah, kadan ne suke tunani (62)" suratun namli.

Wannan abubuwan bautan koma bayan Allah basa mallaki komai ba cikin haka, Allah madaukaki yace: " kira na gaskiya a wurin sa yake, wanda suke kira koma bayan Allah basa iya amsa masu da komai sai kamar mutumin daya shinfida hannunsa akan ruwa domin yakai bakin sa, bazai taba kaiwa ba kuwa, addu'ar kafirai bata kasance komai ba face cikin bata (14)" suratul ra'ad.

 

Hakikanin abunda ake bautamawa koma bayan Allah ranan alkiyama:

Saboda Allah madaukaki ya hana mutum bautan wanin sa ko kuma dogaro ga wanin ya ambaci makomar wanda yayi wanin Allah biyayya da bauta ko kuma sanyama Allah kishiya a lahira, sai Allah madaukaki yace: " lallai ku da abunda kuke bauta mawa koma bayan Allah makamashin wutan jahannama ne wanda zaku shigata (98) da ace wannan alloli ne da basu shigeta ba, ko wanne acikinta zai dawwama (99) a cikinta akwai fitar rayukan su kuma bazasu rika jib a acikinta (100)" suratul anbiya'i.

 • Hakikanin abunda ake bautamawa koma bayan Allah a lokacin mutuwa, Allah madaukaki yace: " wanene yafin zalumci fiye da wanda ya kirkiri karya akan Allah ko kuma ya karyata ayoyin sa, wa'innan sune wanda rabon su zai same su daga cikin littafi, har idan mala'ikun mu sukazo amsan rayukan su sai suce masu ina abunda kuka kasance kuna bautamawa koma bayan Allah, sai suce sun bace mana bamu gansu ba sunyi sheda akan kawunan su cewa lallai su kafirai ne (37)" suratul a'araf.
 • Hakikanin abunda ake bautamawa koma bayan Allah a lokacin hisabi shine kaskanci da nadama, Allah madaukaki yace: " a ranar da za'a ce masu ku kira allolin wanda kuke tsammani zasu cecuku, sais u kirasu amma bazasu amsa masu ba sai musanya wani rami a tsakanin su cikin wutan jahanna (52)" suratul kahfi.
 • Hakikanin abunda ake bautamawa koma bayan Allah a lokacin hisabi shine janyewa da nadama, Allah madaukaki yace: " a ranar da za'a tayar dasu gabaki dayan su sai muce ma masu shirka ku hadu wuri daya ku da wanda kuke bautamawa sai mu yamke tsakanin su, sai wanda suka bautamawa suce masu mu bamu kuka bauta mawa ba (28)" suratu yunus.
 • Hakikanin abunda ake bautamawa koma bayan Allah a lahira shine jayayya da kiyayya, Allah madaukaki yace: " sun rika koma bayan Allah alloli su zaman masu mataimaka (81) al'amarin bah aka yake ba da sannu zasu kafurce ma bautan da suka masu kuma su zaman masu makiya (82)" suratu Maryam.
 • Hakikanin abunda ake bautamawa koma bayan Allah a ranan alkiyama shine me bautan da wanda aka bautamawa duk suna cikin wutan jahannama, Allah madaukaki yace: " lallai ku da abuda kuke bautamawa (162) abunda kuka kasance akansa na bata (162) sai wanda Allah ya rubuta mashi shiga wuta (163)" suratu safat.

 

 

FA'IDOJIN BAUTAN ALLAH:

Bautan Allah yana zaburar da ran mutum akan aikin alheri me daurewa, Allah madaukaki yace: " kuyi taimakekeniya akan aikin alheri da tsoron Allah kada kuyi taimakekeniya akan sabon Allah da zalumci, kuji tsoron Allah lalai me tsananin ukuba ne (2)" suratul ma'ida.

Daga cikin fa'idojin bauatn Allah akwai:

 1. Gyara rayuwan mutum: tana kayyade hakkoki da wajibai da ayyuka tsakanain mutane ta yadda idan koma yana kawo cewa Allah fa yana kallon dukkanin ayyukan sa wanda yayi a bayyane dana sirrizai kasance cikin tsoron kada Allah yaganshi a inda ya hanashi zuwa ko kuma ya rasa shi inda ya umurce shi da zuwa, Allah madaukaki yana cewa: " yasan dukkanin abunda idanuwa suka gani a boye da abunda zukata suke boyewa (19)" suratul gafir.

Sai dabi'un mutum su gyaru a karan kansa, Allah madaukaki yana cewa: " ka riki yafiya ka kuma dinga yin umurni da kyakyawa sannan kuma ka kawar dakai daga jahilai (199)" suratul a'araf.

Haka kuma sai halayen mutum ya gyaru tare da sauran mutane ta hanyar mu'amalar sa da dukkanin abunda suke kewaye dashi na halittu kuma zuciyarsa ya tsarkaka daga zalumci dason duniya, sai ya zama ba'abocin zuciya me kyawu saboda aiwatar da abunda umurnin Allah da yakeyi wanda yake zaburar dashi aikin alheri da kuma nisantar munanan aiki, Allah madaukaki yace: " ubangijinka ya hukunta cewa kada ku bautawa kowa sai shi kadai sannan kuma iyaye a kyautata masu, idan daya daga cikin su zai girma tare dakai ko kuma dukansu su biyu to kada kace wani daga cikin tur kuma kada ka rika tsawata masu karika fada masu magana me dadi (23) ka shinfida masu fukafukan ka na rahama kuma ka rika cewa ya ubangijina ka rama rahama kamar yadda suka rene ni ina yara (24) ubangijin ku yasan abunda ke cikin zuciyar ku, idan kun kasance salihai to lallai ya kasance me gafara ga masu yawan tuba da komawa gareshi (25) ku bay an uwanku hakkokin su da miskinai da matafiya kuma kada ku rikayin almubazaranci (26) lallai masu almubazaranci sun kasance yan uwan shedan shi kuma shedan ya kasance kafuri ga ubangijin shi (27) idan kuna neman wani uba daga gare ka na falalar ubangijinka ka fada masu Magana me dadi (28) kada ka rike hannuwan ka baka kyauta kuma kada ka bude dayawa sai ka kasance me nadama wanda ya daina ciyarwa (29) lallai ubangijin ka yana bada arziki ga wanda yaso kuma shi ke kaddarwa, lallai ya kasance masani game da bayin sa kuma me ganin su (30) kada ku rika kashe yaranku domin tsoron talauci, mu muke azurta su daku baki daya, lallai kashesu ya kasance laifi me girma (31) kada kuma ku kusanci zina domin ta kasance alfasha kuma mummunan hanya (32) kada kuma ku kashe ran da Allah ya haramta sai da cancanta, duk wanda aka kashe shi bisa zalumci to hakaki mun sanya iko a hannun waliyyin sa kuma kada yayi barna wurin kisa domin lallai ya kasance abun taimako (33) kada kuma ku kusanci kudin marayu sai da abunda yafi kyau har sai sun girma sun mallaki hankulan su, kuma ku cika alkawari domin lallai alkawari ya kasance abun tambaya akai (34) ku cika ma'auni idan zakuyi awo kuma kuyi awo da ma'auni na adalci, wannan shi yafi zama alheri a karshe me kyau (35) kada ku fadi abunda baku da ilimi akai lallai shi da gani da tunani dukkanin su za'ayi tambaya akan su (36) ka kayi tafiya a doron kasa da takama domin kai dai bazaka iya tsaga kasa ba kuma bazaka kamo dutse a tsayi ba (37) dukkanin wannan abubuwan da muka hana sun kasance laifuka kuma abun kyama (38)" suratul isra'i.

