SHUBUHOHI GAME DA HAKKOKIN DAN ADAM A MUSULUNCI.
شبهات حول حقوق الإنسان في الإسلام بلغة الهوسا
Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha
د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة
Fassara
European Islamic Research Center (EIRC)
المركز الأوروبي للدراسات الإسلامية
& Hashim Muhammad Sani
Wanda ya bibiyi fassara
Faiz Shuaib Adam
www.islamland.com
SHUBUHOHI GAME DA HAKKOKIN DAN ADAM A MUSULUNCI.
Da sunan Allah me rahma me jin kai.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga annabin mu Muhammad da iyalansa sa da sahabbansa baki daya, bayan haka,,,
GABATARWA:
Lalla ya zama dole ga ko wace al'umma cikin al'ummomin dan adam ya zama cewa kowa acikinta yanada hakkokin wanda zai sanya su suna aikata ayyukan su da sauke nauyin da ya rataya akan su, wanda da hakan ne zasu samu ni'imar tsaro da zaman lafiya ya kuma haifar masu da soyayya a tsakanin su da hakin kai, abunda muke ganin shi a yau cikin zaman takewar mu shine tsaroka guda uku, tsarin farko shine wanda yaba dan adam cikakken girmamawa da yanci wanda yake kaddamar da hakkin mutum akan ci gaban jama'a, sannan kuma ya haramtawa al'umma yin katsalandan cikin yancin nasa da kuma bashi hakkoki na kara zube wanda bashi da tsari hakan ya haifar da rayuwar al'umma kar kashin tsari na jari hujja mara kyaun gani, sai tsari na biyu wanda ya gabatar da maslahar al'umma akan dan adam ta yadda ya kwace masa dukkanin buri nasa da hakkoki, yabar dan adam acikin ta wanda bashi da wani buri da fata kuma suka kwace masa yanci ya zama bashi da wani yanci nasa baki daya sai kawai abun da wannan al'umma ta yaga masa kar kashin arzikin kasa, irin wannan tsari wanda take gabatar da maslahar al'umma akan na dam adam ita ake kira da suna (gurguzu), sai tsari na uku wanda bai gabatar da burin dan Adam ba akan al'umma sannan kuma be kagabatar da maslahar al'umma ba akan na dan Adam, yaba kowa hakkokin sa dai dai, dam adam yanada hakkoki nasa akan al'umma haka suma al'umma suna da hakkoki nasu akan dan Adam hakkoki wanda suke tsare da dokoki sannan kuma ya sanya maslahar al'umma kan gaba akan maslahar mutum idan sunci karo, da sannu zamu koro ma me karatu cikin wannan littafi hakkokin dan adam n agame gari a karkashin inuwar musulunci wanda aka samo su daga cikin alkur'ani da hadisan manzon Allah s.a.w wanda wannan sune littattafan hujja a musulunci na asali, hakkoki da yanci wanda yakeson mutum ya zama mutum cikin siffofin sa da mu'amala da wanin sa, ina me bada tabbacin cewa yin amfani da irin wannan tsari na musulunci da kuma aiwaatar dashi a aikace zai samar da zaman lafiya da cin gaba da tsiran al'umma, saboda wannan hakkoki bawai ansamo su bane daga gwaji da tunanin al'umma ne ba ko kuma yin amfani dasu na wani lokaci ko kuma dan cimma wata muradi na siyasa, daga cikin abunda ya bani kwarin gwewa ga wannan Magana tawa dana fadi shine ganin cewa wannan ya samar da wannan hakkoki shine Allah mahaliccin dan Adam wanda yasan dukkanin abunda zai gyara masa al'amuransa da kuma inganta halinsa, hakika ya cika wannan hakkoki da ayoyi da hadisan manzon Allah s.a.w da tabbatar dasu, sai ya fara da ayar da take Magana akan karrama jinsin dan Adam akan sauran jinsin halitta, Allah madaukaki yana cewa: " hakika mun karrama dan adam sannan kuma muka wanzar dashi a bayan kasa da cikin ruwa muka kuma azurtashi daga dadadan abubuwa kuma muka fifitashi akan dayawa daga cikin halittun mu matukar fiffitawa (70)"[1].
Wannan karramawan yana bukatar wasu hakkoki wanda zai wanzar dashi da ya kuma kunshi yancinsa da bashi shugabancin duniya da kuma tsayawa wurin sauke wajibin khalifancin da Allah ya bayyana cikin fadinsa cewa: " shine wanda ya sanya ku khalifofi a bayan kasa sannan kuma ya daukaka darajan wasun ku akan wasu"[2].
Hakkoki da yancin dan adam a musulunci bawai kawai ya tsaya bane ga hakkoki na rayuwansa anan duniya bane kawai a'a hatta rayuwansa bayan yam utu, daga cikin hakkin mutum a musulunci bayan yam utu shine a masa wankan gawa da kuma sanya masa turare da likafani da tufafi fari sabo kuma ayi masa sallah da addu'a a gareshi, an karbo hadisi daga abi huraira yace, naji manzon Allah s.a.w yana cewa: "idan kunayin sallah ga mamaci to ku tsarkake niyyar ku wurin cikin masa addu'a"[3]. hadisi ne ingantacce, Abu dawud da ibn Hibban ne suka rawaito shi.
Sannan musulunci ya hana a wulakanta gawa da yankan wani abu daga jikin sa, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " karya wani kashi daga jikin gawa kamar karyawa ne a lokacin yana raye" hadisi ne ingantacce, Abu dawud ne ya rawaito hadisin.
Haka musulunci ya hana tune kabarin mutum bayan an rufeshi ko kuma zama akan kabarinshi ko tafiya akai, sabo da fadin sa s.a.w: "yafi sauki ace dayanku ya zauna akan dutse ya kona masa tufafinsa da fatansa da yaje ya zauna akan kabari"[4] sahihu muslim.
Kamar yadda yake daga cikin hakkinsa ne a kiyaye masa mutuncin sa da hana cin zarafinsa a lokacin rayuwan sa da kuma bayan mutuwar sa an rawaito daga manzon Allah s.a.w yana cewa: " ku rika ambaton kyawawan ayyukan mamatan ku sannan kuma ku kame bakin ku daga fadin laifukan sa"[5]. (Abu dawud da Tirmizi da hakim da kuma baihaki ne suka rawaito hadisin) hadisi ne da'ifi watan me rauni be inganta ba.
Sannan kuma hakkin sa ne akan yaransa da yan uwansa su rika masa addu'a ta nema masa gafara da rahama da kuma aiwatar da wasiyyar daya bari da alkawuran da ya dauka bayan ya rasu, saboda fadin manzon Allah s.a.w ga wani mutum wanda ya tambaye shi yace: ya manzon Allah shin akwai abunda yayi saura akaina na biyayya ga iyayena bayan sun rasu wand azan rika masu biyayya dashi na samu lada? Sai yace: " eh akwai shine ka rika masu addu'a da nema masu gafara da kuma aiwatar da alkawuran su da sukayi da sadar da zumincin da suke sadarwa da kuma girmama abokanan su"[6]. Abu dawud da ibn majah da ibn hibban da hakim ne suka rawaito hadisin sannan hakim yace hadisi ne me ingantaccen isnadi amma buhari da muslim basu rawaito shi ba kuma albani ya raunata hadisin.
Ta yiwu makaranci ya samu wasu hakkoki makamantan wannan hakkoki wanda wasu kongiyoyi kamar kungiyar kare hakkin dan adam da makamantar su suke kira dashi amma dai ka sani cewa addinin musulunci ya rigasu kawo wannan hakkoki da tsari sama da karni goma sha hudu, kuma wannan hokkokin da irin wannan kungiya suke kira gareshi akwai nakasu da dama acikin sa saboda mafiya yawa ba'a sanya wannan hakkoki ba domin kare hakkin mutum a matsayin san a mutum sai dan wani amfano dashi da kuma yin amfani da wannan dama tashi da ikonsa da baiwansa don cimma wata maslaha ta musamman shin wannan maslaha ga mutum ne ko kuma ga wani yanki na kasa ne, dalilin mu kuwa akan wannan Magana itace muna gani da yawa daga wasu kasashe wanda suke amfani da karfin tuwu wurin kwace ma dan adam hakkoki nashi amma kuma kaga irin wanan kungiyoyi basa iya Magana saboda duba ga wata maslaha tasu sai suyi shiru suce ai basu da ikon cusa baki cikin al'amuran da ya shafi cikin gidan wata kasa.
Lallai hakkokin dan adam a musulunci baya duba zuwa ga matsayi ko kuma mujamala, ga Umar nan dan Khaddab wanda labarin musuluntan wani babban mutum cikin kiristoci larabawa yazo masa, sia yayi farin ciki da musuluntar sa ya aika masa dayazo madina bayan isowar sa madina yayima umar sallama sannan ya bashi wurin zama yayi hajjin wannan shekarar tare da umar, a lokacin da suke dawafi a ka'aba wani mutum cikin bani fuzarata ya taka masa zanin sa da kafarsa sai wnanan babban mutum yasa hannu ya nushen masa hanci sai wasu mutanen kuma sukace idon say a duka, sai wannan mutumi yakai karar sa wurin umar cikin rakiyan mutanen san a bani fuzarata sai umar ya kira wannan mutumi ya tabbatar masa da aikata abunda aka kawo masa kara akansa dashi sai umar yace masa to ya tsaya wannan mutumi ya rama wannan duka dayayi masa sai yace haba dai ya umar taya za'ani ina babban mutum wannan talakar kaskantacce na tsaya ya rama abunda da nayi masa sai uamar yace masa ai musulunci ya mayar daku daya babu wanda yafi wani daraja sai wanda yafi tsoron Allah wannan mutumi yace bazan iya bafa indai haka addinin musuluncin yake to zanyi ridda na koma kiristanci na sai umar yace masa kanayin ridda kuwa zan sare maka kai, da wannan mutumi yaga cewa lallai umar fa dgaske yakeyi sai yace ya bashi zuw agobe zayyi shawara akan haka cikin dare sai ya gudu ya tafi kasar rum wurin sarki Hirkal ya tarbeshi ya kuma yanka masa shugabancin wani bangare cikin kasar shi ya kuma bashi kyauta me kyau da kayatarwa ya sanya shi cikin makusantansa wanda yake zama dasu ayi raha da nishadi tare"[7].
Al'amarin musulunci be tsaya ba ga kiyaye hakkokin mutum ba kadai musulunci ya ketara zuwa ga kare hakkin kowa da kuma kawar da zalumci akan wanda aka zalumta, Allah madaukaki yace: " me yasa bazakuyi yaki ba domin daukaka Kalmar Allah alhali masu rauni daga cikin ku maza da mata da yara suna cewa ya Allah ka tsiratar damu daga cikin wannann al'umma wanda suke zalumtar mutanen cikin su, ka sanya mana majibincin al'amura daga gareka kuma kasanya mana mataimaki daga gareka (75)"[8].
Wannan hakkokin kuma musulunci ya kiyaye su ga mutumin dayake musulmi da wand aba musulmi ba baki daya, manzon Allah s.a.w yana cewa: " ku saurara kuji duk wanda ya zalumci kafurin amana ko kuma yayi amsa aiki yaki biyansa hakkin sa cikakke, ko kuma ya anya shi wani aiki wanda yafi karfin sa, ko kuma ya kwace masa wani wani da karfi to lallai zamuyita dashi ranan alkiyama". Abu dawud da baihaki ne suka rawaito hadisin sannan kuma Albany ya ingantashi.
Manzon Allah s.a.w yakara cewa: " ku saurara kuji duk wanda ya zalumci kafurin amana ko kuma yayi amsa aiki yaki biyansa hakkin sa cikakke, ko kuma ya anya shi wani aiki wanda yafi karfin sa, ko kuma ya kwace masa wani wani da karfi to lallai zamuyita dashi ranan alkiyama sai manzon Allah s.a.w yayi nuni da yatsan sa zuwa ga kirjin sa yace ku saurara kuji duk wanda ya kasha kafurin amana wanda yake da kariyan Allah da manzon Allah, Allah ya haramta masa kamshin aljanna wanda ake jiyo kamshin ta daga tazaran tafiyar mil saba'in"[9].
Lallai aiwatar da hakkokin dan adam wanda musulunci yayi umurni dashi yana tafiya ne tare da gwargwadon aiwatar da hukunce hukuncen shari'ar musulunci, dga cikin mutane akwai wanda suke gudanar da al'amuransu baki daya a karkashin karantarwan musulunci sannan kuma akwai wanda suke yin amfani da shari'ar musulunci gwargwadon abunda yayi masu dadi ya dace dasu, sannnan kuma akwai wanda suke sanya rigan musulunci domin su ruguza shi ko kuma su bata mashi suna a idon duniya, saboda haka ne duk mutum me hankali da adalci da tunani me kyau cikin mutanen da ba musulmai ba idan yana son yabada hukunci game da addinin musulunci da hakkokin dan adam a cikin musulunci ya zama wajibi daya duba zuwa ga musulunci a matsayin tafarki da addini me tsari a tsuran sa batare da ya hadashi ba da ayyukan mabiyansa ko kuma wata kasa, saboda aiwatar da wannan hakkoki a cikin kasashen musuluni yana karkashin aiwatar da shari'ar musulunci ne dari bisa dari a cikin kasashen musulunci kamar yadda muka fadi abaya, tafarki idan ya kasance me kyau sai aka samu takaitawa wurin amfani dashi to lallai zai shafi wanann tafarki, bari mu bada misali akan haka: da ace zamuga wani mutum yana kira zuwa ga musulunci sannan yana da wasu siffofi ne masu muni kamar karya da ha'inci da yaudara to shin zamuce ai haka addinin musulunci ne yake kira da zuwa ga wannan munanan dabi'un?? Lallai adalci da abunda yafe dacewa a wurin hukunci game da irin wannan hali shine mutum ya koma zuwa ga karantar muslunci na asali da kuma littattafai na asali ingantattu domin sanin gaskiyar musulunci. Sannan kuma mutum yasan cewa siffar kamala da cika ta Allah ne shi kadai madaukaki sannan kuma takaitawa da sakaci bawai ya takaita bane ga musulmai su kadai ba a'a gabaki daya dan adam ajizi ne saboda haka zakaga ana samun takaituwa da tsaiko a cikin al'amuransa na rayuwan dauniya da addinin sa da zaman takewar sa.
Kokarin muslunci wurin ganin ya samar da abubuwan da suka zama lalura a rayuan dan adam.
Lallai musulunci yana kokari tukuru wurin ganin ya samar da al'umma ta gari ta hanyar samar da ka'idoji wanda zai kiyaye mutane da kuma rayuwa ta jij dadi wanda zai basu cikakken hakkokin su domin su samu natsuwa da kwanciyar hankali a tsakanin su, manzon Allah s.a.w yana cewa: "ku saurara kuji lallai jinin ku da dukiyar ku da mutuncin ku haramun ne a gareku kamar haramcin wannan rana taku cikin wannan wata naku me haramci kuma a cikin wannan gari naku shima me haramci"[10].
Addinin musulunci yana aiki tukuru wajen samar da al'umma tare da samar masu da abubuwa Kaman haka a tsakanin su:
- Samar masu da cikakken tsaro ta dukkanin bangarorin sa kamar:
- Samar da tsaro akan dukiyar mutane, Allah madaukai yana cewa: " yaku wanda sukayi imani kada ku rika cin dukiyoyin ku a tsakanin ku da barna sai dai idan kasuwanci ne wanda kuka gina shi akan yarda a tsakanin ku"[11].
- Samar da tsaro ta bangaren mutuncin mutane, Allah madaukaki yace: " lallai wanda suke jifan mata muminai masu kame kansu da wani aikin alfasha sannan kuma suka kasa zuwa da shaidu guda hudu akan haka to ku masu bulala tamanin sannan kuma kada ku sake amsan shaidar su har abadan, kuma wannan sune fasikai (4)"[12].