Allah madaukaki kuma yana cewa:" kace ma bayina su rika fadin abunda yafi alheri domin lallai shedan yana zugi a tsakanin su, kuma lallai shedan ya kasance me bayanannen kiyayya ne ga mutum (53)" suratul isra'i.

 1. Gyara al'umma: bautan Allah tana gadar da gyaruwan al'umma saboda abunda ke cikin ta na hukunce hukunce da tsare tsare wanda suke kare rayuka da kudi da mutunci da hankali da zuriya.
 • Allah madaukaki ya fada cikin bayana akan kare rai da jiki: " kuma mun wajabta masa cewa duk wanda ya kashe akashe, ido da ido hanci da hanci kunne da kunne hakori da hakori sannan kuma wanda yajima wani ciwo sai arama daidai da ciwon dayaji ma wani, wanda kuma ya yafe to hakan ya zama kaffara a gareshi, duk wanda baya hukunci da abunda Allah ya saukar to ya wannan sune azzalumai (45)".
 • Allah yace game da kiyaye dukiya: " barawo da barauniya ku yanke masu hannuwa sakamakon laifin da suka aikata na laifi daga Allah, Allah mabuwayi ne kuma me hikima (38)" suratul ma'ida.
 • Allah madaukaki yace game da kare mutumci daga zina: " mazinaci da mazinaciya kuyima ko wanni daga cikin su bulala dari kuma kada ku tausaya masu cikin addinin Allah idan kun kasance kuna imani da Allah da rana ta karshe kuma asamu wasu daga cikin mutane cikin muminai su shaida wannan azaba nasu da akayi masu (2)" suratun nur.
 • Allah madaukaki yace game da kare mutumci daga kazafi: " wanda suke jefan muminai kamammu da zakafi sa'annan suka kasa zuwa da shedu guda hudu to kuyi masu bulala tamanin kuma kada ku kara amsar shedar su har abada, kuma wannan sune fasikai (4)" suratul muminun.
 •  Allah madaukaki yace game da kare hankali: " suna tambayan ka game giya da caca, kace masu akwai zunubi masu girma akan su da kuma dan amfani ga mutane amma zunuban su yafi amfanin su yawa, kuma suna tambayan game da abunda zasu ciyar, kace masu abunda ya ragu daga bukatuwar iyalansu, kamar hakane Allah yake bayyana maku ayoyin sa koda zakuyi tunani (219)" suratul bakara.
 • Allah madaukaki yace game da kare zuriya: " idan suka juya sai su shiga barna a bayan kasa kuma su lalata gonaki da zuriya, lallai Allah bayason masu barna (205)" suratul bakara.
 1. Tsara alaka tsakanin kasashe da kuma makwabtaka me kyau: mutane dukkanin su bayin Allah ne wanda suke bauta masa da wanda basa bauta masa dukkanin su anyi umurni da a kyautata masu a anan duniya amma a lahira hisabin su yana wurin ubangijin su, Allah madaukaki yace: " yaku mutane lallai mun halicce ku ne daga adam da hauwa'u sai muka sanya kuka zama al'umma da kabilu domin ku samu sanayya, lallai wanda yafi wani daraja acikinku a wurin Allah shine wanda yafi tsoron sa, lallai Allah masani ne kuma me bada labara (13)" suratul hujurat.

Allah madaukaki be aiko manzonsa ba Muhammad sai domin rahama ga mutane baki daya wanda yayi masa biyayya da wanda beyi mas aba, wanda yayi masa biyayya yana da ladan abunda Allah yayi masa alkawari da sakamako wanda kuma beyi masa biyayya ba baza'a zalumce sa a wurin da da addinin sa, Allah madaukaki yace: " bamu aikeka ba face rahama ga talikai (107)" suratul anbiya'i.

Wannan itace da'awar sa kuma wannan shine addinin sa wanda Allah ya aiko shi dashi domin kira zuwa ga bautan Allah cikin sauki da Magana me kyau, Allah madaukaki yace: " kayi kira zuwa ga hanyar ubangijin ka da hikima da kuma wa'azi masu kyau, ka kuma yi jayayya dasu da abunda yafi kyau, lallai ubangijin ka shine mafi sani ga wanda ya bace daga hanyarsa kuma shine mafi sanin wanda suka shiryu (125)" suratun nahli.

Bautan ka ga Allah da kuma biyayyar ka ga shari'ar sa suna lazumta maka ka kasance me adalci tare da komai na dukkanin abunda suke kewaye dakai na haittun Allah hatta dabbobi da kuma kyautata masu, hakika wata mata ta shiga wuta saboda wata mage wacce ta kulleta ta hanata abinci kuma ta hanata fita taci kwari a waje, kuma karuwa cikin bani isra'ila ta shiga aljanna saboda ta shayar da wani kare wanda ta ganshi yana cin kasa saboda kishi, kuma an gafarta ma wani mutum saboda ya kawar da kaya daga hanyar mutane daka ta cucar dasu, kamar yadda manzon Allah s.a.w ya bada labara, da kuma yin adalci ga wanda yake adawa dakai ba'ace ka zalumce shi ba an umurce ka ne da kayi mu'amala dashi me kyau da halaye nagari, Allah madaukaki yace: " kace ubangijina yayi umurni da adalci kuma ku tsayar da guskarku cikin ko wnai masallaci kuma ku kirashi kuna masu tsarkakeshi da bauta kamar yadda haife ku haka zaku koma (29)" suratul a'araf.