- Samar da tsaro ta bangaren rayukan mutane, Allah madaukaki yace: "kace masu ya Muhammad kuzo na karanta maku abubuwan da Ubangijin ku ya haramta cewa kada ku hada shi da wani cikin bauta sannan kuma ku kyautatawa iyayenku, kada kuma ku rika kasha yaranku saboda tsoron talauci mune muke azurta ku dasu yaran baki daya, sannan kuma kada ku kusance alfasha na fili dana boye, kuma kada ku kasha rai wanda Allah ya haramta sai da hakkin haka, da wannan ne nake maku wasiyya koda zaku hankaltu (151)"[13].
- Samar da tsaro ta bangaren hankulan mutane, manzon Allah s.a.w yana cewa: " dukkanin abun da yake bugarwa giya ne kuma dukkanin giya haramun ne"[14].
Baya halatta tsoratar da mutane da kuma yada tsora a tsakanin su ta hanyar masu kashedi da ta Magana, hakika an rawaito hadisi daga annabi s.a.w yana cewa: " duk wanda ya tsoratar da wani mumini ya zama hakki agun Allah da yaki amintar dashi daga tashin hankalin ranan alkiyama"[15] Dabari ne ya rawaito hadisin albani ya raunata shi cikin littafin san a da'iful jami'u lambar hadisi na 5362.
Ko kuma tsoratar da mumini ta hanyar nuna masa makami, manzon Allah s.a.w yana cewa: " kada dayanku ya nuna ma dan uwanshi makami saboda besani ba kila shedan ya ingiza hannun sa sai ya fada cikin ramin wutan ranan alkiyama"[16] buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Musulunci yanason samar da al'umma me cike da zaman lafiya da tsaro wanda mutum zai samu damar kaiwa da komowa acikin ta da neman halaliyar sa ta hanyar aiki da tafiye tafiye a doron kasar Allah, saboda haka ne musulunci ya wajabta yin haddi (hukunce hukunce) dan hukunta masu laifi wanda suke kokarin lalata zaman lafiyar kasa.
- Samar da abinci a tsakanin su ta hanyoyi kamar haka:
- Samar da hanyoyi da dama dayawa na ayyuka ga mutanen da zasu iya domin ganin cewa ya samar masu da aminci dangane da bukatunsu na lalurorin su da kuma kosar dasu daga burice buricen su ta hanyar kwadaitar da mutane yin aiki, manzon Allah s.a.w yana cewa: " yafi alheri ga dayanku daya dau itace a kafadansa yaje ya siyar ya samu rufin asirin sa daga Allah ya fiye masa alheri da yaje yana rokon mutane su bashi ko kuma su hanashi"[17].
- Musulunci yayi umurni da arika ciyar da mutanen da bazasu iya aiki ba saboda tsofar su ko kuma rashin lafiyar su ko marayu daga baitil malin musulmai, manzon Allah s.a.w yana cewa: " duk wanda ya mutu yabar dukiya to na iyalansa ne sannan kuma duk wanda yabar yara ko kuma iyalai mabukata nauyin su yana kai na nine majibincin muminai" hadisi ne ingantacce muslim da Ahmad ne suka rawaito shi.
- Musulunci ya wajabata bayar da zakka ga talakawa da miskinai cikin al'ummar musulmai, wanda hakan shi yake karantar da taimakekeniya a tsakanin al'umma cikin addinin musulunci na amsan zakka daga hannun masu kudi da bayar dashi ga talakawa saboda fadin manzon Allah s.a.w ga mu'azu dan jabal lokacin daya aikeshi zuwa kasar yaman: "…..ka sanar dasu cewa lallai Allah ya wajabta masu zakka cikin dukiyar su wanda za'a karba daga hannaun masu kudin su a bawa talakawar su"[18].
- Musulunci ya kwadaitar da bayar da sadaka da nafila wanda musulmi yake bayar da ita dason zuciyar sa domin toshe bukatu nay an uwansa yana me neman ladan haka agun Allah da yardan sa, manzon Allah s.a.w yace: " yaku mutane! Ku yada sallama a tsakanin ku sannan kuma ku sadar da zumunta kuma ku ciyar da mabukata, kuma kuyi salla cikin dare a lokacin da mutane suke bacci, zaku shiga aljanna cikin aminci" Tirmizi ne ya rawaito hadisin ya kuma ingantashi.
Manzon Allah s.a.w ya kara cewa:" duk wanda ya yayewa wani mumuni wata damuwa cikin damuwar duniya Allah zai yaye masa damuwa cikin damuwar ranan alkiyama, duk wanda ya yalwatama mutumin dake cikin kunci Allah zai yalwata mashi duniya da lahira, duk wanda ya suturta musulmi Allah zai suturtashi duniya da lahira, Allah yana cikin taimakon bawa matukar yana taimakaon dan uwansa" muslim ne ya rawaito hadisin.
Manzon Allah s.a.w yakara cewa kuma: " mafi soyuwan mutane a wurin Allah shine wanda yafi amfanar da mutane, sannan kuma mafi soyuwan ayyuka agun Allah shine farin cikin da zaka saka musulmi ko kuma ka yaye masa wata damuwa tashi ko ka biya masa bashin sa da ake binsa ko ka kore masa yunwan, yafi soyuwa a gareni nayi aiki wurin biyan bukatan dan uwana musulmi danayi ittakafi cikin wannan masallaci nawa na tsawon wata daya, duk wanda ya kame fushin sa Allah zai rufa masa asiri, sannan duk wanda ya hadiye fushin sa wanda daya ga dama zai aiwatar da ita Allah zai cika masa zuciyar sa da yarda reanan alkiyama, duk wanda ya tsaya tsayin daka wurin biyan bukatar dan uwansa musulmi har hakan ya tabbata Allah zai tabbatar da diga digansa ranan da diga digai suke girgiza, lallai mummunan mu'amala tana lallata aiki kamar yadda madaci yake lallata zuma". Sahihul jami'u.
- Musulunci yayi alkawarin azaba me tsanani da duk mutumin da baya damuwa da halin yan uwansa musulmai, manzon Allah s.a.w yana cewa: " imanin dayan ku baya cika har sai ya soma dan uwansa abunda yake soma kansa" buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
- Musulunci yana samar da ilimi ga al'umma, allah madaukaki yace: " Allah zai daga darajan wanda sukayi imani daga cikin ku wanda kuma aka basu ilimi suna da darajoji"[19]
Ilimi a cikin al'ummar musulmai baya takaita bane ga daidaikun su ya zama wajibi akan kowa cikinsu ya nemi ilimi wanda zai yi rayuwan san a duniya dana lahira dashi, sannan kuma ya zama wajibi ga hukumar kasashen musulmai su samar da duk wani abu da zai taimaka wurin samar da ilimi ga al'ummanta, manzon Allah s.a.w yana cewa: " neman ilimi wajibi ne akan ko wani musulmi"[20] sahihul jami'u 3913, da sahihul targib wattarhib 72.
Kamar yadda musulunci ya tabbatar da hanyar neman ilimi da wahalhalun hakan daga cikin hanyoyin samun aljanna, manzon allah s.a.w yana cewa: "…. Duk wanda ya riki wata hanya yana me neman ilimi acikinta Allah zai sawwake masa hanya zuwa aljanna…."[21].
Sannan musulunci ya irga buye ilimi da rashin yadashi dan aci amfaninsa cikin ayyukan da aka haramta a shari'a sannan kuma yayi tsawatarwa akan haka me tsanani, manzon Allah s.a.w yace: " duk wanda ya boye wani ilimi Allah zai sanya masa linzami na wuta ranan alkiyama"[22] hadisi ne in gantacce.
- Musulunci ya samar da hanyoyin lafiya cikin al'umma ta hanyoyi kamar haka:
- Haramta duk wani abu da zaiyi tasiri wurin haifar da rashin lafiya ga mutum kamar shan kayan maye da miyagun kwayoyi, Allah madaukaki yana cewa: " yaku wanda sukayi imani lallai giya da caca da baiko da gumaka da dara datt ne cikin ayyukan shedan ku nesance su koda zaku samu rabauta da tsira (90)"[23].
- Haramta cin mushe da jinni da naman alade, Allah madaukaki yana cewa: "an haramta maku mushe da jinni da naman alade da duk bunda aka ambaci wanin Allah wurin yankashi da dabbar da aka shaketa ta mutu dabbar da aka duketa da wani abu ta mutu da dabbar da ta fado daga bisa ta mutu da dabbar da wata ta soketa da kaho ta mutu da abunda dabbar farauta taci ta rage sai dai idan kun samu yankawa da abunda aka yankama gumaka da kuma yin rantsuwa da guma wa'innan duka ayyukan fasikanci ne"[24].
- Haramta aikata alfasha kamar luwadi da zina da madigo, Allah madaukaki yace: " kada ku kusanci zina domin ta kasance alfasha kuma mummunar hanya (32)"[25].
- Samar ma al'umma da kariya ta lafiya da kuma tabbatar da dukkanin hanyoyin inganta lafiya, manzon Allah s.a.w yana cewa: " idan kunji labarin annoba a wani gari kada ku shigeta amma kuma idan annoba ta afkoma kasar ku kada ku gudu daga cikinta"[26].
Da kuma hanyan yima kai riga kafi, manzon Allah s.a.w yana cewa: " kada wani me lafiya ya shiga wurin wani me cucan dake yaduwa"[27].
Dukkanin abunda aka lissafo na samar da abubuwa na lalura wanda kowani dan adam ke bukata, manzon Allah s.a.w yana cewa: " duk wanda ya wayi gari yana me cikakken lafiya da kwanciyan hankali cikin gidan sa da iyalinsa kuma yanada abuncin da zaici na wannan rana kamar an tattara masa duniya ne baki dayan sa"[28] sahihul jami'u 6042, da sahihah 2318.
Dai-dai ko a musulunci:
Musulunci yayi aiki tukuru wurin kawar da dukkanin abun dake haifar da banbance banbance tsakanin al'ummar musulmai na abunda ya shafi dangantaka ko kalar fata ko bangaren kasa ko yare, Allah madaukaki yace: " yaku mutane kuji tsoron ubangijin ku wanda ya halicce ku daga mutum daya sannan kuma ya halitta masa matar sa daga jikinsa ya kuma yada al'umma maza da mata a tsakanin su"[29] .
Anyi haka ne saboda kowa yayi rayuwa da morewa hakkinsa cikin al'umma sannan kuma kowa yaji cewa yanada hakki bawai ya takaita bane ga wasu mutane, manzon Allah s.a.w yace: " yaku mutane ku saurara kuji lallai ubangijin ku daya ne kuma babanku daya ne, saboda haka balarabe bashi da wani fifiko akan wand aba balarabe ba ko kuma wand aba balarabe ba bashi da wani fifiko akan balara be, ko farin mutum bashi da wani fifiko akan bakin mutum sai da tsoron Allah kadai"[30] hadisi ne ingantacce.
Asalin mutum a musulunci ya fara ne daga abu daya saboda haka babu wani dama ta fariya a cikin musulunci da dangantaka da matsayi wanda zai kawo wulakanta wasu da kaskantar dasu dacin hakkokin su, manzon Allah s.a.w yana cewa: " yaku mutane lallai Allah ya kawar maku da dabi'ar zamanin jahiliyya na alfahari da iyaye, mutane gida biyu ne, kodai masu biyya da tsoron Allah wanda suke da karamci a wurin Allah, ko kuma fajirci da bijirewa wanda basu da wani kima agun Allah, mutane yayan Adam ne sannan kuma Allah ya halicci adam ne daga tabo….."[31] . hadisi ne in gantacce cikin littafin sahihah 2803.
Babu wani dama a cikin musulunci na zalumci da nuna banbanci ko kuma alfahari a tsakanin mutane saboda kalar fatar su ko jinsin su watan abunda ayau ake kira da suna nuna kabilanci, hakika yahudawa da kiristoci sun kasance suna ikirarin cewa sune mafifitan mutane sai allah madaukaki yace yana me bayanin karyan ikirarin su da kuma nuna cewa lallai mutane daya suke babu wanda yafi wani sai wanda yafi tsoron Allah acikin su: " yahudawa da kiristoci sunce mu yayan Allah ne kuma yan gaban goshin sa, kace masu idan haka ne me yasa yake azabtar daku da zunuban da kuka aikata, baku kasance ba sai mutane kamar sauran mutane cikin halittun sa"[32].
An karbo hadisi daga Ma'amur dan Suwaid yace: naga abu zarri algifari sanye da tufa me kyau iri daya da wanda bawan sa ke sanye dashi sai na tambayeshi nace ya naga kasa kaya iri daya da bawanka? Sai yace wata rana na zagi wnai mutum sai yakai karana wurin manzon Allah s.a.w sai yacemun: (ya abu zarri yanzu ka zageshi da mahaifiyar sa? Lallai kai wani irin mutum ne wanda har yanzu akwai sauran fiffan mutanen jahiliyya tattare dakai, masu maku hidima fay an uwanku ne wanda Allah yasanya su a karkashin ku, saboda haka duk wanda wani dan uwansa ya kasance a karkashin say a ciyar dashi daga abinda yaci sannan kuma ya tufatar dashi irin tufar dana tufatar da kansa kuma kada ku sanya su aikin da bazasu iya ba, idan kuma kun sanya su aikin da bazasu iyaba to ku tayasu). Buhari ne ya rawaito hadisin.
Haka abun yake ta bangaren ibada mutane daya suke wurin ibada me kudin su da talakar su, shugaba da wanda ake shugabanta, fari da baki, me matsayi da wanda bashi da matsayin komai babu wani bauta ko umurni ko hani wanda ya kebanta ga wasu nau'in mutane kawai banda sauran, mutane daya suke a gaban Allah, Allah madaukaki yace: " duk wanda yayi aiki na kwarai sakamakon na gareshi wanda kuma ya munana aiki zunubin haka nakansa ubangijinka bame zalumtar bayin sa bane (46)"[33].
Haka a bangaren hukunci da shari'ar musulunci da kuma aiwatar da hukunce hukuncen laifukan cikinta babu banbanci a tsakanin mutane ba'a kebance wata ukubaba ga wasu nau'i na mutane ba su kadai haka kuma babu wani abu da zai ba wasu nau'in mutane kariya wanda zai hana a masu hukunci, an karbo hadisi daga Aisha Allah yakara mata yarda cewa kuraishawa sun shagaltu da al'amarin matar nan yar kabilar makhzumatu wacce tayi sata suna cewa: wanenen zai yima manzon Allah Magana akanta a sassauta mata hukunci? Sia sukace babu wanda zai iya tunkarar manzon Allah s.a.w da haka sai Usama dan Zaid dan gaban goshin manzon Allah s.a.w sai Usama yayi masa Magana yana nema mata ceto daga hukuncin yanke hannu sai manzon Allah s.a.w yace mashi: " yanzu kana neman ceto a cikin hukuncin Allah madaukaki? " sai manzon Allah s.a.w ya mike yana khudba da cewa: " lallai abunda ya halaka mutanen da suka gabace ku shune sun kasance idan me matsayi a cikinsu yayi sata sai su kyale shi suki yanke masa hukunci amma idan me rauni acikinsu yayi sata sais u yanke masa hukunci, ina me rantsuwa da Allah da ace fadima diyar manzon Allah zatayi sata sai nayanke mata hannu"[34].