Bari mu kawo wasu daga cikin ayoyi domin nazari akan su wanda suke tsara kyakyawan makwabtaka:

 • Kyautata musu da biyayya zuwa gare su, Allah madaukaki yace: " Allah baya hanaku game da mutanen da basu yake ku ba cikin addini sannan kuma basu fitar daku daga gidajen ku da ku masu biyayya kuma ku masu adalci, lallai Allah yanason masu adalci (8)" suratul mumtahana.
 • Basu tsaro da amana, Allah madaukaki yace: " idan daya daga cikin mushrikai ya nemi makwabtaka dakai to ka bashi domin yaji maganar Allah kuma ka bashi cikakken tsaro, hakan ya faru ne saboda su mutane wanda basu sani ba (6)" suratul tauba.
 • Rashin yaudara da ha'intar su, Allah madaukaki yace: " idan kana tsoron ha'inci daga mutanen da kukayi alkawari dasu to ka nuna masu ka warware wannan alkawri dasu, lallain Allah bayason mutane masu ha'inci (58)" suratul anfal.
 • Mayar masu da amanar da suka baka, Allah madaukaki yana cewa: " lallai Allah yana umurtan ku da ku mayar da a mana zuwa ga masu shi kuma idan zaukuyi hukunci a tsakanin mutane kuyi hukunci da adalci, lallai Allah abunda yake umurtan ku dashi cikakke ne kuma me girma na yake maku wa'azi dashi, lallai Allah ya kasance meji kuma me gani (58)" suratun nisa'i.
 • Cika masu alkawuran su da kuma rashin karya su, Allah madaukaki yana cewa: " sai dai wanda kukayi alkawarin zaman lafiya dasu daga cikin mushrikai sa'annan kuma basu karya maku wannan alkawari ba kuma basu taimaki wani akanku to ku cika masu alkawarin su zuw alokacin da kuka yanke, lallai Allah yana son masu takawa (4)" suratul tauba.
 • Yi masu adalci da kuma rashin zalumtar su, Allah madaukaki yana cewa: " yaku wanda sukayi imani ku zama wakilan Allah masu tsayawa akan adalci, kada adawar dake tsakanin ku da mutane yasa kukiyin adalci, kuyi adalci domin shi yafi kusa da takawa, kuji tsoron Allah lallai Allah me bada labari ne akan abunda kuke aikatawa (8)" suratul ma'ida.
 • Rashin yi masu ta'addanci, Allah madukaki yana cewa: " kuyi jihadi domin daukaka addinin Allah amma kada kuyi ta'addnci, lallai Allah bayason masu ta'addanci (190)" suratul bakara.
 • Tabbatar da aminci da zaman lafiya tare dasu, Allah madukaki yana cewa: " idan suka nemi ku zauna teburin sulhu na zaman lafiya to kazauna dasu kuma ka dogara ga Allah, lallai shi ya kasance meji kuma me gani (61)"
 1. Toshe kafofin sha'awa irin ta dabbobi na mutum, Allah madukaki yawe: " kace lallai ubangijina ya haramta alfasha na bayyane dana boye da sabo da zalumci batare da hakki ba da kuma yima Allah shirka da abunda be saukar da dalili akai ba da kuma fadin abunda baku da ilima akansa game da Allah (33)" suratul a'araf.
 2. Tana gadar da aiki da kwazo da kuma kyautatama Allah zato kuma kana kashe kasala da zaman banza, sai mutum ya samu natsuwa da kwanciyar hankali da yarda da hukuncin Allah da kaddaran sa saboda saninsa cewa dukkanin abunda Allah ya kaddara alheri ne koda kuwa a zahirin sa ba hakan bane, sai yaci gaba da rayuwa kuma bazai taba gani ba cikin wannan rayuwa sai bangaren alheri kadai, Allah madukaki yana cewa: " lallai dukkanin tsanani yana tare da sauki (5) lallai dukkanin tsanani yana tare da sauki (6)" suratul sharhi.
 3. Tana tsarkake mutum daga tatsuniyoyi da dimuwa da tsiddabaru wanda suke alakanta mutum da bautan abubuwan da baza amfanar wa kuma basa cucarta, wannan shine hakikanin abunda Ibrahim baban Annabawa ya bayyana ma mutanen sa da usulubi wanda zai sanya su tunani na hakikanin abunda suke bautamawa, sai Allah madaukaki ya fada yana bada labari akan sa: " ka karanta masu labarin Ibrahim (69) a lokacin da yace ma mahaifin sa da mutanen sa me kuke bautamawa (70) sai suka ce muna bautama gumaka ne kuma mun tsayu akan bautan su da rokansu (71) sai yace masu shin sunajin ku idan kuna rokon su (72) ko kuma suna amfabar daku ko cucar daku da wani abu (73) sai suka ce a'a basayi mun dai samu iyayen mu ne kawai suma haka suke aikatawa (74) sai yace masu shin bakwa ganin abunda kuke bauta mawa ne (75) ku da iyayen naku kakanni (76) lallai su makiyana ne sai dai ubangijin talikai (77) shine wanda ya halicce ne kuma shine yake shiryar dani (78) shine kuma wanda yake ciyar dani kuma yake shayar dani (79) kuma idan nayi rashin lafiya shine yake warkar dani (80) shine kuma wanda zai kashe ni kuma ya rayani (81) shine kuma wanda nake fatan zai gafarta mun zunubai na ranan sakamako (82)" suratul shu'ara'i.
 4. Yana tsarkake mutum daga bautan kundun tsarin mulki da dokokin na mutum wanda aka gina su domin maslahar wani mutum ko kasa ko wani yanki cikin duniya, wanda mutum zai koma bauta a cikin ta, Allah madukaki yace: " kace masu yanzu wanin Allah zan rika majibincin al'amura na bayan Allah shine wanda ya kirkiri sammai da kasa kuma shine yake ciyarwa ba'a ciyar dashi, kace ni dai an umurce ni dana zama farkon wanda zai musulunta kuma kada kazama cikin masu shirka (14)" suratul an'am.
 5. Kosar da zuciyar mutum da yakini da kuma kyautata dogaro ga Allah hakan sai yayi galaba akan sa a lokacin tsanani da annoba saboda abunda ya samu na bautan Allah a cikin zuciyar sa yin amanna dashi bazayyi asarar karshe ba kuma bazai yanke daga kwadayi ba, annabin Allah musa amincin Allah ya tabbata agareshi bayan ya gudu da mutanen sa daga rundunar fir'auna da mabiyan sa wanda suka kashe yaransu maza suka kyale mata ya kuma yi masu kawanya da rundunar sa zuciyar sa yana cike da fushi dasu da kuma mugunta sai ga kofi a gabansu shi da mutanen sa babu wata dabara ko hanyar da zasubi ga kuma fir'auna da rundunar sa a bayan su babu wani me taimako da agaji, musa da mutanen sa sun sakankance cewa sun halaka sai sukace " shikenan zasu riske mu (61)" sai musa yace masu yana me kyakwan dogaro da yakinin ga Allah, ina lallai da sannu Allah zai kunyatar da karshen azzalumai kuma zai tarwatsa taron su, kuma Allah bazai taba tabar da duk wanda ya dogara ba agareshi ya kuma kyautata masa zato, Allah madaukaki yace: " sai suka biyo su da sassafe lokacin fitowar rana (60) lokacin da kowa yaga kowa sai mutanen musa sukace shikenan sun kamo mu (61) sai musa yace ina lallai ubangijina yana tare dani kuma zai shiryar dani hanya (62) sai mukayi wahayi zuwa ga musa cewa ya bugi wannan kogi da sandar sa, sai ruwan wannan kogi ya rabe sai gashi ko wani bangare kamar dutse me girma (63) sai muka kusanto da mutanen fir'auna kusa da sauran rundunar sa (64) muka tsiratar da musa da mutanen da suke tare dashi baki dayan su (65) sa'annan muka nutsar da sauran (66) lallai cikin haka akwai aya amma dayawa daga cikin su basa imani (67)" suratul shu'ara'i.
 6. Sirri kwanciyar hankalin zuciya da natsuwa shine hanyar imani da kaddarar Allah da hukuncin sa har bawa yasan cewa duk abunda ya sameshi bazai kubce mas aba kuma duk abunda ya kubce masa be same shi ba rabon sa bane kamar yadda manzon Allah s.a.w ya fada cikin fadin sa cewa: " ka sani cewa da ace mutane zasu hadu dukkanin su akan su amfanar dakai da wani abu bazasu iya amfanar dakai ba dakomai sai abunda Allah ya rubuta maka, haka kuma da zasu hadu akan su cucar dakai da wani abu shima bazasu iya cucar dakai ba dakomai da abunda Allah ya rubuta zai sameka" Tirmizi ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi cikin sahihul jami'u.
 7. Aloakcin da mutum yake jin haka kuma yake da hakinin cewa dukkanin al'amura na Allah ne kuma babu wani abunda zai fara a wannan duniya sai abunda Allah ya kaddara kuma ya hukunta shi sai zuciyar sa ta natsu yaci gaba da harkokin sa kamar yadda aka umurce shi kuma ya yarda da abunda aka bashi, Allah madukaki yana cewa: " babu wata musiba da zata samu wani sai da izinin Allah, duk wanda yayi imani da Allah zai shiryar da zuciyar sa, Allah ya kasance masani ga komai (11)" suratul tagabun.

Sai ya mika al'amarin sag a Allah bazai furgita ba ko tsoro ga abunda zai faru wanda zuciya ke kinsa saboda Allah zai iya yaye masa damuwan sa, abubuwa nawa ne na bala'i da jaraba zasu samu mutum wanda a zahirin sa ana ganin alheri ne da ni'ima lallai Allah shine ya sani ku baku sani ba, dabari ya ambata cikin tafsirin sa daga ibn Abbas Allah yakara masu yarda yace: na kasance a bayan manzon Allah s.a.w akan rakumin sa sai yace mun: ya kai dan Abbas ka harda da abunda Allah ya kaddara maka koda kuwa sabanin abunda kake so ne domin kuwa hakan ya tabbata a littafin Allah. Sai nace ya manzon Allah a ina hakan yake cikin kur'anin dana karanta! Sai yace: cikin fadin sa: " sau dayawa kuna kin abu amma shine alheri agareku kuma sau dayawa kuna son abu amma sharri ne a gareku, Allh shine masani ku baku sani ba (216)" suratul bakara. Dabarani ya Ambato shi cikin tafsirin sa da kuma suyudi cikin darul mansur.

 1. Jure wahala da hakuri akansa: bautan Allah tana gadar da dandanon cikin zuciya babu wanda yake jinta sai wanda ya gasgata imanin sa cikin bautan Allah, wannan halawar kuwa zata rika mantar dashi dukkanin wasu radadi na wannan duniya, bokayen da fir'auna ya kawo su domin su kara da musa da tsafin su,alokacin da sukaga gaskiyar ayar sa sai imani ya shiga zuciyar su daganan suka tabbatar da bauta ga Allah sai fir'auna yayi umurni da a azabtar dasu kafin a kashe su, amma hakan be girgiza imanin su ba sukayi hakuri akan azabtarwan da akayi masu kamar yadda Allah madaukaki ya bada labara cikin fadin sa cewa: " sai wannan bokaye suka fadi suna masu sujjada sukace munyi imani da ubangijin musa da haruna (70) sai fir'auna yace zakuyi imani dashi tun kafin na maku umurni, lallai shine ogan ku daya koya maku wannan sihiri saboda haka zan sassare maku kafafuwa da hannaye ta sabani kuma zan tsire ku ajikin bishiyar dabino kuma zaku sani cewa wanene cikin mu zai fi shan tsananin azaba da dorewa acikinta (71) sai sukace bazamu zabe ka ba mu fifitaka akan akan abunda yazo mana na hujjoji da wanda ya kirkiri halittan mu, ka aikata duk abunda zaka aikata, kasani kawai anan duniya ne zaka iya aikata abunda zaka aikata (72) lallai mu munyi imani da ubangijin mun domin ya gafarta mana zunuban mu da abunda ka tilasta mana fadawa acikin sa na sihiri, Allah shine mafi alaheri da dawwama (73) lallai duk wanda ya zoma ubangijin sa a matsayin mujirimi lallai yanada wutan jahannama bazai taba mutuwa ba a cikinta kuma bazai rayu na dadi ba acikinta (74)" suratu daha.
 2. Tana haifar da tsoron Allah ga mutum da jin cewa lallai Allah yana tare dashi a koda yaushe wanda da hakan ne zai zama me taka tsantsan cikin ayyukan sa da maganganun sa saboda tuna fadin Allah madaukaki cewa: " yasan abunda ido ke aikatawa da abunda zuciya ta boye (19)" suratu gafir.