Haka al'amarin yake ta bangaren amfani da rabon arzikin kasa musulunci yaba kowa yanci dai dai da kowa cikin al'ummar musulmai ba'a ana mufin kudin da mutum ya samo ba sakamakon aikin da yayi da karfinsa ba ko dabarar sa wannan mallakin kansa ne shi kadai sannan kuma a cikin irin wannan yanayi ana samun banbanci tsakanin mutane babu shakka, ga Abubakar Siddiq nan khalifar manzon Allah s.a.w na farko yana rabon kyauta atsakanin mutane musulmai bai day aba tare da banbanci ba sai akace masa: ya khalifar manzon Allah s.a.w kana rabo wannan kudi a tsakanin mutane bai daya daidai wa daida alhali kuma acikin mutane akwai masu falala da wanda suka riga musulunta me yasa bazaka banbanta ba tsakanin mutanen da suka riga musulunta da falala akan sauran? Sai yace: abunda kuka fada na falalar wanda suka musulunta wurin rabo bansan wani abu ba game da haka akan rabon dukiya wannan aiki nasu sakamakon sa yana gun Allah amma kam rabon kudi dai daito yafi zama alheri akan cewa a banbanta wani a cikinsa saboda ya riga musuluntar sa dayayi, duk wanda sukayi aiki domin Allah sakamakon su yana wurin Allah, wannan kudi kuma hakki ne wanda bawan Allah me biyayya ga wanda yake fajiri duk zasuci daga cikin sa wanda bawai ladan ayyukan su bane.[35]
Ko wani mutum cikin al'ummar musulmai yana da hakkin amfanuwa da dukkanin arzikin da Allah yayiwa kasa, ya zama wajibi akan hukumar kasashen usulmai samar da damar ayyuka da kuma tsara yadda muatane zasu amfanu da wannan arziki na kasa ta yadda baza takaitu ga wasu mutane ba kawai abar wasu abaya, Allah madaukaki yana cewa: " shine wanda yasanya maku kasa yalwatacciya kuyi kai komo a cikinta kuma kuci daga cikin arzukinta kuma gareshi za'a koma baki daya (15)[36].
Musulunci ya daidaita tsakanin mutane cikin dukkanin al'amuran daya shafi rayuwan duniya da darajar dan adam babu wani banbanci ko soyayya ga wani bangare amma ta bangaren abunda ya shafi al'amuran lahira kuwa akwia banbanci tsakanin mutane da tazara me yawa, mutumin dayayi aiki bazai zama day aba da wanda bayyi ba kasalalle, haka kuma wanda yayi aikin kwarai bazai zama dai dai ba da wanda yayi aikin barna, llah madaukaki yace: " kowa yana da daraja daga irin aikin daya aikata ubangijin ka bai kasance ba me rabkana daga abunda suka kasance suna aikatawa ba (132)"[37].
Kiyaye abubuwan da suka zama lalura ga rayuwan dan Adam a cikin musulunci
Kakika musulince yazo ne domin cika sauran shari'ar addinan da suka gabace mu wanda suke daga Allah sannan kuma manzon muslunci Muhammad s.a.w shine cikamakon Annabawa da manzanni Amincin Allah ya tabbata a garesu, musulunci yana kokarin ganin ya samar da kuma kiyaye abubuwan da suka zama ginshikai na lalurar rayuwan dan Adam da kuma kiyaye rayuwansu domin cigaba kamar yadda sauran shari'un da suka gabace shi daga Allah sukayi irin wannann kokari, musulunci yazo ne da kokarin kiyaye wannan abubuwa kamar haka:
Kiyaye addini.
Addini akida ce wanda take zama ginshiki da dokoki na gina rayuwan mutum da al'umma baki daya, daga cikin akidu akwai wanda yake na zuciya ne kawai sannan akwai kuma wanda yaci karo da fidiran dan adam da hankali me lafiya ina nufin duk wata akida wacce take kira zuwa ga bauta da tsarkake wani halitta cikin halittun Allah kamar yadda Allah ya bada labara akan su cikin fadin sa cewa: " sun riki wasu Alloli koma bayan sa wanda basa halittan komai sudin halittar su akayi…." Suratul furkan ayata 3.
Daga cikin wannan akidu akwai wanda bin son rai ne kawai da kuma kosar wa da biyan bukatun shawa'a itace duk wata ikida wacce take girmama wani abu me ganagan jiki da kuma wurgi da duk wani abunda bashi ba kamar yadda Allah madaukak ya abda labara cikin fadin sa cewa: " shin bakaga wanda ya riki son zuciyar sa ba ta koma abun bautansa…." Suratul jasiya ayata 23.
Sannan kuma daga cikin akida akwai wanda ya kunshi zuciya da gangan jiki wanda shine addinin musulunci wanda baya banbancewa tsakanin zuciya da ganagan jiki haslima ya hadasu ne tare wanda guda daya acikin su baya iya yalwatuwa da barin dayan, akwai wasu umurni da suke ishara da kula da zuciya kmar yadda take umurni da kula da gangan jiki haka kuma akwai wasu hani wanda suke kunshi zuciya kamar yadda take hani ga dukkanin wani abu dazai cucar da gangan jiki, Allah madaukaki yace: " ka nemi gidan lahira da abunda Allah ya hure maka sannan kuma kada ka manta da rabonka na duniya ka kyautata kamar yadda Allah ya kyautata maka " sannan kuma ya kara cewa: " ya ubangujun mu ka bamu kyawawa anan duniya sannan kuma ka bamu kyawawa a lahira ka kuma tsare mu daga azabar wuta (201) suratul bakara.
Matukar musulunci ya kasance addini da kuma kasa wanda, kuma shune addinin da Allah ya yardan ma mutane baki daya ya zaman masu addinin karshe kuma cikamakon addinai ya kasance matsakaici wanda baya cin karo da fidiran ko kuma dabi'a, to ya zama wajibi ga al'umma wanda suka yarda dashi dasu kiyaye shi ta hanyar aiki tukuru domin kira zuwa gareshi da kuma nunama mutane kyawun sa ta hanyar amfani da kyawawan kalamai da kuma mu'amala me kyau wanda addininsa ya karantar dashi su saboda fadin Allah madaukaki cewa: " ku rika fadin Magana masu dadi ga mutane kuma ku tsaida sallah ku kuma bada zakka" suratul bakara ayata 83.
Hakika dokikin musulunci sun kunshi kariya ga mutum saboda kasancewar su sun kunshi dokoki masu falala na alheri da adalci da soyayya da rahama wanda suke samar da al'umma masu daraja wanda dukkanin dan adam ke burin rayuwa a cikinta.
Daga cikin hanyoyin kiyaye Addini shine kasancewar musulunci yayi umurni da abubuwa kamar haka:
- Ya umurci mabiyansa da kiyayeshi ta hanyar ilimi akansa ingantacce wanda yayi nesa da tsanantawa da wuce gona da iri cikin addini ko kuma yin sakaci dayawa akansa karkashin yin aiki da fadin manzon Allah s.a.w cewa: "Allah be aiko nib a dan na zama me tsanantawa ko kuma me yin sakaci ya aiko ni ne nazama malami kuma me saukake al'amura" muslim ne ya rawaito hadisin.
- Ya umjurci mabiyansa da kada su haifar da makiyan musulunci ta hanyar tilasta mutane da sasu bin wannan addini da karfin tuwo, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " ka fadi gaskiya daga wurin ubangijinka duk wanda yaso yayi imani wanda kuma yaso ya kafurce, lallai mun tanadarwa azzalumi wuta wacce take shanye gabbansu…." Suratul kahafi ayata 29.
- Ya umurci mabiyansa da kada suyi gaggawa wurin ganin sakamakon isar da musulunci ga wand aba musulmai ba, Allah madaukaki yana cewa: " lallai mun saukar maka da littafi zuwa ga mutane da gaskiya, duk wanda ya shiryu sakamakon haka yana gareshi wanda kuma ya bace to lallai sakamakon bacewar yana gareshi, baka zama wakili ba akan su (41)" suratu zumar ayata 41.
- Ya umurci mabiyansa dayin riko da karantarwan sa wanda yake kiran mutane zuwa gareshi da kuma aiwatar dashi a aikace domin ya zama kariya da kuma tarbiyyan jama'a akansa da kuma kiran mutane zuwa gareshi ta hanyar aiwatar da kyawawan karantarwansa wanda ya kunshi kyawawan mu'amala saboda haka ne ma Allah ya zirgi mutumin da aikin sa yake sabawa abunda yake fadi cikin fadin sa cewa: " shin kuna umurtan mutane da kyakyawan aiki alhali kuna manta kawunan ku bakwa aikatawa" suratul bakara ayata 44.
- Ya umurci mabiyansa da su rika tausayin mutane baki daya, manzon Allah s.a.w yana cewa: masu tausayi Allah yana tausaya masu, kuji tausayin mutanen doron kasa sai Allah yaji tausayin ku" Ahmad da tirmizi da abu dawud ne suka rawaito hadisin kuma albani ya ingantashi cikin sahihul jami'u 3522, da kuma sahihah 925.
Kuma ya umurce su son alheri ga mutane baki daya, saboda fadin sa s.a.w: " kasoma mutane abunda kake soma kanka sai ka zama musulmi" Tirmizi ne ya rawaito hadisin kuma hadisin ne ingantacce cikin littafin sahihah 72.
- Musulunci ya tanadar da lada me dunbin yawa ga duk me kira zuwa gareshi da karantar da mutane shi saboda zaman lafiya da tsaro da kwanciyan hankali ya wanzu a tsakanin su wanda ko wani mutum yake fatan samun haka ta hanyar karantar karantar da musulunci , manzon Allah s.a.w yana cewa: "Allah ya shiryar da wani mutum daya ta sanadiyyar ka yafiye maka alheri da a baka garkin jan rakumi" buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Me karatu kada kamanta cewa kiyaye addini yana daga cikin karantarwan da addinan da suka gabace mu suka zo dashi cikin shari'ar su.
Kiyaye Rai
Lallai rai dan adam abuce me matukar kima da daraja a cikin addinin musulunci sannan kuma musulunci ya taba kariya matuka, manzon Allah s.a.w yana cewa: " na rantse da wanda raina ke hannun sa kasha ran mumini daya yafi girma agun Allah sama da rasa duniya baki dayanta"[38]. Ibn majjah ne ya rawaito hadisin kuma albani ya inganta shi cikin littafin sahihul jami'u 5078, da sahihul targib wattarhib 2438.
Musulunci yana kiyaye ran dan adam ta hanyoyi Kaman haka:
- Kare ran dan adam agun dan uwansa saboda haka ne musulunci ya hukunta kisasi yadda yayi umurni da akashe mutumin daya kashe wani da gangan matukar waliyyan wannan wanda aka kasha basu yafe a kasha shi ba shima, amma kisan da mutum yayi bisa kuskure yana da hukuncin sa a musulunci na biyan diyya da kuma yin kaffara- watan yay anta bawa idan kuma baidashi sai yayi azumin wata biyu ajere idan kuma bazai iya ba sai ya ciyar da miskinai sittin- anyi haka ne saboda a kiyaye rai da rayuwan dan adam daga hannun yan ta'adda kada su salwantar da ita, saboda duk wanda yasan cewa fa idan ya kasha shima za'a kasha shi ne kai tsaye to zayyi kokari kin yin kisa, badan kuwa yasan cewa hukuncin laifin wanda yayi kisa shima kasha akeyi ba da bai fasa yin kisan ba, Ka kiyasta sauran hukunce hukuncen aikin ta'addanci a musulunci wanda ake cema hudud akan wannan hukunci zakaga tafi amfani da dacewa wanda ba'asanya su sai dan a kare mutum da hakkokin sa, Allah madaukaki yace: " kunada rayuwa acikin kisasi yaku ma'abota hankula koda zaku samu takawa (179)"[39].
Musulunci be say aba kawai akan wannan ukubar ta duniya akan duk mutumin da yayi kisa da gangan ya tanadar masa kuma da azaba a lahira wanda ta kunshi fushin Allah akan mutum da azaba me tsanani, Allah madaukaki yace: " duk wanda ya kasha mumini da gangan to sakamakon sa shine jahannama yana me dawwama acikinta kuma Allah yayi gfushi dashi ya kuma tsine masa kuma ya tanadar masa da azaba me girma (93)[40].
- Muslunci ya kare mutum daga sharrin zuciyar sa wanda take umurtansa da aikata munanan ayyuka, hakika ya wajabtama dan adam kiyaye hakan ta hanyoyi kamar haka:
- Musulunci ya hana mutum yakai kansa zuwa ga halaka saboda rai ba mallakin sa bane mallaki ne na Allah madaukaki saboda haka kada kayi amfani da ita sai ta hanyar sa da ya yarda da hakan, saboda haka musulunci ya hana mutum ya kasha kansa cikin fadin Allah madaukaki cewa: " kada ku kasha kawunanku lallai Allah ya kasance me tausayi da rahama a gare ku (29)"[41].
- Musulunci ya umurci dan adam da ya rika ba ransa hakkokinta, baya halatta ya rika zalumtar ransa ta hanyar hanata abunda da Allah ya halatta mata na cin abinci da shan abubuwa da sanya tufafi da aure, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " kace wanene ya haramta kayayyakin kawa wanda na Allah wanda ya fitar dasu dan bayin sa da kuma dadaden abubuwa daga arziki"[42]. Sai dai wannan jin dadi da wannan kayayyaki na more rayuwa sunada iyakokin su da dokoki wanda shari'a tayi umurni dashi na rashin yin almubazaranci ko kuma girman kai cikin hakan, saboda fadin Allah madaukaki: " kuci kusha kada kuyi almubazaranci domin lallai Allah bayason masu almubazaranci (31)"[43] .
Baya halatta cikin musulunci mutum yayi watsi da jikin sa da azabtar da ita ko kuma hanata abunda take bukata koda kuwa hakan ta hanyar ibada ne ga Allah, an karbo hadisi daga Anas dan malik Allah yakara masu yarda yace: wasu mutane uku sunzo gidan manzon Allah suna tambayan matan sa game da ibadun san a gida, bayan sun fada masu yadda yake ibada a gida sai sukace idan dai har manzon Allah s.a.w wanda aka gafarta masa zunubansa baki daya wanda yayi da wanda zayyi zai rika yin irin wannan inbada haka mu kuma fa ina muke lallai mu muka fi cancanta da hakan, sai dayan su yace: ni daga yau kullum sai na sallaci dare baki dayan sa, dayan kuma yace: ni daga yau kullum azumi zan rikayi, dayan kuma yace: ni daga yau babu ruwana da mace, sai labara yajema manzon Allah s.a.w ya kirasu yace masu: " kune kuka ce kaza da kaza ko? Ku sani cewa wallahi nafiku tsoron allah da kiyayeshi amma dukda haka ina sallah da daddare kuma nayi bacci, ina azumi wata rana nasha ruwa wata rana, kuma ina aure, saboda haka duk wanda ya kyamaci sunnata to baya tare dani"[44].
Kiyaye hankula
Hankali a musulunci shine sharadi ko kuma wurin daukan wajibobin da Allah ya daurama dan adam saboda haka ne musulunci ya haramta dukkanin wani abu da zaiyi tasiri wurin gusar da hankalin dan adam ta hanyar shan kayan maye da kwayoyi masu bugarwa, musulunce ya kira giya da sauran kayan maye irinta da sunan ummul kaba'isi saboda girman hatsarin sakamakon da take haifarwa na kawar da hankula duk dan saboda hankulan mutane su kasance masu lafiya da kuma kare mutuncin su da dukiyoyin su, zai shiga cikin wannan abuwan da suke tasiri ga hankula duk wata fikira da take halakar wa da kuma kira zuwa ga aikata barna da munanan abubuwa a doron kasa, Allah madaukaki yace : " yaku wanda sukayi imani lallai giy da caca da rantsuwa da gumaka da dara datti ne daga cikin ayyukan shedan saboda haka ku nesance su koda zaku rabauta (90) shedan ne kawai yake son ya yada kiyayya a tsakanin ku da gaba ta hanyar giya da caca kuma ya kange ku daga ambaton Allah da barin sallah, shin zaku hanu ku bari (91)"[45].
Saboda musulunci ya kawar da gina acikin al'umma yasa ya haramta yinta ko kuma kasuwanci da ita ko taimakawa wurin samar da ita ko yada ta, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " an tsine ma giya ta bangarori guda goma, ita kanta, da me yinta dan yasha ko kuma dan ya siyar ma wasu su sha, da me siyar da ita, da me siyan ta, da me dakonta, da me daurawan, da me cin kudinta, da me shanta, da me tallanta"[46]. Ahmad da Ibn majjah ne suka rawaito hadisin kuma albani ya igantashi cikin littafin al irwa'i 1529.
Kiyaye mutumci
Musulunci ya haramta dukkanin abunda yake jawo cin mutuncin musulmi kai tsaye ko ta shagume, saboda haka ne musulunci ya haramta abubuwa kamar haka:
- Musulunci ya haramta zina, Allah madaukaki yace: " kada ku kusanci zina domin ta kasance alfasha da mummunan hanya (32)"[47].
Kuma ya haramta dukkanin abun da zai kawo afkawa zina irinsu:
- Shafawa da runguman macen da ba matar mutum ba ko kuma wanda bata halatta mas aba, manzon Allah s.a.w yana cewa: " ko wani mutum yana aikata zina babu makawa, ido zinarta shine kallo, hannu kuma zinanshi shine tabawa, zuciya kuma zinanta shine sha'awar hakan sai farjin mutum ya karyata ko kuma ya gasgata"[48]. Hadisi ne ingantacce Ahmad da ibn hibban ne suka rawaito shi.
- Musulunci ya haramta kebanta da mace ba tare da muharraminta ba, manzon Allah s.a.w yana cewa: "kada dayanku ya kebanta da wata mace sai da muharraminta kusa sai wani mutum ya tashi yace ya manzon Allah matata ta tafi aikin haji kuma ni an rubuta ni cikin rundunan yakin kaza da kaza, sai manzon Allah s.a.w yace masa yi maza ka bi matanka kuyi aikin hajin tare"[49]. Buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
- Musulunci ya haramta kallon abunda yake haramun, Allah madaukaki yace: (" kace ma muminai maza su kiyaye ganin su kuma su kiyaye farjin su hakan shi yafi zafi tsabta a garesu lallai Allah ya kasance me bada labara game da abunda suke aikatawa (30) kuma kace ma muminai mata su kiyaye ganin su…..) suratun nur, kuma manzon Allah s.a.w yace ma aliyu: " ya aliyu kada ka rika bibiyan kallo akan kallo, domin kuwa kallon farko baza'a rubuta maka zunubi ba akai amma kallo na biyu za'a rubuta maka zunubi akai". Tirmizi da abu dawud ne suka rawaito hadisin kuma albani ya inganta shi.
- Haka kuma musulunci ya haramta kazaki domin kiyaye mjutuncin mutane, duk wanda ya tuhumi wani mutam ko mace da aikata wani aikin alfasha kuma ya kasa tabbatar da haka da shaidu za'a masa haddin me kazafi na bulala tamanin, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " wanda suke jifan muminai salihai masu kama kai sa'annan kuma basuzo da shaidu hudu ba akan haka to kuyi masu bulala tamanin kuma kada ku kara amsar shaidar su har Abadan kuma wa'innan sune fasikai (4)"[50].
- Kamar yadda musulunci har wayau ya haramta dukkanin wani Magana ko kuma aiki wanda zai taba karamar mutum da darajar sa da rage masa kima a idon mutane da cucuwa da hakan saboda kiyaye mutunci, Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani kada wasunku su rika yima wasunku izgilanci me yuwa sunfisu alheri, haka ma daka mata su rika yima mata izgilanci suma me yuwa sunfi su alheri, kada ku rika jifan junanku da Magana marasa kyau kuma kada ku rika kiran kawunan ku da sunayen banza, tir da sunan fasikanci bayan imani, duk wanda kuma be tuba ba to wannan sune azzalumai (11) yaku wanda sukayi imani ku guji yawaita zato domin wasu zaton zunubi ne, kada kuma ku rika bin diddgin laifin junanku daka kuma shashin ku ya rika cin naman shashi, yanzu dayanku yana son yaci naman mushin dan uwansa ne saboda haka ku gujeshi, kuji tsoron Allah lallai Allah me yawan amsan tuba ne kuma me rahama (12)"[51].
Kiyaya dukiya
Hakika musulunci ya kewaye mallakan dukiyoyin mutane da kariya me karfin gaske domin bashi tsaro ta hanyar wajabta wasu hukunce hukunce na ukuba masu tsaurin gaske domin tabbatar da kare dukiya da kuma han wasu ta'addanci akan dukiyoyin mutane, musulunce ya hukunta yanke hannun barawo saboda kiyaye wannan mallakar, Allah madaukaki yace: " barawo da barauniya ku yanke masu hannu sakamakon abunda suka aikata daga Allah, Allah kuma ya kasance mabuwayi me hikima (38)"[52].
Yanke hannun arawo a musulunci bawai hakanan bane kawai babu wani sharadi kamar yadda mutanen da basusan hakikanin musulunci ba suke tsammani, hakika yanada sharudda wanda dole ne sai an same su kafin a yanke hannu da ace za'a rasa wani sharadi ko kuma shubuha ya shigo ciki shikenan baza'a yanke hannu ba, wannan sharuddan kuwa na yanke hannun me sata sune kamar haka:
- Ya kasance kudin da aka sata yana cikin a susu ko kuma boyayyen wuri wanda yaci sunan boyewa sai barayo ya fasa asusun ko kuma ya karya kofar wurin yayi sata, amma kudin da suke a fili kowa yana ganin su ko kuma ba'a boyesu a wani wuri ba idan wani ya sata irin wannan kudi baza'a yanke masa hannu ba sai dai a masa wani hukuncin daya dace domin a tsawatarwa wanda kuma shugaba shine yake da daman zartar da hukuncin nan wurin ance baza'a yanke hannun barawon bane saboda me dukiyan yayi sakaci akanta be kiyaye dukiyar sa ba.
- Ya kasance babu wata bukata ta abinci wacce tasa wannan mutumi sata, idan bukatar ci ne ko sha yasa shi yin wannan sata to baza'a yanke masa hannu ba saboda hukuncin dan Abdullahi dn Umar dayayi akan haka. Mu sani cewa wannan hukunci na haddi da sauran hukunce hukunce na haddi a musulunce ba'a zartar dasu sai idan babu wata shubaha akan haka, saboda ba'a zartar da haddi akan mutumin da akwai shubaha akan wanda ake tuhuma.
Sai dai kuma shari'a bayan ta kore zartar da haddi a lokacin da aka samu shubuha ta tabbatar da wani huknci na tsawatarwa ga wannan me laifi wanda be kai wannan haddi ba wanda alkali zai tabbatarwa mutum gwargwadon girman laifin sa gwargwadon ukubar da za'a masa kodai a daure shi ko kuma a mashi bulala ko kuma ya biya tara na kudi daidai makamantan su abunda alkali yaga yadace dashi.
Kamar yadda musulunci ya haramta dukkanin wasu aiki wanda akai ta'addanci akan mallakar wasu haramci me tsanani kamar kwace da cin filayen mutane da gonaki batare da hakki ba ko kuma kwace masu kudi ta hanyar da bata dace ba kamar fince da damfara, Allah madaukaki yace: " kada ku rika cin dukiyoyin ku a tsakanin ku da barna"[53].
Duk mutumin dayake ta'addanci akan dukiyoyin mutane ba tare da hakki ba zai hadu da ukuba me tsanani ranan alkiyama, saboda fadin manzon Allah s.a..w cewa: " duk wanda ya kwaci kudin wani mutum musulmi ba tare da hakki ba zai tarar da Allah mabuwayi yana me fushi dashi"[54]. Buhari da muslim da Ahmad da tirmizi ne suka rawaito hadisin.
Sannan musulunci ya wajabta ma mutumin dayayi kwcen kudin wani ko kuma ya sata da ya mayar masa da abunda ya sata ko kuma ya kwata, idan kuma ya cinye wannan abu sai ya biyashi kudin wannan abu amma idan me kayan ya yafe masa shikenan bazai biya ba, sannan kuma akwai ukuba na tsawatarwa akan mutumin da yayi kwace.
Kuma musulunci ya umurci me dukiya daya kare dukiyar sa ta hanyar da zai iya koda kuwa al'amarin zai kai zuwa ga kasha wannan barawo, idan kuma aka samu aksain haka aka kasha me kaya ta hanyar kokarin kare dukiyar sa ko yayi shahada saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: "duk wanda aka kashe shi akan kare dukiyar sa to yayi shahada"[55].
Hukuncin Tsuntuwa a musulunci:
Musulunci yazo da dokoki domin kare dukiyoyin jama'a dana mutum, amma anan wurin zamuyi Magana ne akan hakkokin mutum wanda suka shafi dukiya, dukiya a musulunci abuce wacce aka kiyayeta haramun ne wani yayi ta'adi acikinta hatta kudin tsuntuwa domin kuwa ba ko wani irin kudin tsuntuwa bane ya halatta ga wanda ya tsinceta yaci akwai dokoki da ka'idoji na abun da aka tsinta kafin wanda ya tsinta din ya iya cinta ko kuma yayi amfani da ita watan ta zama tashi kenan, daga cikin dokokin musulunci wanda ya shinfida domin kare dukiyan mutum akwai dokoki na tsuntuwa wanda yana cikin dokoki wanda wannan addini ya kebanta dashi, tsuntuwa dai it ace duk abunda mutum ya tsunta na kudi kuma ba'asan me shi ba, tsuntuwa yana iya zama na kudi ko kuma kuwa dabbobi du kana kiransu da sunan batattun hanya.
Hakika musulunci ya wajabta daukan tsuntuwa idan mutum ya ganta a wurin da babu aminci watan zai iya salwanta idan yabar shi a wurin ko kuma wani ya sace anyi haka ne domin a kiyaye dukiyoyin mutane daga salwanta da kuma mayar dashi zuwa ga masu shi idan an same su, saboda fadin manzon Allah s.a.w ga wani mutum da yazo masa yana tambayan sa akan abun tsuntuwa? Sai yace masa: " idan kayi tsuntuwa to ka san irin abunda take ciki da kuma irin igiyan da aka daureta dashi da kuma yawanta sai kuma kayi cigiyanta na tsawon shekara daya, idan me ita yazo kabashi kayan shi idan kuma be zo ba to kayi abunda kake so da ita" sai wannan mutum yace idan mutum ya tsinci akuya fa ko rago ya zayyi dasu? Sai manzon Allah s.a.w yace: " shidai tsuntuwan akuya ko rago naka ne ko kuma na dan uwanka ko kuma kabarma kura ta cinye" sai mutum yakara cewa: to rakuma fa? Sai manzon Allah s.a.w yace masa: " ina ruwanka da ita domin kuwa tana da abincin ta a cikin ma'ajiyi na jikinta da abunshan ta wanda zata rika ci da sha kuma zata rika wuce wa ta wurin wura tasha da bisha ko ciyayi taci har sai me ita ya ganta" buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Wannan hadisi yana Magana ne akan kayan tsuntuwa wanda ba'a basu da daraja kuma ba abinci bane, irin wannan baya wajabta neman me shi ya halatta mutum yayi amfani dashi kai tsaye ko kuma yaci kayansa, Anas dan malik Allah ya kara masa yarda yana cewa manzo Allah s.a.w ya wuce wani dabino akan hanya sai yace: " badan ina tsoron ace daga cikin kayan sadaka bane wannan dabinon dana dauka naci" buhari da muslim ne suka rawaito hadisin. (Manzon Allah s.a.w yace haka ne saboda Allah ya haramta masa cin sadaka).
Haka kayan tsuntuwa wanda basu da daraja ya halatta ga mutumin daya tsince su yayi amfani dasu saboda hadisin Aliyu Allah yakara masa yarda cewa yazo gun manzon Allah s.a.w da dinari wanda ya tsinceta a kasuwa sai manzon Allah s.a.w yace mashi: " kayi cigiyar me shin a kwana uku" sai Aliyu yayi cigiya na kwana ukun be samu me shi ba, sai manzon Allah s.a.w yace masa: " kaci ta zama naka" hadisin yazo ne cikin sunan abu dawud.
Sannan kuma wanda yayi tsuntuwan yana da hakkin yayi sadaka dashi da niyyar ladan yaje ga me kaya ko kuma yayi amfani dashi bayan cigiya da ajiyan shekara daya be samu me shi ba, saboda hadisin Aus dan Ka'ab da yake cewa: na tsinci a susu a ciki akwai dinari dari sai nazu gun manzon Allah s.a.w yacemun: " kayi cigiyar me shin a tsawon shekara daya" sai nayi cigiyan na shekara daya amma ban samu me shi ba, sai na kara dawowa wurin manzon Allah sau uku sai yace mun: "ka kiyaye irin asusun da igiyan da aka daure kudin da kuma yawansu idan me shi yazo kabiyashi kayan shi idan kuma be zo ba kayi amfani dashi" buhari ne ya rawaito hadisin.
Kiyaye dangantaka (nasaba):
Muslunci yaba dangantaka kula sosai saboda shine hanyan wanzuwar mutane kamar yadda Allah ya sanya su don su zama kahlifofin sa a bayan kasa, saboda hake ne muslunci ya haramta dukkanin abunda zai kawo wasa ko raunata shi da rageshi ko kuma yanke wanna wanyar na yaduwan mutane a doron kasa ta hanyar da bana shari'a ba, Allah madaukaki yace: " idan aka shugabantar dasu a doron kasa sais u koma masu barna acikin ta suna halaka gonaki da dangantaka, Allah bayason masu barna (205)"[56].
Sai musulunci ya hana zubar da ciki domin hakan ta'adi ne ga rayuwan dan adam sai dai idan tsayuwar cikin hatsari ne ga rayuwan mahaifiyar. Hakika musulunci ya kwadaitar da zabuwar da musulmai akan yin aure saboda su samu dangantaka da kuma samun zuriya, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " ku aure mata masu haihuwa wanda kuke son su, saboda zanyi alfari da yawanku yaran alkiyama"[57]. Hadisi ne in gantacce Ahmad da abu dawud da nasa'I da ibn Hibban ne suka rawaito shi.
Manzon Allah ya kara fadi har wayau cewa: " yaku taron samari duk wanda ya samu daman aure a cikin ku to yayi aure saboda hakan shine zai kiyaye masa idonsa daga kallon haramun da kuma kiyaye farjin sa daga yin zina, duk kuma wanda bai samu daman haka ba to ya rika yin azumi domin tana yanke sha'awa" buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Kiyaye zuriya:
Saboda matsayin iyalai da girman al'amarin ta a musulunci kasancewa shine wakilan wanda suke zama al'aumma, saboda kiyaye zuriya daga samun Baraka musulunci yayi tsayin daka akansa na bashi kulawa cikakke, a lokacin da ya zama zuriya shine sila na haduwar iyalai da dangi na kusa yasan na nesa domin ya bashi hakkin sa da Allah ya wajabta masa na sadar da zumunta da sauran hakkoki, manzon Allah s.a.w yana cewa: "kusan dangin ku wanda yay a wajaba ku rika sadar masu da zumunta domin sada zumunta yana haifar da soyayyar yan dangi kuma yana kara arziki da tsawon kwana"[58]. Hadisi ne in gantacce Ahmad da tirmizi ne suka rawaito shi, albani ya ingantashi cikin littafin sahihul jami'u 2965.
Saboda haka ne muslunci yayi tsayin daka wurin bashi kula da kuma kiyaye shi daga cakuduwa wanda zai haifar da rudani ga al'umma da kuma maganin aure tsakanin namiji da macen da take haramun ne ya aure ta da kuma bayar da gado ga mutumin da bashi da hakkin cin gadon ko kuma hana wanda ke da hakkin haki akan gadon.