Sai ka sameshi me matukar kwadayi na ganin cewa Allah me rasashi ba a inda yayi umurni kuma be ganshi ba a inda ya hana saboda yanajin cewa Allah yan ganinsa kuma yana tare dashi cikin dukkanin ayyukan sa, sai kaga yana kokarin aiwatar da abunda ya bashi amana akai da amanan mutane, sabanin sa ido na waje wanda mutum ke kokarin guje masa a lokacin da yaga babu wannan me lura dashi din ko kuma yayi bacci ko bashi da lafiya, kamar misalign zakka acikin musulunci musulmi yana kokarin ganin ya fitar da ita da ganin y aba wanda suka cancanta ya basu tare da dadin rai da annashwa, sabanin haraji wanda aka wajabtama mutane zakaga yana neman hanyoyin guje mata ko dai yayi karya ko ya bada cin hanyi ko kuma yayi takardan bugi cewa ya biya da makamantan wannan halaye dai marasa kyau.

 1. Magance masifun bawa da kuma samun sukunin zuciyarsa: da bautan Allah ne mutum ke samun maganin dukkanin masifun da suka same shi da matsalolin dake damun sa ta hanyar kebanta da Allah mahaliccin sa da kuma riko da umurnin sa cikin wannan yanayi, Allah madaukaki yana cewa: " yaku wanda sukayi imani taimako akan hakuri da salla, lallai Allah yana tare da masu hakuri (153)" suratul bakara.

Allah madaukaki yace: " zamu jarabeku da wani na tsoro da yunwa da karayan arziki da rayuka da kayan itace kayima me hakuri bushara (155) shine wanda idan masifa ta same shi sai yace innalillahi wa inna ilaihi raji'un (156) wannan suna da adduwa daga ubangijin su da rahama kuma wannan sune shiryayyu (157)" suratul bakara.

 1. Daukaka da buwaya ga mutum: duk wanda ya kasance me bauta ga Allah shi kadai Allah zai kasance tare dashi wanda Allah ya kasance tare dashi kuma bazai taba kaskanta ba ko kuma wani yayi galaba akansa ko tankwara shi ba, Allah madaukaki yace: " lallai Allah yana tare da wanda suke jin tsoron sa da kuma masu kyautatawa (128)" suratun nahli.

                        Taya hakan bazai kasance ba kasancewar mamallakin duniya da wanda ya halicceta da jujjuyata ya kewaye shi da taimakon sa, domin gasgata fadin sa cewa: " duk wanda ya jibinci Allah da manzon sa da muminai to lallai kungiyar Allah sune masu galaba (56)" suratul ma'ida.

 1. Kariya daga shedanu da wasiwasin su: duk wanda ya tabbatar da bauta ga Allah za'a kiyaye shi da damar sa da hagunsa da samar sa da kasansa, Allah madaukaki yace: " lallai bayina bada da wani iko dasu sai wanda ya bika cikin batattu (42)" suratul hijri.
 2. Natsuwa da kwanciyar zuciya: bautan Allah tana yantar da mutum daga abubuwan tsoro wannan tsoron na abunda ya wuce ne ko kuma wanda zai zo ko na yanzu saboda mutum yanajin cewa fa lallai al'amura dukkanin su a hannun wanda ya wajabtama kansa rahama suke to taya zuciya bazata natsuba da samun sukuni bayan yanajin fadin Allah cewa: " duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa, lallai Allah yana tafiyar da hukuncin sa cikin bayinsa yadda yakeso, hakika Allah yasanya kaddara ga faruwan komai (3)" suratul dalak.

                        Dukkanin dangin tsoro na mutum suna tafiya dayinn rauni cikin farfajiyar bauta ga Allah saboda kasancewar tana ciyar da zuciya da rai da yarda, idan tsoro ya kasance:

 • Tsoron abunda ba'a sani ba: tare da bautan Allah babu wani tsoro na abunda ba'a sani ba ko kuma jin tsoron rayuwan mutan ta gaba yadda zata kasance, taya wanda yakejin fadin Allah madaukaki zaiji tsoro: " Allah ya tanadar wa muminai maza da mata aljanna wanda koramu suke gudana a karkashinta suna masu dawwama acikinta da gine gine masu kyau da aljanna na zinari da azurfa kuma yarda daga Allah yafi wannan dukansu girma, wannan shine rabo me girma (72)" suratul tauba.
 • Tsoron rashin lafiya: tare da bautan Allah taya wanda yakejin fadin Allah madaukaki zaiji tsoro: " babu wata musiba wacce zata samu mutum ko kuma ta faru a doron kasa face tana cikin littafi tun kafin a halicci halittu, lallai wannan abu ne me sauki a wurin Allah (22)" suratul hadid.
 • Tsoron mutuwa: tare da bautan Allah taya wanda yakejin fadin Allah madaukaki zaiji tsoro: " wata rai bata kasance zata mutu ba face da izinin Allah, har sai ya cika lokacin da Allah ya kaddara masa, duk wanda yake son sakamakon duniya zamu bashi daga cikin ta wanda kuma yake son sakamakon lahira zamu bashi daga cikinta, kuma da sannu zamu sakama masu godiya (145)" suratu al'imran.
 • Tsoron rashin samun zuriya: tare da bautan Allah taya wanda yakejin fadin Allah madaukaki zaiji tsoro: " mulkin sammai da kasa duk na Allah ne, yana halittan abunda yaso yana ba wanda yaso yaya mata kuma yana ba wanda yaso yaya maza (49) ko kuma ya hada mashi maza da mata sannan kuma ya mayar da wanda yakeso mara haihuwa, lallai shi masani ne kuma me iko (50)" suratul shura.
 • Tsoron ciwon zuciya: tare da bautan Allah taya wanda yakejin fadin Allah madaukaki zaiji tsoro: " wanda sukayi imani kuma zukatansu ta natsu da ambaton Allah, ku saurara da ambaton Allah ne zuciya take samun natsuwa (28)" suratul ra'ad.
 • Tsoron azzaluman mutane: tare da bautan Allah taya wanda yakejin fadin Allah madaukaki zaiji tsoro: " wanda wani mutum yace masu lallai mutane fa sun taru suna jiran ku saboda haka kuji tsoron su sai ya kara masu imani sukace Allah ya isan mana kuma madalla da wakilcin Allah (173) sai suka juyo da ni'ima daga Allah da falala ba tare da wani mummunan abu ya shafesu ba kuma sukabi yardan Allah, Allah ya kasance me falala me girma (174) lallai wancan shedan ne yake tsoratar da mutanen sa kada kuji tsoron sa ni zakuji tsoro idan kun kasance muminai (175)" suratu al'imrana.
 • Tsoron talauci da yunwa: tare da bautan Allah taya wanda yakejin fadin Allah madaukaki zaiji tsoro: " kuma sau nawa ne wata dabba wacce bata iya samun abincin ta Allah zai ciyar da ita daku, shi ya kasance meji kuma me gani (60)" suratul ankabut.
 • Tsoro akan arziki: tare da bautan Allah taya wanda yakejin fadin Allah madaukaki zaiji tsoro: " babu wata dabba cikin kasa face arzikin sa yana wurin Allah kuma yasan inda take zuwa da kuma makomarta, komai yana cikin littafi bayyananne (6)" suratu hud.
 • Tsoron rashin samun gafara daga zunubai: tare da bautan Allah taya wanda yakejin fadin Allah madaukaki zaiji tsoro: " kace yaku bayina wanda suka aikata zunubai akan kawunan su kada su cire rai daga rahamar Allah, lallai Allah yana gafarta zunubai baki daya, lallai shi me gafara ne kuma me rahama (53)" suratul zumar.
 • Tsoron mutum: tare da bautan Allah taya wanda yakejin fadin Allah madaukaki zaiji tsoro: " idan Allah ya shafeka da wata cuta babu wanda zai yaye maka ita sais hi, haka kuma idan yaso da wani alheri babu wanda ya isa ya mayar da falalar Allah, yana ba wanda yaso ita cikin bayin sa kuma shi me gafara ne kuma me rahama (107)" suratu yunus.