Hakika musulunci ya haramta dukkani wasu hanyoyi na gina dangantaka da zuriya wanda ba hayar aure ba cikin hanyoyin da suka yada a tsakanin larabawa da wasun sun a dokoki da tsare tsare me muni, daga cikin irin wannan tsare tsare da musulunci ya haramta akwai:
- Tsarin zamar da wani yaronka wanda ake kira da (Tabanni): wannan tsari na tabanni yana nufin mutum ya samu wani yaro kawai cikin gari wanda bashi ya haifeshi ba sai yace inason ka zama yarona wanda zaici gadona idan na mutu da sauran hakkokin yaro akan ubansa, Allah madaukaki yace: " Allah be sanya wa mutum zuciya biyu ba a kirjin sa, kuma Allah be sanya wannan mat aba wanda kuce zihari dasu dacewa suna matsayin mahaifiyan ku ne su zama matayen ku, kuma be sanya yaran da kuke kira da sunan yaranku ba su zama yaranku na hakika, wannan kawai Magana ce kuke fadi da bakunan ku, Allah shine yake fadin gaskiya kuma shine me shiryarwa zuwa ga hanya ta gaskiya (4) ku rika kiransu da sunan iyayen su hakan shi yafi zama adalci a wurin Allah, idan kuma baku san iyayen su ba to yan uwanku ne a addini ba yaranku bane…."[59].
- Tsarin ikirarin mahaifi ga yaron sa: wannan tsari yana nufin yaron mutum wanda ya sameshi ta hanyar shari'a bazai zama yaron sa ba har sai wannan mutumi yayi ikiririn haka ta hanyar fadin haka a bayyane kuma ya yarda ya zama zuri'ar sa, musulunci ya haramta wanna tsari saboda yana cin fuska ga aure da kuma kiyaye martaban mace saboda a cikin hakan akwai tuhuma cikin darajar ta da kuma kama kanta da kuma abunda ke ciki na raba yara da iyayensu da kuma bacewar zuri'a, musulunci ya tabbatar da cewa duk wani yaron da aka sameshi ta hanyar saduwar aure ingantacce na shari'a yaron wannan mijin ne ba tare da anjira yardan sa akan jingina shi ba dashiki kuma ikirarinsa akan haka, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " yaro na wannan mijin ne da aka daurawa aure ingantacce"[60]. Buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Amma ancire a cikin wannan hukuncin matar da ya tabbata tana ha'intar mijinta wacce zata iya yin cikin da banashi ba, irin wannan abubuwa suna da hukunce hukuncen su a cikin littattafan fiqhu na musulunci wanda nan ba wurin tsawaita Magana bane akan hakan.
- Tsarin yin khul'i: wannan tsarin yana nufin mutum ya nemi rabuwa da wani yaro nashi cikin yaransa ta hanyar yarjejeniya wanda ya tabbata yaron sa ne a shari'ance, idan yayi hakan shikenan ya yanke dangantakar sa kenan dashi daganan ya zama cikin gama garin mutane wanda basu da wata dangantaka da wannan mutumi, manzon Allah s.a.w yana cewa: " abubuwa biyu acikin mutane kafurci ne, bata wani cikin zuri'a ba tare da dalili ba da kuma kuka na daga murya akan mamaci"[61] muslim ne ya rawaito hadisin.
- Danganta mace da mijinta bayan tayi aure: a musulunci mace zata kiyaye sonata da sunan babanta da ganginta na asali bayan aurenta, haramun ne a jinginata da sunan mijinta da dangin sa bayan tayi aure, wannan abu kuwa buba shakka akwai daraja mace a cikin sa da kuma bata gashin kanta da daidaita dana miji kasancewar su yan adam, manzon Allah s.a.w yace: " duk wanda ya riki wani wand aba ubansa ba a matsayin ubansa ya koma yana amfani da sunanshi dashi a matsayin mahaufinsa ko kuma ya riki maula wanda bashi ya yantashi bay a koma ubangidanshi to tsinuwan Allah ya tabbata akansa da mala'iku da mutane baki daya"[62]. Sahihu Ibn Hibban.
Musulunci ya kiyaye hakkokin mutane marasa karfi wanda daga cikin haka akwai:
- Kiyaye hakkokin gajiyayyyu da masu rauni, manzon Allah s.a.w yana cewa: " lallai Allah tsarkake mutane daga zunubai matukar me me raunin cikin su baya iya amsan hakkin sa agun me karfi ba tare da wani tsoro ba ko kokwanto"[63]. Sahihul baihaki da Ibn Majjah da Hakim.
An karbo hadisi daga Mus'ab dan Sa'ad cewa: manzon Allah s.a.w yace: "shin kuna ganin za'a baku nasara ne da arziki badan masu raunin cikin ku ba?!" buhari ne ya rawaito hadisin.
An karbo daha abu huraira Allah ya kara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace: "me kai komo akan harkokin miskinai da mata gajiyayyu kamar muhajidi ne dan daukaka Kalmar Allah, ko kuma me sallar dare da zumi da rana" buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
- Kiyaye hakkokin mabukata: Allah madaukaki yana cewa: " kuba makusantar ku hakkokin su da miskinai da matafiya kada kuyi almubazaranci cikin haka (26) lallai masu almubazaranci abokanan shedan ne, shedan kuma ya kasance kafiri ga ubangijin sa (27)"[64]. Ya madaukaki kuma ya kara cewa: "me tambaya kada ka tsawatar mas aka koreshi (10)"[65]
- Kiyaye hakkokin yara kanana, manzon Allah s.a.w yana cewa: "duk wanda baya tausayin kananan cikin mu kuma baya girmama manyan cikin mu to baya tare damu"[66] sahihul buhari cikin adabul mufrad da abu dawud.
- Kiyaye hakkokin tsofaffi, manzon Allah s.a.w yana cewa: "yana daga cikin girmama Allah martaba tsofaffin cikin musulmai, da mahaddacin alkur'ani wanda baya tsanantawa da wuce gona da iri wurin aiki dashi, da kuma martaba adalin shugaba" hadisi ne ingantacce, abu dawud ne ya rawaito shi.
- Kiyaye hakkokin marasa lafiya, manzon Allah s.a.w yace: " hakkin musulmi akan dan uwansa musulmi guda biyar ne, mayar masa da sallama, da duba mara lafiya, ta bin gawarsa, da amsa masa kira idan ya kira walima, da gaida me atishawa da masa addu'a"[67]. Buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
- Kiyaye hakkokin marayu, Allah madaukaki yace: " maraya kada a wulakantashi da kyamatar sa da koransa (9)"[68].
- Kiyaye hakkokin yara, Allah madaukaki yana cewa: " kada ku rika kasha yaranku domin tsoron talauci, lallai mune muke azurta ku da azurta su"[69].
Kiyaye arzikin kasa da kuma hana lalatashi ko ta'ada akanshi:
Lallai arzukin dake doron kasa na dunbin alherai ba mallakan wani mutum bane shi kadai banda wani ko kuma mallakar wasu mutane kadai banda sauran, mallakar kowa da kowa ne domin cin gajiyar shi da abunda zai tabbatar da maslahar wanda zai komawa mutum da al'ummar baki daya da alheri, daga cikin nauyin daya ratayu a wuyan kowa cikin al'ummar musulmi hukunta duk wanda yayi kokarin ta'adi ga arzikin kasa ko kuma yin amfani dashi ta hanyar da shari'ar musulunci be yarda dashi ba, Allah madaukaki yana cewa: " Allah shine wanda ya hure maku kogi domin jiragen ruwa su rika kai komo akansa da umurnin sa kuma dan ku nemi arziki daga falalar Allah acikin sa koda zaku gode masa (12) ya kuma hure maku abunda ke cikin sama da kasa baki daya daga gareshi shi kadai, lallai acikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani (13)"[70].
Hakkokin game al'aumma da na dai dai kun mutane a cikin musulunci:
Kasancewar musulunci yana aiki tukuru dan karfafa dangantakan al'umma da zumunci atsakanin su, wannan zumunci na kusa ne wanda ake kira da sunan dangantaka na jinni a musulunci wanda Allah yayi umurni da arika sadar da ita sannan kuma yayi alkawarin azaba me girma da wanda ya yanke ta, Allah madaukaki yace: yaku mutane kuji tsoron ubanjigin mu wanda ya halicce ku daga rai guda daya sannan kuma ya halitta masa mata kuma ya yada mutane maza da mata daga garesu, kuji tsoron Allah wanda kuke rokon sa kuma kuke sadar da zumunta domin shi, lallai Allah ya kasance me kallon dukkanin al'amuran ku da kuke gudanarwa (1)"[71].
Ko kuma dangantaka ta nesa wacce take hada mutumin cikin al'umma wasun su da wasu domin asamu hadin kai da tausayi a tsakanin al'ummar musulmai, musulunci ta umjurci musulmi da sauke nauyin dake kansa na wajibobi da hakkokin musulmai yan uwansa, manzon Allah s.a.w yana cewa: "kada kuyi hassada, daka kuyi ha'inci, kada kuyi kiyayya, kada ku juyama juna baya, kada kuma sashin ku yayi cikinin akan cinikin sashi, ku kasance bayin Allah yan uwan juna, musulmi dan uwan musulmi ne, kada ya zalumce shi kada kuma ya wulakanta shi, kada kuma ya kaskantar dashi, takwa na yananan sai yayi nuni zuwa ga kirjin sasau uku, ya isa mutum sharri ya wulakanta dan uwansa musulmi, dukkanin musulmi akan dan musulmi haramun ne jinin sa da dukiyan sa da kuma mutuncin sa"[72] sahihu muslim.
Shari'ar muslunci ta wajabta hakkokin gama garin mutune da kuma hakkokin dai daikon mutane cikin al'umma a cikin muslunci hakkoki hakar haka:
Hakkokin Allah wanda yake kunshe cikin Kalmar tauhidi watan " LA'ILAHA ILLALLAH" wannan shahadar ta kunshi abubuwa haka:
- Kadaita Allah cikin renon halittunsa, watan shine mutum ya kudurce cewa Akwai Allah kuma shi kadai ne ya halicci wannan duniyar da abunda ke cikinta kuma shine mamallakin ta me sarrafata, allah madaukaki yace: " ku saurara halitta da umurni nashi, tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin talikai (54)"[73].
- Kadaita Allah cikin sunayen sa da siffifin sa, hakan shine kudurcta cewa lallai Allah madaukaki yana da sunayi masu tsarki da siffifi masu kyawu madaukaka sannan kuma ya barranta daga dukkanin wani aibu ko nakasa, Allah madaukaki yace: "Allah yana d sunaye kyawawa ku kirashi dasu, ku kyale masu yin ta'adi cikin sunayen sa da sannu zai saka masu da abunda suke aikatawa (180)"[74].
Zamu tabbatar da abunda ya tabbatar ma kansa cikin unayen sa a cikin littafin sa ko kuma manzon sa Muhammad s.a.w ya tabbatar masa dasu wanda babu wani mahaluki da yayi kamancece niya dashi cikin su, ba tare da tambayar yaya yanayinsu yake ba ko kuma kore su da yin inkarin su ko kuma kamanta su da wani siffa na dan madam ko wani abu daban, llah madaukaki yace: " babu wani abu dayayi kama dashi, ya kasance me ji ne kuma me gani (11)"[75].
- Kadaita Allah cikin Allantakarsa, hakan ya kunshi kudurcewa wanda babu tabbas acikida cewa lallai Allah shine abun bauta na gaskiya babu wani abun bauta koma bayan sa ko kuma Allah bayan sa wanda ya cancanta a masa wani abu cikin bautansa, Allah madaukaki yace: " bamu aiki wani manzo ba gabanin ka face mun masa wahayi cewa babu abun bautawa da gaskiya sai ni kadai saboda haka ku bautamun (25)"[76] .
Sannan kuma ayyukan bawa da kalmomin sa su kance kamar yadda Allah ya shar'anta yana me neman yardan Allah da hakan shi kadai, Allah madaukaki yana cewa: " lallai wanda suke girman kai game da bautata zasu shiga jahannama suna makaskanta (60)"[77].
Ibada na nufin bawa ya tashi tsaye wurin aikata abunda Allah ya wajabta masa na wajibobin sallah wanda daga cikin amfanin ta shine tana kare mutum daga aikata alfasha da munanan aiki, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " lallai salla tana hana aikata alfasha da munanan aiki"[78].
Da kuma bayar da zakka wacce daga cikin amfanin a musulunci shine tana tsarkake mutum daga dattin rowa, Allah madaukaki yana cewa: "ka amshi zakka daga cikin dukiyoyin su wacce zata tsarkake su da wanke su"[79].
Da kuma azumi wanda shima amfanin shi a musulunci shine yana gadar da takwa da hana rai sha'awowinta, Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani an wajabta maku azumi kamar yadda aka wajabtama wanda suka gabace ku koda zaku samu takawa (183)"[80].
Da kuma aikin hajji wanda daga cikin hikimar ta shine abunda Allah ya bada labara dashi cikin fadin sa cewa: " domin su shaida amfanu a garesu kuma su ambaci sunan Allah acikin ranaku sanannu akan arzukin dayayi masu na dabbobin ni'ima, kuci daga garesu kuma ku ciyar sa masu bukata da talakawa (28)"[81].
Kasantuwar dukkanin ibada cikin musulunci sunzo ne gwargwadon ikin dan Adam wanda ba'a daura masa abunda bazai iyaba saboda kasancewa addinin ne me sauki, domin fadin allah madaukaki cewa: " Allah yana son ku da sauki baya son ku da wahala"[82].
Da kuma fadin sa manzon allah s.a.w cewa: "idan na umurce ku da wani aiki to ku aikata gwargwadon iyawar ku"[83]. Buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Amma wannan ibadun suna fadi acikin wasu haliye, misali:
- Sallah, daga cikin wajibobin ta shine yinta a tsaye idan mutum yana da ikon haka amma idan bazai iya yinta ba a tsaye sai yayita a zaune idan bazai iya yinta ba azaune shima sai yayi shi a kwance, idan hakan shima ya gagara sai yayishi da ishara watan nuni da gabbansa, kuma yana daga cikin wajibobinta har wayau yinta cikin jama'a a masallaci ga maza sai dai wannan wajabcin yana fadi akan mutum idan bashi da lafiya ko kuma halin tsoro ko sanyi da ruwan sama me tsanani, haka kuma sallah tana fadi akan mace me haila da jinin haihuwa ha sai tayi tsarki kuma babu ramako a akanta.
- Faduwar zakka akan mutumin da be mallaki yawan kudin da ake fitar masa da zakka ba, hasalima shi za'aba idan ya kasance talaka mabukaci.
- Faduwar azumi akan mara lafiya wanda ba'a sa ran warke wansa daga wannan ciwo sai yayi kaffara, amma mara lafiyan da ake sa ran warkewan sa daga wannan cuca zai rama azumin sa bayan ya warke, haka kuma azumi yana fadi akan mace me ciki idan taji tsoron halaka ko kuma halakan dan cikinta itama sai ta rama bayan ta haihu tayi lafiya, da kuma halaccin san azumi ga matafiyi saboda tafiya dalili cikin dalilai na wahala da kunci sai ya rama azumin da yasha a wasu lokuta na daban, haka kuma azumi ya fadi akan mace me al'ada ko kuma jijin haihuwa har sai tayi tsarki itma sai ta rama azumin da tasha bayan tayi tsarki.
- Faduwar aikin haji ga mutumin da bashi da kudi ko kuma ga kudin amma ba lafiya, amma idan yanada kudi bashi da lafiyar jiki ne sai ya wakilta wani yayi masa aikin hajin, shi kuma wanda bashi da duki hajji ya fadi akansa har sai ya samu kudin yin hajji wanda zayyi guziri dashi da kuma wanda zai barma iyalansa wanda suke karkashin ciyarwan sa har yadawa, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " Allah ya wajabtawa mutane ziyartan dakin sa ga wanda ya samu ikon haka"[84].