 

 

 

KOMAWA ZUWA GA ASALI:

            Yana cikin abunda da kayi ittifaki akai kuma tabbatacce shine komai fa yanada asali, sannan kuma duk wani abu da aka kirkiro yana da farko saboda haka mutum asalin su guda ne kuma baban su daya ne Adam amincin Allah ya tabbata a gareshi shine baban mutane baki daya daga tsatson shi ne aka fara halittan mutu har sukayi yawa suka yadu cikin kasa, Allah madaukaki yace yana me bayyana wannan hakikanin: " yaku mutane kuji tsoron ubangijin ku wanda ya halicce ku daga mutum daya ya kuma halitta masa mata daga jikin say a kuma yada daga tsakanin su maza da mata, kuji tsoron Allah wanda kuke rokon sa da kuma sada zumunta domin sa, lallai Allah ya kasance me sa ido akanku (1)" suratun nisa'i.

            Hankali yana cewa tunda dai asalin daya ne to ya kamata a dabi'ance ya zama cewa akida daya wacce itace tauhidi da bautan Allah shi kadai ba tare da masa tarayya ba da wani kasancewar haka itace akida da addinin baban mu Adam amincin Allah ya tabbata agareshi ya kasance a kan tauhidi tatacce da bautan Allah, Allah madaukaki yace: " mutane basu kasance ba face al'umma daya sai suka rabu, badan Kalmar ubangijinka ba data gabata da an yanke masu hukunci a tasakanin su cikin abunda suke sabani acikinsa (19)" suratu yunus.

            Wannan sabanin kuwa ya samo asali ne daga banabancin tunani da rayuwa da kuma yare kamar yadda Allah madaukaki yace: " daga cikin ayoyin sa shine halittan sammai da kasa da kuma banbancin yarukan ku da fatar ku, lallai cikin haka akwai ayoyi ga masana (22)" suratul rum.

            Kuma daga cikin dabi'a ne har wayau wannan sabanin ya haifar da canzawar akida da addini kamar yadda muke gani na banabantan addinai da akidu da bauta kala kala a fadin duniya, ya kasance wajibi ga ko wani mutum da ya koma zuwa ga asali cikin bauta da addininsu na gaskiya wanda suka kansa gabanin shedanu su canza su wanda shine tauhidi tsantsa ga Allah da kuma mika wuya gareshi da jayuwa gareshi da masa biyayya da tsarkaka daga shirka, kuma suyi hukunci da dukkanin abunda ya umurce su dashi cikin rayuwan su baki day aba tare da kebance wani abu ba idan sun kasance sunason tsrira da daukaka da karamci da rayuwa me kyau idan kuma ba haka ba rayuwa zatayi daci a nan duniya da lahira, Allah yayi gaskiya: " alif lam mim, wannan littafin mun saukar maka dashi ne domin ka fitar da mutane daga duhu zuwa haske da izinin ubangijinsu zuwa ga hanyar mabuwayi me godiya (1)" suratu Ibrahim.

 

KIRA DA WA'AZI:

            Daga nan ga kira zuwa ga wand aba musulmai ba masu fahimtar cikin su da hankali kan karatun fassarar ma'anar alkur'ani me girma kundin tsarin mulkin musulunci da sannu zasu samu mafita ga dukkanin matsalolin su da matsalolin duniya na siyasa da tattalin arziki dana zamanta kewa da dabi'u, sai dai yana bukata daga gare su da suyi amshe shi su kuma yi nazari akan sa suna masu nisanta daga son zuciyar su da kabilanci na addini saboda kasancewar sa kundun tsarin mulki kuma ansanya shine domin mutane baki dayan su har zuwa tashin alkiyama bawai na larabawa bane kawai kamar yadda wasu suke ikirarin haka, hukunce hukunce sa da dokokin sa sun game komai na bangaren rayuwa kuma yayi daidai da ko wani irin zamani da wuri, kuma da sannu zasu samu a cikin sa dukkani amsoshi gamsassu game da tambayoyin da yake bijiro wa cikin zukatan mutane da yawa wand aba musulmai ba akan rayuwa da mutuwa da abunda ke bayan sa, ( a shirye muke mu kara maka taswiri na alkur'ani idan kana bukata), dukda kasancewar karshen sakonni cikin littattafai ya kasance littafi ne me girmama sauran addinai na yahudawa da kiristoci kuma yana hani game da barin zagin akidun wasu addinan mutane na daban, Allah madaukaki yace: " kada ku zagi abunda suke bautama wanin Allah ai su zagi Allah saboda zalumci da rashin ilimi, da Kaman haka ne muka kawatama ko wace al'umma aikin ta sa'annan zuwa ga ubangijin su zasu koma yaba su labarin abunda suka kasance suna aikatawa (108)" suratul an'am.