- Idan mutum yaji tsoron zai iya mutuwa ya halatta yaci ko yasha abun da Allah ya haramta ci da sha na naman alade da giya ko mushe ko kuma jini gwargwadon abun da zai rike masa ciki kada ya mutu, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " duk wanda yake cikin bukata lalura yasa yaci abunda aka haramta ci wanda bayaci bane dan son zuciya ko kuma ta'adi to babu zunubi akansa"[85].
Sayyid khudub Allah yayi masa rahama yace cikin tafsirin wannan aya " wannan itace ikida wacce ta dauki mutum a matsayin sa na mutum ba dabba ba, ko mala'ika ko shedan, dana dauki mutum tana me la'akari da dukkanin halinsa na rauni ko kuma karfi, da daukan sa a matsayi me gangan jii me hankali da matsayi da rai da kuma shauki, tana wajabta masa ayyuka wanda zai iya aikatawa sannan kuma tana la'akari wurin rubutama mutum lada ko kuma zunubin aikin da aka wajabta masa gwargwadon damar sa ba tare da tsananta mas aba ko kuma kuntatat masa….
Hakkokin manzon Allah s.a.w wacce take kunshe cikin Kalmar shahada wacce hakan yana wajabta abubuwa kamar haka:
- Yi masa biyayya cikin umurnin sa, Allah madaukaki yana cewa: " duk wanda yayima manzon Allah biyayya to hakika yayima Allah biyayya, duk kuma wanda ya juya baya bamu aikoka b aka zama ke kiyaye su (80)"[86].
- Gasgatashi cikin abunda ya bada labara, Allah madaukaki yana cewa: " baya Magana da son zuciyar sa (3) maganarsa wahayi ne cikin abunda ake masa wahayi (4)"[87].
- Nisantar abunda ya hana kuma ya tsawatar akansa, Allah madaukaki yana cewa: "duk abunda manzon Allah yazo maku dashi to ku rikeshi, kuma abunda ya haneku akansa ku hanu"[88].
- Kada a bautawa Allah sai da abunda ya koyar kuma ya karantar, manzon Allah s.a.w yana cewa: " duk wanda ya aikata wani aiki wanda baya cikin umurnin mu to an mayar masa da kayan sa baza'a amsa ba"[89].
Hakkokin Annabawa baki dayan su:
A cikin shari'ar musulunci mutum bazai zama musulmi ba har sai yayi imanai da dukkanin annabawa da manzannin Allah kuma ya so su da kuma girmama su tun daga kan annabi Adam amincin Allah ya kara tabbata agareshi har zuwa kan annabi Muhammad s.a.w, duk wanda be yi imani ba da daya daga cikin manzanni to wannan kafuri ne wanda hakan ya fitar dashi daga musulunci, Allah madaakaki yace: " lallai wanda suka kafurce da Allah da manzannin sa kuma sunanson rarrabewa tsakanin allah da manzannin sa suna cewa munyi imani da wasu manzannin mun kuma kafurce ma wasu, suna son riki tafarki a tsakanin haka (150) wa'ainnan sune kafirai na hakika kuma mun tanadar da azaba ta wulakanci ga kafirai (151)"[90].
Manzon muslunci yazo ne cikamakon Annabawa da manzanni, kuma shari'ar sa tazo ne domin cike shari'o'in da suka gabace shi daga Allah sannan kuma tana shafe dukkanin shari'on da suka gabace ta saboda kasancewar manzannin da suka gabata sun zo ne ga wasu bangare na mutane sabanin wannan manzon na musulunci wanda Allah ya aiko shi zuwa ga mutane baki daya har zuwa tashin alkiyama, Allah madaukaki yana cewa: " bamu aikeka ba face ga mutane baki daya a matsayin me bishsara da gargadi amma sai dai dayawa daga cikin mutane basu sani ba (28)"[91].
Saboda haka, musulmi an umurce shi da isar da sakon addinin musulunci da shari'arsa ga wanin sa, idan ya amsa wannan sako nasa madalla da hakan haka musulunci yake bukata idan kuma yaki amsa to hujja ta isar masa, Allah madaukaki yana cewa: " babu tilastawa cikin addini, tuni ashiriya ta bayyanu daga bata da rudu, duk wanda yayi imani da Allah kuma ya kafurce ma dagutu hakika yayi riko da wani igiya wacce bata katsewa, Allah ya kasance me ji ne kuma masani"[92].
Hakkokin iyaye (baba da mama):
Hakkokin iyaye ya kunshi yi masu biyayya da kuma rashin saba masu cikin dukkanin abunda sukayi umurni dashi matukar ba sabon Allah bane, da kuma kyautata masu, da daukan dawainiyar sun a laluran abinci da abun sha da tufafi da wurin zama, da sausauta murya wurin masu Magana, da Kankan dakai a garesu, da hakuri wurin yi masu hidima, da kuma lura da yayinsu kada kayi labarin da zai cucar dasu ko kuma ya tunzira su saboda Allah madaukaki ya hada hakkin sa da hakkin su, yace: " ubangijinka ya hukunta cewa kada abautawa kowa sais hi kadai sannan kuma iyaye a kyautata masu, idan daya daga cikin su yayi tsawon kwana tare dakai ko kuma su biyun dukan su kada kace masu uffan kada kuma ka tsawatar dasu da gujansu kuma ku fada masu Magana masu dadi da karamci (23) ku shinfida masu fuka fukanku na rahama ku kuma ce ya Allah kayi masu rahama kamar yadda sukamun rahama ina karami (24)"[93].
Da kuma fadin manzon Allah s.a.w cewa: " yardan Allah ga mutum yana cikin yardan iyayen sa, sannan kuma fushin Allah yana cikin fushin iyayen mutum"[94]. Hadisi ne in gantacce Tirmizi da ibn Hibban ne suka rawaito shi.
Wannan hakkoki na iyaye wajibi doka kuwa ba addinin ku day aba matukar basuyi umurni da sabon Allah ba, saboda hadisin Asma'u yar Abubakarr siddiq Allah ya kara masu yarda tace: mahaifiyata tazo wurina mun ziyara kuma mushrika ce a zamanin alakawarin kuraishawa da manzon Allah s.a.w, sai na tambayi manzon Allah s.a.w nace mai: ya manzon Allah mahaifiyata ta ziyar ce ni tana me son na ziyar ce ta nima shin zan iya kai mata ziyara? Sai yace: " eh ki ziyar ce ta"[95]. Nuhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Mahaifiya tana gaba da mahaifiya wurin biyayya da tausayi da ramgwame da sada zumunci, saboda hadisin Abu huraira cewa wani mutum yazo wurin manzon Allah s.a.w sai yace masa: wanene yafi hakki akaina cikin mutane da in kyautata masa? Sai yace mahaifiyar ka, har sau uku sai yace mahaifinka sai yan uwanka wanda suka fi kusa dakai haka sai wanda yake samanshi"[96]. Buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Manzon Allah ya kebance mahaifiya da hakkoki guda uku, sannan yakebe mahaifi da guda daya, anyi haka ne saboda mahaifiya itace wacce tadau cikin mutum cikin wahala da gajiya wanda mahaifi be dauka ba, kamar yadda Allah ya bada labara cikin fadin sa cewa: "mahaifiyar sa ta dauki cikinsa cikin wahala sannan kuma ta haifeshi cikin wahala"[97].
Hakkin miji akan matar shi:
- Na miji shine me daukan nauyin gidan sa kuma shine zai tashi da aikata duk wani da yake ganin shine maslaha ga iyalan sa, saboda fadin Allah madaukaki: " maza sune tsayayyu akan mata da abunda Allah ya daukaka sashin su dashi aka sashi da kuma abunda suke ciyarwa daga cikin dukiyarsu"[98].
Saboda a fiya yawan ci maza suna amfani da hankular su wurin tunkaran harkokin yau da gobe masu bijirow, saboda yawanci ranaunin yan tasiri wurin al'amuran su, amma hakan bayana nufin baza'a rikayin shawara bane dasu da amsan ra'ayin su cikin al'amarin daya shafi rayuwan su.
- Yi masa biyayya matukar ba sabon Allah bane, an karbo hadisi daga Zaid dan Arkam Allah yakara masa yarda yace: manzon Allah s.a.w yace bace bazata sauke hakkokin Allah ba dake kanta har sai ta sauke hakkokin mijinta baki dayan sa" hadisi ne ingantacce Dabari ne ya rawaito shi da isnadi me kyau.
- Kada ta rika daura masa abunda yafi karfin sa ko kuma ta rika neman abunda yafi karfin sa a wurin shi,
- Ta kiyaye masa dukiyar sa da yaransa da mutuncin sa, manzon Allah s.a.w yana cewa: " mafi alherin mace itace wacce kallonta ke faranta maka rai, kuma tana maka biyayya idan ka umurce ta, kuma tana kiyaye kanta da dukiyarka idan baka nan" dabarani ne ya rawaiti hi kuma albani ya ingantashi cikin littafin sahihul jami'u 3299.
- Kada ta rika fita daga gida sai da yardan sa da kuma sanin ta, kuma kada wanda baya so ya shigo masa gida, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " kunada hakki akan matan ku kuma suma sunada hakki akanku, hakkin ku akansu shine kada su shigo da wanda bakyaso gidan ku suyi fira, haka kuma kada su shigo da wanda bakwa so gidan ku, hakkin su kuma akanku shine ku kyautata masu wurin tufatar dasu da abinci"[99]. Sahihut tirmizi da ibn majjah.
Hakkokin mace akan mijinta:
- Sadaki wanda hakki ne na wajibiwanda miji zai ba mata, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " kuba mata sadakin su kyauta a garesu, idan sun tsammaku wani abu daga ciki to kuci hankalin ku kwance (4)"[100].
- Adalci da dai-daiko a tsakanin mata da wanke yake da mata biyu zuwa sama, ya wajaba agareshi da yayi a dalci a tsakanin su wurin basu abinci da abunsha da tufafi da wurin zama da kwana, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: duk wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ga dayan cikin su zai zo ranan alkiyama gefen jikin sa daya a tsanye"[101]. Hadisi ne ingantacce, Abu dawud ne da nasa'I da tirmizi da darami da ibn majjah suka rawaito shi.
- Ciyar da ita da yaranta da kuma bata kudin da ta bukata gwargwadon halin mutum, saboda fadin Allah madaukaki: " wa wadata ya ciyar dai dai wadatar sa, wanda kuma yake talaka ya ciyar gwargwadon halin sa, Allah baya daurawa rai wani nauyi sai abunda zata iya dauka"[102].
Domin musulunci ya zaburar da mutane da kwadaitar dasu akan ciyar da iyalan su sai ya sanya wannan ciyarwan a matsayin sadaka saboda fadin manzon Allah s.a.w ga Sa'ad dan Abi wakkas "…babu wata ciyarwa da zakayi wa iyalanka kana me neman ladan haka agun Allah face ya baka lada akanta harta loman abincin da matar ka zatasa a bakanta…."[103]. buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Mace tana da hakkin ta dauki abunda zai ishe ta ci da ita da yaranta cikin dukiyar sa ba tare da ya sani ba idan ya kasance me rowa baya basu abunda zai ishe su, saboda hadisin Hindu yar Ukubata tace ya manzon Allah: lallai abu sufyan mutum ne me rowa baya bani abunda zai isheni da yarana sai dai idan na dauka bada sanin sa ba, sai manzon Allah s.a.w yace mata: " ki rika daukan abunda zai isheki da yaranka amma kada kiyi barna ki kara akan haka"[104]. Buhari ne ya rawaito hadisin
- Kwana da kuma kyautata mata mu'amala, wannan yana daga cikin hakkoki masu muhimmanci wanda musulunci ya umjrci miji da aikata shi da kuma kiyaye shi, domin a matsayin ta na mata tana da bukatar wani zuciya wanda zai rika sauraranta da kuma tausaya mata, saboda haka wajibi ne miji ya rika wasa da matar say a kuma rika biya mata bukatar ta domin kareta daga aikata abubuwa marasa kyau, saboda fadin manzon Allah s.a.w ga Jabir: " kayi aure ne ya Jabir?" sai yace: eh nayi aure, sai yace masa: " budurwa ka aura ko bazawara?" sai yace: bazawara na aura, sai yace masa: " ai da budurwa ka aura ka rika mata wasa ita tana maka ko karika bata dariya itama tana baka"[105].
- Kiyaye mata sirrorinta da kuma boye aibinta, da kuma kiyaye abunda yake gani daga gareta da abunda yaji, da kuma kiyaye abunda suke aikatawa na alakar aure a tsakanin su, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " lallai daga cikin mafiya sharrin mutane a wurin Allah ranan alkiyama mutumin da zai sadu da matar sa sai yaje yana yadawa"[106]. Muslim ne ya rawaito hadisin.
- Yi masu mu'amala me kyau da zama dasu da kyakyawan hali da kuma kyautata masu da yin shawara dasu cikin al'amuran da yashafi rayuwan su, kada kullum ya rika zartar da ra'ayin sa ba tare da ya tuntubeta ba yaji shawaranta ta yarda zai tushe kafar soyayya da tausayin dak tsakanin su, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " mafi cikin imani cikin muminai shine wanda yafi su kyakyawan mu'amala sannan mafi fificin ku shine wanda yake mafifici wurin iyalin sa"[107]. Hadisi ne ingantacce Ibn hibban ne ya rawaito shi.
- Yin hakuri akan cucurwanta da kawar da ido akan dabi'unta marasa kyau, da kuma rashin bibiyan al'auranta, manzon Allah s.a.w yace: " kada mumini ya kyamaci mumina, idan ya kyamaci wani hali nata zai ga wani hali da yake so a tare da ita"[108]. Muslim ne ya rawaito hadisin.
- Kishi da killace ta, kada ya rika fita da ita wurin da akwai fasadi da sharri, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " yaku wanda sukayi imani ku tsamatar da kanku da iyalanku daga wuta, wacce makamashinta sune mutane da itace"[109].
- Kiyaye mata dukiyar mallakinta kada mutum ya rika daukan mata komai aciki sai da yardan ta sannan kuma kada mutum yayi amfani da komai a ciki sai da yardanta da saninta, manzon Allah s.a.w yace: " dukiya mutum musulmi baya halatta sai idan ya bayar da son ransa". Hadisi ne ingantacce, baihaqi ne ya rawaito shi cikin sahihul jami'u 7662.
Hakkokin yara:
- Hakkokin yara ya kunshi kiyaye rayuwan su da kuma himmatuwa da al'amuransu da tsayin daka akan tarbiyyar su da dauke nauyin abubuwan da suke bukata na abinci da abun sha da tufafi da wurin zama, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " ya ishi mutum zunubi ya tuzarta wanda yake ciyarwa"[110]. Sahihu muslim.
- Zaba masu suna masu kyau wanda zai dace dasu, hakika an rawaito hadisi daga manzon Allah s.a.w yace: "lallai za'a kiraku da sunayen ku da iyayen ku ranan alkiyama saboda haka ku kyautata sunayen ku"[111].
- Karantar dasu da cusa masu halaye na gari cikin zukatansu kamar kunya da girmama manya da makwabta da fadin gaskiya da rikon amana da yima iyaye biyayya… da sauran su, da kuma nesantar dasu daga munanan maga da ayyuka kamar karya da ha'inci da yaudara da zamba da sata da cucar da iyaye… da sauran su, manzon Allah s.a.w yace: "lallai Allah madaukaki zai tambayi kowa akan kiwon daya bashi shin ya kiyaye haka ko kuma yaci amana? Har akan iyayen gidan mutum sai amtambaye shi" Ibn hibban ne ya rawaito hadisin cikin alsahiha 1636.