            A yayin nazari cikin wannan alkur'ani zasu same shi me bi a sannu sannu cikin maganganun sa me saukin shiga zuciya da gamsar da hankula cikin shari'ar sa da hukunce hukuncen sa, ALllha yayi gaskiya cikin fadin sa cewa: " shin bazasuyi nazari ba cikin alkr'ani da ace daga wurin Allah yake da sun samu sabani da yawa acikin sa (82)".

            Maganar ta sallamawa ce da aiki da ita, kasan wanene Allan ka na gaskiya wanda zaka natsu da bautan masa kuma ka rika jin dadin munajati dashi domin samun natsuwa da kwanciyar hankali cikin nan duniya da kuma dammawa cikin aljanna me dawwawa a lahira, ka nisantar da kanka daga jahilci da makauniyar koyi wacce bataji kuma take rafkanar da zuciya wacce bazata taba barinka b aka amshi gaskiya kuma zuciyar ka taji dadi dashi domin ka isa zuwa gaskiya da kuma sanin Allah madaukaki, lallai dama ce wanda ya wajaba ka ribace ta matukar kofar tuba yana bude da komawa zuwa ga Allah tun gabanin mutuwa ta zo maka, a lokacin nadama bata amfani, a wurin Allah kuma baka tsoron zalumci ko kuma kunge kayi murna da abunda zai farnta maka yadda zai gafarta maka dukkanin zunuban ka baki daya wand aka aikata da kura kurai saboda haka kada wannan dama ta wuce maka, Allah madaukaki yana cewa: " kace ma wanda suka kafurta idan suka bar kafurcin nasu za'a gafarta masu abunda suka aikata a baya amma idan suka ci gaba to hakika sunnar mutanen farko ya gabata (38)" suratul anfal.

            Lallai ina cikin yarda cikakke cewa dayawa basu yarda da abunda suke ciki ban a bautan wanin Allah daya mabuwayi wanda ya halicce su kuma ya samar dasu daga rashi musamman ma masu bautan halittu irinsu kamar dabbobi da dabi'a, lallai zakayi mamaki matuka ga wanda suke neman abun bauta mutum me hankali da wayewa zai rika bautan wuta da shedan da makamantan haka, hakika zuciyar su ta kurmance kafin ganin su game da bautan Allah na gaskiya, Allah yayi gaskiya: " lallai ba idanuwa bane suke makance wa zuciya da take cikin kiraza ne take makancewa (46)" suratul hajj.

            Duk wanda yakeson gaskiya Allah zai datar dashi idan Allah yasan gaskiyar niyyar sa akan haka, Allah madaukaki yace: " duk wanda yayi imani da Allh zai shiryar da zuciyar sa, Allah masani ne ga dukkan komai (11)" suratul tagabun.

            Kada ka kasance cikin masu girman kai game da gaskiya da masu dagawa akan mutane sai gaskiya ta bace cikin zuciyar ka, da shamaki a idanun ka yadda bazaka ga komai ba sai abunda yayi daidai dason zuciyar ka kuma hakan ya zama sanadin halakar ka, Allah madaukaki yace: " da sannu dan shafe ayoyi nag a mutanen da suke girman kai cikin kasa batare da gaskiya ba, idan sunga ko wani aya basa imani dashi, idan sunga hanyar shiriya basa riketa a matsayin hanyar bi, idan kuma sunga hanyar bata da rudu sais u riketa a matsayin hanyar bi, hakan ya kasance ne saboda sun kasance suna karyata ayoyin mu kuma suna gafala daga garesu (146)" suratul a'araf.

            Ka koma zuwa ga abun bautanka na gaskiya zaka same shi me rahama a gareka sama da mahaifiyar ka wacce ta dauki cikin ka ta kuma shayar dakai da renon ka, Allah madaukaki yace: " shine wanda yake yabon ku da ambatan ku kuma mala'ikun sa suna maku addu'a domin ya fitar daku daga duhu zuwa haske, kuma ya kasance me rahama ga muminai a lahira (43)". Suratul ahazab.

            Yana farin ciki da tuban ka da komowa zuwa ga bautan sa kamar yadda manzon Allah s.a.w ya fadi cewa: " lallai Allah yana farin ciki da tuban bawansa bayan yayi zunubi sama da farin cikin mutumi matafiyi cikin sahara tare da abun hawan sa wanda ya daura mata abincin sa da ruwan shansa kawai sai ta bace masa ya cire rai da rayuwa tabbas mutuwa kawai zayyi ya zauna yana jiran lokacin sa sai barci ya kwashe shi yana bude ido sai yaga wannan abun hawar nasa ta dawo irin murnan da wannan mutumi zayya to lallai Allah yafi murna da tuban bawan sa sama dashi" sahihu muslim.

                                   

 

 

JAWABIN KARSHE:

            Yakai makaranci me daraja, lallai ina cikin masu nasiha agreka masoya agareka, lallai kwadayi na akan gabatar da wani abun amfani ga mutane shi yasani wallafa wannan littafi " mafi alherin mutane shine wanda yafi amfanar dasu" ( sahihul jami'u) kamar yadda addinin mu ya koyar damu ya dauramu kuma akai, son rahama da nake yi masu shi ya kara sanya ni wannan aiki " masu rahama Allah zai masu rahama" ( hadisi ne ingantacce, Ahmad da abu dawud da tirmizi duk sun rawaito shi) kamar yadda ubangijin mu ya umurce mu da mu rika son alheri ga mutane shine abunda yake zaburar wa zuwa ga haka kamar yadda manzon Allah s.a.w ya fadi: " kasoma mutane abunda kake soma kanka" ( hadisine ingantacce, tirmizi da ibn majjah me suka rawaito shi) dukkanin wannan fadakarwan na ubangiji sune wanda suka sanyani yin kokarin ganin ya bayyanar da gaskiya wacce kusan ta bace a gare ku ta dalilan kafafen yada labarai wanda suka lallata zuciyar mutum ko kuma su canza gaskiya wanda yake sanya ma zuciya rigar kura sai ya rika mayara da gaskiya karya, karya ya mayar da ita gaskiya, barna ya mayar da ita gaskiya, ita kuma gaskiyar ya mayar da ita barna, me rabo shine wanda ya iya banbance wa ya kuma amshi gaskiya da wurgi da karya, fadakarwan ubangiji tana umurni da tabbatar da komai da kuma rashin sallamawa akan komai sai bayan bincike da bayyanar gaskiyar haka, Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani idan wani yazo maku da labara to kuyi bincike akansa ku tabbatar da gaskiyar haka domin kada ku afkama mutane akan jahilci da rashin sani sai daga baya ku zama masu nadama akan abunda kuka aikata (6)" suratul hujurat.

            Kada me bautan wanin Allah ya rude da abunda yake ciki na lafiya da kuzari ya yawan arziki da yara, da ace duniya ta kai girman fiffikan kuda agun Allah da ba'a shayar da wanda ya kafirce masa ba ya kuma bauta ma wanin sa koda kurba daya na ruwa daga cikinta ba, Allah madaukaki yace: " kada wanda suka kafurta suyi zaton cewa tsawon rayuwan da muke basu da arzuki alheri ne a garesu, hakika ka mun basu hakan ne domin su kara zunubi, kuma sunada azaba ta wukanci (178)" suratu al'imran.

            Yawan kyauta na abubuwan duniya bashi bane dalilin Allah yana sonka da kuma yarda da ayyukan k, Allah yana bayar da duniya ga wanda yaso da wanda bayaso, amma biyayyar sa da bautan sa baya bayar wa sai ga wanda yake so, hanya a bude take a gabanka domin ka kasance cikin wanda Allah yake son su kuma ya yarda da ayyukan su, hakan zai faru ne ta hanyar gaskiyar bautan ka gareshi, Allah yana cewa: " badan kada mutane su zama kan tafarki guda ba da munsanya gidajen wanda suka kafurta rufin azurfa da matakala wanda zasu rika katawa suna hawa (33) kuma mu sanyama gidajen nasu kofofi da gidajen azurfa wanda zasu rika kishingida akai (34) da kuma zinarai, dukkanin wannan abubuwa na more rayuwan duniya ne kawai, ita kuma lahira a wurin ubangijin ka na masu tsoron sa ne masu takawa (35)" suratul zukhruf.

            Lallai mutum abunda ya tara na dukiya ko kuma ya bari na yara da dukiya bazasu amfanar dashi da komai ba idan yamutu yana bautan wanin Allah face ma bala'i ne da hasara da tambaya zasu zaman mai ranan alkiyama kamar yadda Allah madaukaki ya fadi: " dukiyoyin ku da yaranku bazasu kusantar daku ba garemu sai dai wanda yayi imani kuma yayi aiki na kwarai to wannan sunada sakamako nunkin abunda suka aikata kuma zasu kasance cikin kololuwan aljanna masu aminci" suratu saba'i ayata 37.

            Lallai mutum zai tsaya ranan sakamako shi kadai ba tare da duk abunda ya mallaka ba a duniya, babu takalmi kuma tsirara kamar yadda aka haifeshi, Allah madaukaki yace: " hakika kunzo mana daya bayan daya kamar yadda aka haife ku da farko, kuma kun baro duk abunda kuka tara a duniya, kuma bamuga masa taimakon naku ba a tare daku wanda kuke tsamman haka sune mataimakai a gareku a duniya, hakika an katse tsakanin ku kuma duk abunda kuke tsammani sun bace maku da gani (94)" suratul an'am.

            Babban abun da za'afi baka lada akai shine addinin ka da akidar ka kamar yadda kake neman lamuni na dukiya akan kasuwancin ka domin ka tabbatar da gaskiyar ta, abunda yafi ka tabbatar shine addinin ka da akidarka domin ka tabbatar da ingancin abunda kake kai na addini da akida tun kafin ranar nadama tazo maka wanda nadama bazata yi amfani ba, domin gaskiya ya bayyanar maka daga karya fa kasani baka bazaka rayu ba a wannan duniya sama da daya saboda haka ka natsu ka zama ka zabi addini na gaskiya, me wayo da dabara shine wanda tsaya a kan addini yayi aiki domin gobe bayan mutuwar sa, Allah baya nema daga gare ka face abu kadan daga gareka wanda shine bauta masa da kuma yin hukunci da shari'ar sa, shi mawadaci ne dakai kuma yayi maka alkawarin rayuwa me tsayi ta har Abadan karkashin ni'ima me durewa, kuma ya haramta maka mutuwa acikinta, wanda yake amfanuwa farko da karshe dai duk kai ne dan Adam, zunubin masu zunubi basa cucar da Allah ko kuma biyayyar masu biyayya ta amfanar dashi, kawai hakan jarabawa ne domin agane me biyya da mara biyayya, Allah madaukaki yace: " kuma hakika mun jarabe mutanen da suka gabace su, domin Allah yasan masu gaskiya cikin su ya kuma san makaryata" suratul ankabut ayata 3.

            Bautan Allah madaukaki lamuni ce dan tabbatar maka da nasara cikin duniya da lahira bawai kudi da matsayi ba kawai ita kudi da matsayi inuwa ce wacce bata dorewa bazaka iya siyan lad aba da shi ranan alkiyama ko kuma ka kankare maka zunuban ka, Allah madaukaki yace: " lallai wanda suka kafurta da ace duk abunda cikin duniya baki daya nasu ne da kwatan kwacin sa da sun badashi fansa daga azaba ranan alkiya amma baza'a amsa masu ba kuma sunada azaba me radadi" suratul ma'ida ayata 36.

            Ina rokon Allah da ya haskaka ganinka ya kuma shiryar da zuciyar ka ya kuma nuna maka gaskiya, Allah yai dadin tsira abisa annabin mu Muhammad da iyalan gidan sa da sahabban sa baki daya.

            Kenan taya za'ace wannan duniya da abunda ke cikinta na sama da kasa da rana da wata da dare da yini da taurari basa nuna akwai wanda ya samar dasu ya kuma halitta su? Kuma wannan mahaliccin me yake so daga wannan halittu kuma dan me yayi halicce su?

 

www.islamland.com

 

 

 


[1] Allah ya tsarkaka daga haka me girma mabuwayi

[2] Allah ya tsarkaka daga haka me girma mabuwayi

[3] Sahih wal targib 2187

[4] Aljawabul kafi na Ibn kayyim


About the book:

ADDINI (BAUTA) DA MAGUZANCI (MARASA ADDINI)