- Karantar dasu ilimi me amfani da basu tarbiyya ta gari da zaba masu abokanai masu hali na gari, manzon Allah s.a.w yace: " dukkan ku masu makiwata ne kuma za'a tambayeku akan abun kiwon ku, shugaba za'a tambayeshi akan mutanen sa, Uba me kiwo makiwaci ne akan mutanen gidan sa kuma za'a tambaye shi akan su, mace me kiwo ce a gidan mijin ta kuma za'a tambayeta akan haka, me kasuwanci da kudin me gidan sa shima makiwaci ci kuma za'a tambayeshi akan haka"[112]. Buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
- Sa ido akan lafiyar su da ci gaban su ta hanyar rashin yi masu addu'ar banza akan su, manzon Allah s.a.w yace: " kada ku rika yima kanku munanan addu'a kuma kada ku rika yinta akan yaranku ko kuma dukiyoyin ku, saboda kada ku dace da sa'ar da Allah yake amsar addu'o'I sai ya amsa maku wannan addu'ar taku munana"[113]. Hadisi ne ingantacce.
- Yin adalci a tsakanin su da rashin fifita wani akan sauran wurin bada kyauta ko kuma mu'amala ta tausayi, domin rashin yin adalci atsakanin yara yana haifar da kiyayya da gaba a tsakanin su, an karbo hadisi daga Nu'umanu dan Bashir Allah ya kara masu yarda yace: mahaifina ya bani kyauta wani abu cikin dukiyar sa sai mahaifiyata Amratu yar Rawaha tace bata yarda ba har sai yaje ya shaidawa manzon Allah s.a.w wannan kyauta dayamun, sai ya tafi wurin manzon Allah s.a.w ya shaida masa sai yace mashi: " shin kaba yaranka dukan su irin wannan kyauta?" sai yace: a'a ban basu ba, sai manzon Allah s.a.w yace: " kaji tsoron Allah kuyi adalci a tsakanin yaranku sai mahaifina ya dawo gida ya kwace wannan kyauta dayamun"[114]. Hadisi ne ingantacce.
Hakkokin yan uwa(dangi):
Sune iyalan mutum da yan uwansa danginsa, musulunci ya kwadaitar da arika sadar masu da zumunci da kuma kyautata masu da kudi idan yana da hali ya rika biya masu bukatun su cikin zakkar san a wajibi da kuma sadaka na nafila, ya kuma rika tambayan halayen su ta kyautata masu mu'amala da kuma yin tarayya dasu cikin bakin ciki idan abun bakin ciki ya same su ko kuma taya su murna idan abun murna ya same su, Allah madaukaki yace: " kuji tsoron Allah wanda kuke rokin sa bukatun ku da sadar da zumunci domin sa"[115].
Hakika musulunci ya umurci mutum daya rika sadar da zumunci koda kuwa sun yake masa, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " baya cikin sadar zumunci mutumin da idan an zo mashi shima sai yaje idan kuma ba'azo mashi ba shima bazai je ba, sada zumunci shine wanda yake sadarwa koda kuma an yanke masa"[116]. Buhari ne ya rawaito shi.
Sannan kuma musulunci yayi tsawatar wa sosai akan yake yanke zumunci da rashin sadar da ita ya sanya aikata hakan cikin manyan laifuka, manzon Allah s.a.w yace: " Allah ya halicci dan adm bayan yagama sai ya zumunci ta nema alfarma agun Allah sai yace ma dan adam ka kiyaye yanke zumunci, shin baka yard aba ace ka sadar da zumunci ga mutumin daya yake sadar maka da wanda ya yanke maka ba? Sai yace na yarda ya ubangiji na, sai yace to wannan naka ne" sai abu huraira yakaranta ayar da Allah yake cewa acikin ta (yaya kuke zato idan kun juya baya zaku rika barna abayan kasa da kuma yanke zumuncin ku, wa'innan sune wanda Allah ya tsine masu ya kurmantar dasu ya kuma makantar da ganin su)[117].buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Hakkokin shuwagabanni akan mabiyan su:
- Yi masu da'a da biyayya cikin abunda suka bada umurni matukar ba sabon Allah bane, Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani kuyi ma Allah biyayya kuma kuyima manzon Allah biyayya da shuwagabannin ku"[118].
- Yi masu nasiha ta lalama da amfani da kalamai masu dadi da ladabi da sauki da kuma rashin ha'intar su ta hanyar nuna masu abun da zai amfanar dasu ya amfanar da mutanen su, kuji abunda Allah ubangijin mu ya fadama musa da dan uwansa Harun a lokacin da zai aikesu zuwa ga fir'auna domin su isar masa da kira: " ku fada masa Magana masu sanyi koda zai tuna kuma yaji tsoron Allah (44)"[119].
- Goya masu baya a lokacin wahala da annoba da rashi da kuma rashin masu fito na fito da juya masu baya da rashin taimakon su koda kuwa yana cikin bangaren da mutum baya so, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " duk wanda yazo maku yana neman ya rarraba maku kawunan to ku kasha shi"[120]. Hadisi ne in gantacce.
Hakkokin mabiya akan shuwagabannin su:
Daga cikin hakkokin mabiya akan shuwagabannin su akwai abubuw akamar haka:
- Yin adalci a tsakanin su daba duk me hakki hakkin sa, wajibi ne yin adalci a tsakanin su cikin hakkoki wajibai da yin adalci wurin rabon mukamai a tsakanin su, da kuma adalci a tsakanin su wurin hukunci, dukansu daya suke a gaban ka babu wani wanda yafi wani matsayi ko kuma fifita wata jama'a akan wata, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " lallai mutumin daya fi kowa azaba a ranan alkiyama shine Azzalumin shugaba". Dabarani ne ya rawaito shi cikin littafin ausat, da kuma dayalisi cikin sahihul jami'u 1001.
- Rashin zalumta da ha'inci da yaudaran mutanen sa, manzon Allah s.a.w yace: "babu wani bawa wanda Allah zai bashi sguhabancin mutane yam utu yana ha'intar wannan nauyi da aka daura masa face Allah ya haramta masa shiga Aljanna"[121]. Buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
- Yin shawara dasu cikin al'amuran da suka shafi maslahar siyasar suda zaman takewar su da tattalin arzikin su cikin abunda babu nassi akansa da kuma basu dama da cikakken yanci na bayar da shawarwarin su da tunanin su akan haka, da kuma amsar wannan ra'ayoyi nasu idan ya bayyana cewa akwai maslaha kasa baki daya acikin sa, Allah madaukaki yace: "badan tausayin Allah da yasa maka ba kake nuna masu, da ka kasance me tsatsauran hali a garesu da basu taru maka ba, ka rika masu afuwa da nema masu gafara da neman shawarwarin su cikin al'amura"[122].
- Ya kasance yana masu amfani da shari'ar Allah wurin yi masu hukunci da kundun tsarin mulkin kasa.
- Kada ya rika boyewa mutanen sa wanda yake mulka da kuma rufe masu kofar ganawa da girman kai da canza masu fuska da sanya wani me shiga tsakanin ka da su, wanda sai sunga dama su bar wani ya gana dakai, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " duk wanda aka bashi shugabancin wani abu na al'amarin mutane sai ya sanya Katanga tsakanin shi dasu baya sauraran wani bukatar su da da latakawan su, shima Allah zai sa Katanga atsakanin sa dashi ranan alkiyama akan bukatunsa"[123]. Hadisi ne ingantacce cikin littfain sahiha 629.
- Tausayin mutanen sa da kuma rashin daura masu abun da bazasu iya ba ko kuma kuntata masu cikin rayuwan su, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " ya Allah duk wand aka bashi shugabancin al'ummata sai ya kuntata masu shima ka kuntata mashi, wanda kuma ka bashi shugabanci yaji tausayin mutanen sa shim aka tausaya mashi"[124]. Hadisi ne in gantacce.
Hakkin makwabta:
Musulunci yayi umurni da kyautata ma makwabta matuka, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " ku bauta wa Allah shi kadai kada kuyi masa tarayya da wani sannan kuma ku kyautatawa iyaye da yan uwan ku da marayu da miskinai da makwabci dan uwa da makwabci na zamantakewa da aboki na kusa da matafiyi da abun da kuka mallaka na bayi, lallai Allah bayason me yawan rowa kuma da alfahari (36)"[125].
Sannan kuma musulunci ya haramta cucar da makwabci da Magana ko kuma aiki, an karbo hadisi daga abu huraira Allah yakara masa yarda yace: ance ma manzon Allah s.a.w: wata mata tana sallar dare da azumtar rana amma kuma tana cucar da makwabtan ta da harshenta sai yace: " babu alheri a tattare da ita tana cikin wuta" sai akace masa kuma: wata mata tana sallolin ta na farilla guda biyar kullum da azumtar watam Ramadan sannan kuma tana sadaka da abunda ya sawwakan mata na madara bushashe amma kuma bata cucar da kowa da harshen ta sai yace: " tana cikin aljanna"[126]. Hadisi ne ingantacce, buhari ne ya rawaito shi cikin littfin adabul mufrad (190).
Sannan har wayau musulunci yaba makwabci matsayi me girma da hakki babba cikin fadin manzon Allah s.a.w cewa: " mala'ika JIbril be gushe ba yana mun wasiyya game da makawabci har sai da nayi tsammanin za'a bashi gadon makwabcin sa"[127]. Buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Sannan muslunci ya irga cucar da makwabci cikin ayyukan da suke kore imanin mutum, manzon Allah s.a.w yana cewa: " na rantse beyi imani ba, na rantse beyi imani ba" sai aka ce masa wanenen wannan ya manzon Allah? Sai yace: " wanda makwabcin sa be amince mas aba akan sharrin sa". Buhari da muslim ne suka rawaito shi.
Kamar yadda ya dace jurewa cutarwan sa da kuma yi masa lalama, an karbo hadisi daga abu huraira Allah yakara masa yarda yace: wani mutum yazo gun manzon Allah s.a.w yace masa: ya manzon Allah makwabcina na cutar dani, sai yace masa: "jeka ka fito da kayan gidanka ka zuba akan hanya" sai wannan mutumi ya tafi ya fito da kayansa kan hanya sai mutane suka ganshi suke tambayansa meke faruwa haka? Sai yace masu: makwabcina ne yake cutar dani sai na fadama manzon Allah s.a.w yacemun nazo nafito da kayana kan hanya, sai mutane suka rika cewa: " ya Allah ka tsinewa wane, ka tozarta shi", sai wannan abu ya isa zuwa ga wannan makwabci sai yazo gun wannan makwabcin nasa da yake cutarwa yace masa: kayi hakuri ka komar da kayanka cikin gidan ka wallahi bazan kara cutar dakai ba. Hadisi ne in gantacce cikin littafin adabyl mufrad.
Makwabci yanada hakkoki koda kuwa bayahude ne ba musulmi ba, ga Abdullahi nan dan Amru wanda aka yanka masa akuya ta tarban sa bayan ya dawo daga tafiya, lokacin da aka kawo masa wannan nama sai yace ku kaima makwabcina bayahuden nan domin naji manzzon Allah s.a.w yana cewa: " mala'ika Jibril be gushe ba yana mun wasiyya game da makwabci sai da nayi tsammanin za'a bashi gadon makwabcinsa idan yam utu". Buhari da muslim ne suka rawaito shi.
Hakkin abokai:
Musulunci ya kwadaitar da mutum ya himmatu da abokanan sa sannan kuma ya sanya hakkoki na abota wanda dole ne aboki ya kiyaye su na umurtan sa da aikata kyakyawan aiki da kum ayi masa nasiha, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " mafiya alheri aboki agun Allah shine wanda yafi alheri agun abokin sa, sanna kuma mafi alheri makwabci agun Allah shine wanda yafi alheri agun makwabtan sa" hadisi ne ingantacce, Tirmizi ne ya rawaito shi cikin littafin alsahha 103.
Hakkin bako:
Daga cikin bako a musulunci shine a karrama shi, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " duk wanda yayi imani da Allah da ranan alkiyama to ya karrama makwabcin sa, sannan kuma duk wanda yayi imani da Allah da ranan alkiyama ya karrama bakon sa cikin ranakun bakunta sa" sai suka ce yaushe ne ranakun bakuntan sa sai yace dare da rana, bakunta kwana uku ne duk abunda ya karu akan haka to sadaka ne yi masa hidima, kuma duk wanda yayi imani da Allah da ranan alkiyama ya fadi alheri ko kuma yayi shiru". Buhari da muslim ne suka rawaito shi.
Karrama bako yana cikin manyan ayyukan lada, manzon Allah s.a.w yace: " cikin mutane babu kamar mutumin da zai fita da dokin sa domin jihadi dan daukaka Kalmar Allah, kuma yana nesantar ashararan mutane, da kuma mutumin da yake karrama bakon sa wanda yake masa hidima a matsayin san a bako yana me bashi hakkin sa" hadisi ne ingantacce, Imam Ahmad da hakim ne suka rawaito shi.
Kamar yadda ya wajaba akan bako da lura da halin wanda ya sauka a wurin sa kada ya daura masa abunda bazai iya ba, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " baya halatta ga musulmi ya sauka wurin dan uwan sa bakunta ya wuce kwana uku har sai yasa shi aikata zunubi".
Hakkokin miskinai da talakawa:
Allah madaukaki ya yabi masu ciyarwa dan neman yardan sa wanda suke kai koma wurin biyan bukatar mutane miskinai da talakawa da mabukata cikin fadin sa: " a cikin dukiyarsu suna cire hakkokin masu tambayar su da wanda basa tambayar su (19)"[128].
Musulunci be tsaya nan ba sai da ya irga sadakar da mutum ke bawa yan uwansa talakawa cikin ayyukan lada masu kusantar da mutum ga Allah, Allah madaukaki yace: " ba muslunci bane kawai ku kallai alkibla kuna sallah, musulunci shine wanda yayi imani da Allah da ranan karshe da mala'iku da littattafai da manzanni kuma yaba da sadakar kudi da son ransa gay an uwansa da marayu da miskinai da matafiyi da masu neman taimako……."[129].
Sanann kuma anyi alkawari azaba me tsanani ranan alkiyama ga mutanen da suke boye dukiya su tara basa bayar da hakkin Allah aciki, Allah madaukaki yana cewa: " wanda suke tara dukiya na zina da azurfa basa ciyar dashi ga hanyar Allah, to kuyi masu bishara da azaba me radadi (43)"[130].
Saboda haka ne aka wajabta bayar da zakkah a cikin muslunci sannan kuma aka sanya ta cikin ginshikan na wajibi akan ko wani musulmi wanda ya mallaki kudin daya kai zakkah sannan kuma yakai shekara yana juya su ko a ajiye, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " bamu umurce su da komai ba sai su bautawa ubangijin su suna masu tsarkake shi da ibada da masu mika wuya suna tsaida salla da bayar da zakkah, wannan shine addini mikakke (5)" suratul bayyinah
Sannan kuma Allah kadansa yayi bayanin wanda suka cancanci cin wannan zakkah yace: "lallai zakkah anabawa fakirai ne da miskinai da masu aikin tarata da wanda ake lallashin zuciyar su da bawanda zai fanshi kansa da wanda ya daukan ma kansa wani kudi domin raba fada tsakanin mutum biyu da masu jihadi dan daukaka Kalmar Allah da matafiyi, wajibi ne daga Allah, Allah ya kasance masani me hikima (60)"[131].
Kuma hakika tsoratarwa yazo ga duk wanda suka hana zakkah cikin fadin Allah madaukaki: "kada wanda suke rowa da dukiyar da Allah ya basu cikin falalar su suyi tsammanin haka shine alheri a garesu, hakan sharri ne akansu da sannu za'a da abunda suke rowa dashi ranan alkiyama"[132].
Hakkoki a bangaren aiki:
Ta bangaren aiki da ma'aikata musulunci ya tsara dokoki wanda suke gyra alaka tsakanin me kamfani da ma'aikatansa domin yaba kowa hakkin say a kuma sanya alakar dake tsakanin su ta koma alaka ce ta yan uwantaka da soyayya ba alaka ba ne na kudi da maslahar juna ba kawai.
Hakkokin ma'aikata:
Musulunci yayi umurni da kasancewar alaka tsakanin ma'aikata da me kamfani ya zama alaka ce ta yan uwantaka da wanda zata dace da hakkin dan adam, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " lallai ma'aikatan ku yan uwanku ne Allah yasanya su a karkashin ku, dan haka duk wanda yake da wani ma'aikaci a karkashin sa to ya rika ciyar dashi irin abincin daya ci ya kuma tufatar dashi irin tufar daya sa kuma kada ya rika sashi aikin daya fi karfin sa, idan ya sanya shi aikin daya fi karfin sa to ya tayashi"[133]. Sahihul buhari.
Sannan musulunci ya tabbatar da hakkin ma'aikaci na biyansa ladan aikin sa, manzon Allah s.a.w yace: " Allah yace: mutune uku zanyi shari'a dasu ranan alkiyama, mutumin daya yayi alkawari da rantsuwa da sunana kuma yayi saba alkawarin, da mutumin daya siyar da mutum me yanci yacinye kudin, da mutumin daya dau hayan dan aiki ya hanashi ladan aikin sa". Buhari ne ya rawaito shi.
Musulunci yayi umurni da biyan ma'aikaci ladan aikin sa nan take bada bata lokaci ba da zaran ya gama aikin sa, manzon Allah s.a.w yace: "kuba ma'aikaci ladan aikin sa kafin gumin sa ya bushe"[134].
Kamar kuma yadda yayi umurni da kada a daura masa aikin da bazai iyaba, idan kuwa aka sanyashi aikin daya fi karfin sa to dole ne a taimaka masa imam dai akara masa ladan aikin sa ko kuma a tayashi da jiki, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: "…. Kada ku sanya su aikin da yafi karfin sui dan kuma kun sanya su to ku tayasu". Sahihul buhari.
Hakkokin me kamfani ko me aika:
Kamar yadda musulunci ya nemi me kamfani daya kiyaye hakkokin ma'aikatansa haka suma ma'aikatan ya umurce su da su kiyaye hakkokin me kamfani ko kuma wanda suke ma aiki, ta hanyar yi masa aikin yadda ya kamata ba tare da yi masa cuge ba ko kuma latin zuwa wurin aiki wanda zai cutar da me aikin ko kamfani, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " lallai Allah yanason idan dayan ku zayyi aiki ya inganta aikin sa" sahihul jami'u 1880.
Saboda ya kwadaitar da ma'aikata inganta aikin su dayin aiki dakyau da kuma kiyaye karamar su da martaban su ya sanya aikin su ya zama mafi alherin hanyar samun halal idan sun ingantashi kuma suka sa ikhlasi aciki, manzon Allah s.a.w yace: " mafi alherin aikin samun kudi shine aikin hannu idan mutum ya ingantashi ya kuma kiyaye ha'inci a cikin sa" sahihul jami'u 3283.
Hakkokin sauran halittu na dabbobi da sauran su:
Musulunci be takaitu ba kawai akan liyaye hakkokin dan adam ba kadai ba hatta dabbobi ya basu hakkokin su wanda duk wanda toye masu hakkoki zai iya kai mutum ga shiga wuta, daga cikin hakkikin akwai:
Hakkin dabbobi:
Hakkin dabba ne abata abinci da kuma kada a zabtar da ita da yunwa da kishin ruwa har ta mutu da haka, Manzon Allah s.a.w yana cewa: " an azabtar da wata mata akan wata mage da ta kulleta ta hanata abinci da ruwa tar ta mutu, wanda hakan ya shigar da ita wuta saboda ta hanata abinci sannan ta kulle ta bata barta tafita ba bare ta ci abinci fari a waje". Buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
- Kyautata masu da rashin azabtar dasu ko kuma cutar dasu da sanya su aikin daya fi karfin su, hakika manzon Allah s.a.w ya wuce wani jaki wanda aka daura mawa kaya wanda ya dankwafar dashi saboda nauyi sai yace: " kuji tsoron Allah game da dabbobin ku wanda basa Magana, ku rika daura masu kaya dai dai gwargwado kuma ku rika ciyar dasu dai dai gwargwado" hadisi ne in gantacce, Ahmad ne ya rawaito shi.
- Kada arika yin wasa dashi wanda zai azabtar dashi, saboda hadisin da aka rawaito daga Abdullahi dan Umar Allah ya kara masu yarda cewa ya wuce wasu matasa guda biyu na kuraishawa sun daure wani tsuntsu suna jefansa, sai yace: duk wanda ya aikata haka Allah ya tsine masa, lallai manzon Allah s.a.w ya tsine ma wanda ya cutar da wani abu me rai da gangan"[135]. Buhari da muslim ne suka rawaito shi.
- Rashin sassa[136]
- Kada a rika tsoratar dasu ko kuma cutar dasu, mun kasance tare da manzon Allah s.a.w a cikin tafiya sai yaje biyan bukatar sa sai muka ga wani tsuntsu da jaririnta sai muka dau jaririn muka bar uwar da manzon Allah s.a.w yadawo yaga jaririn tsuntsu yace: " wanene ya rabo wannan yaron tsuntsun da uwar sa? Ya mayar dashi gun uwar sa" sannan kuma mukaga ramin tururuwa a ramin su muka kona su sai yace mana: "wanene ya kona wannan" sai mukace mune, sai yace baya halatta da wani yayi azaba da wuta sai ubangijin wuta kadai" abu dawud ne ya rawaito hadisin cikin sahihul adabul mufrad 295.
- Musulunci yayi umurni da yanka dabba idan anason amfani da ita saboda a hutar da ita, kuma ya wajabta a wasa abun yanka kuma kada a yanta dabba a gaban yan uwanta suna kallo ko kuma a karya mata wuya ko kuma a gasata kafin ta mutu, manzon Allah s.a.w yana cewa: " lallai Allah yayi umurni da kyautatwa komai, idan zakuyi kisa to ko kyautata kisan, idan kuma zaku yanka dabbo ku kyautata yankan, ku wasa abun yankan ku domin ku hutar da dabba" muslim ne ya rawaiti shi.
Sannan musulunci yayi umurni da akashe dabbobi wanda suke cutar da dan adam saboda a kare rayuwansa wanda yafi na dabban muhimmanci a wurin Allah.
Idan musulunci yaba dabbobi irin wannan hakkoki yaya kake tsammanin mutum wanda Allah ya daukaka shi akan dukkanin halittun say a kuma karramashi, Allah madaukaki yace: " hakaika mun karrama dan adam sannan kuma muka sanya shi abayan kasa sa cikin ruwa, kuma muka azurta shi daga dadaden abubuwa muka kuma daukakashi akan halittun mu daukaka (70)"[137].
Ya sanya tausayi da rahama ga dabbobi amatsayin hanyar samun gafara da shiga aljanna, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " lokacin da wani mutum yake dafiya sai kishi ruwa ya dame shi akan hanyar sa sai ya samu wata rijiya ya tsaya ya dibo ruwa yasha y agama kenan zai tafi sai yaga wani kare yana cin kasa alamun yana bukatar rruwa sai wannan mutumi yace:Allah sarki shima irin kishin daya koro ni shi ya koro shi sai ya koma rijiyan ya debo masa ruwa a cikin takalmin sa ya bashi yasha sai Allah ya gode masa ya gafarta masa, sai suka ce ya manzon Allah yanzu muna da lada akan dabbobin mu? Sai yace eh kunada shi cikin dukkanin wani hanta me rai idan kuka rayashi kunada lada" buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Hakkin bishiyoyi da shukoki:
Muslunci ya halatta amfani da yayan bishiya domin ci amma kuma ya hana cira badan ci ba ko kuma barna kawai badan amfanin mutum ba, yayi umurni da kiyaye su da kuma sanya gasa wurin shukata da yawaitata, saboda fadin manzo Allah s.a.w: " da ace alkiyama zata tashi a kwai bishiyar dabino karama a hannun dayan, idan har ya samu damar shuka ta yayi maza maza ya shuka kafin alkiyamar ta tashi" buhari ne ya rawaito shi cikin adabul mufrad.
Sannan kuma kuma ya irga shuka da dasa bishiyoyi masu amfani a cikin ayyukan sadaka wanda ake ba musulmi lada akan haka, manzon Allah s.a.w yace: " babu wani mutum musulmi da zai shuka wata bishi ko kuma kayan tsirrai sai wani tsuntsu ko mutum ko dabba taci wannan shuka nashi face Allah ya rubuta masa ladan sadaka akan haka" muslim ne ya rawaito shi.
Hakkin hanya dana kasuwanni:
Musulunci ya sanya hakki ga kasuwanni da hanyoyi, manzon Allah s.a.w yace: " kashedin ku da zama akan hanya, sai sukace ya manzon Allah bamu da wurin zama wanda muke fira sai anan! Sai manzon Allah s.a.w yace: "idan kunki dole sai kun zauna akan hanya to ku rika bashi hakkin sa" sai sukace: menene hakkin hanya ya manzon Allah? Sai yace: " hakkin hanya shine ku rufe idon ku daga kalle kallen banza, da kuma kame bakinku akan cutar da mutane, da kuma mayar da sallama, dayin umurni da kyakyawan aiki, da kuma yin hani da mummunan aiki". Buhari da muslim ne suka rawaito shi.
- Kawar da wani abun da zai cutar da matafiya akan hanya, manzon Allah s.a.w yace: " imani kaso ne saba'in da da tara ko kuma sittin da tara, mafi kololuwan su shine, mutum yace la'ilaha illah, sannan mafi karancin su shine kawar da abun cutarwa akan hanya, sannan kunya wata kaso ne cikin imani". Buhari da muslim ne suka rawaito shi.
- Musulunci ya haramta lalata hanyoyi da kasuwanni da wani abunda mutum ke kyama na datti ko kazanta, manzon Allah s.a.w yace: " tsinanne ne" sai suka ce wanene wannan tsinannen ya manzon Allah? Sai yace " duk wanda yake bayan gida akan hanyar mutane ko kuma inuwar su na hutawa" muslim ne da abu dawud suka rawaito shi.
Wannan hakkoki idan ba'a samu wani karfin ido ba wanda zai rika sa ido akai ta tabbatar da mutane sun kiyaye su zai zama kamar misali ne kawai saboda acikin mutane akwa wanda lalama baya masa sai an sa masa karfi, manzon Allah s.a.w yana cewa: "na rantse da wanda raina ke hannun sa, immadai ku rika umurnin junanka da aikata kyakyawan aiki da hana juna aikata mummunan aiki ko kuma Allah na gab da ya aiko maku da azaba daga gareshi sannan kuma kuta addu'a baza'a amsa maku ba" Ahmad ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi cikin littafin sahihul targib wattarhib 2313.
Amma cikin abunda ya shafi hakkokin gama garin mutane wanda muslunci ya wajabta ma kowa:
Hakika musulunci ya wajabtawa ko wani musulmi damuwa da halin yan uwansa duk inda suke, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " zakaga muminai cikin zaman takewarsu suna masu tausayin juna da son juna da taimakon juna, kmar misalin gangan jiki ne wanda idan wani gaba daya yana ciyo sai kaga duka gangan jikin ya amsa zazzabi shima da radadi".
Sannan kuma musulunci yayi umurni da kyautatawa muslumi ta inganta halinsa, manzon Allah s.a.w yace: "imanin dayan ku baya cika har sai ya soma dan uwansa abunda yake soma kansa". Buhari da muslim ne suka rawaito shi.
Da kuma jimami tare dasu a zamanin rashin lafiya da annoba, manzon Allah s.a.w yana cewa: "misalin mumin da mumini kamar gini ne wanda sashi yake karfafa sashi sai ya kama yatsunsa na hannu ya kulle". Buhari da muslim ne suka rawaito shi.
Sannan kuma yayi umurni da taimakon sa idan ya bukaci haka, Allah madaukaki yace: "idan suka nemi taimakon ku cikin addini ya zama wajibi ku taimaka masu sai dai idan akwai alkawari ne na zaman lafiya tsakanin ku da mutanen da suka nemi taimakon su akan yakar su, Allah ya kasance me ganin abun da muke aikatawa (72)"[138].
Sannan kuma muslunci ya hana kaskantar da musulmi, manzon Allajh s.a.w yace: " babu wani mutum musulmi wanda zai kaskantar da musulmi a wani wuri wanda zai ci mutuncin sa da kuma rage masa kima face shima Allah ya kaskanta shi a wani wuri wanda yake son taimako, sannan kuma babu wani mutum musulmi wanda zai taimaki musulmi a wani wuri wanda mutuncin sa da darajar sa zai zube face shima Allah ya taimake shi a wani wurin da yake bukatan taimaka" Ahmad da Abu dawud ne suka rawaito shi, sannan malam albani yace hadisi ne hasan duka hadisi me lamba 5690 cikin littafin sahihul jami'u.
Saboda kiyaye hakkokin mutum cikin al'ummar musulmai ne yasa Allah ya aiko ma manzannin sa dokoki wanda suka kunshi umurni da hani wanda zasu kiyaye wannan hakkoki na mutum da bashi kariya ta yadda baza'a mai ta'adi ba sannan kuma ya sanya hokunce hukunce masu tsauri akan haka anan duniya wanda akafi sani da suna iyakoki (Haddi) cikin musulunci ko kuma azaba a lahira, daga cikin wannan dokoki na umurni da hani akwai:
- Musulunci ya hana yin amfani da kujeran mulki da karfin iko domin samun wani amfani na mutum shi kadai, sanan yaba shugaba iko na kwace irin wannan dukiya da aka tara ta wannan hanya ya mayar da ita cikin baitul mali na musulmai, hakika manzon Allah s.a.w ya aiki wani mutum wanda ake kira da suna dan latabiyya da ya amso masa zakka a wurin wasu mutane, daya dawo sai yace ma manzon Allah: wannan shine kudin kun a zakkah wannan kuma kyauta ce suka bani, sai manzon Allah s.a.w yace masa: " me yasa be zauna ba agidan ubanshi ko uwarsa yagani idan zasu bashi wannan kyauta?! Na rantse da wanda raina ke hannun sa dayan ku bazai amshi wani kyauta ba da aka bashi sanadiyyar mukamin sa ko kuma wani aikin da aka daurashi akai face yazo da wannan abu ranan alkiyama yana daure dashi akansa sannan ya daga kowa yagani, ya Allah ka shaida na isar masu da sakon ka". Buhari da muslim ne suka rawaito shi.
- Musulunci ya haramta cutar wa da hannu kamar amsar haraji wanda ya wuce kima da makamantan haka ko kuma cutarwa da harshe kamar gulma da annamimin ci da bayar da shedar karya ko zagi, Allah madaukaki yace: " wanda suke cutar da muminai maza da mata da wani abunda basu aikata ba hakika sun daukan ma kawunan su babban kaya da zunubi bayyananne"[139].
- Musulunci ya haramta ta'adi akan mutuncin mutane da bin diddgin akai, Allah madaukaki yace: " kada ju rika binciken aibin junan ku" suratul hujurat ayata 12.
Allah madaukaki ya kara cewa kuma: "yaku wanda sukayi imani kada ku rika shiga gidajen junanku har sai sunyi salla da neman izini daga mutanen gidan, hakan shi yafi dacewa da zama alheri a gareku koda zakuyi tunani (27) idan kuka samu wani a gidan kada ku shiga har sai an baku izinin shiga idan kuma akace ku koma to ku koma hakan shi yafi zama tsarki a gareku, Allah ya masani ne akan abunda kuke aikatawa (28)"[140].
- Musulunci ya haramta zalumci baki dayan sa, zamuntar mutane ko kuma zalumtan kai, saboda fadin Allah madaukaki: " lallai Allah yana umurtanku da adalci da kyautatawa da bayar da sadaka ga yan uwa sannan kuma yana hani game da alfasha da mummunan aiki da zalunci akan mutane da haka yake maku wa'azi koda zakuyi tunani (90) ku cika alkawuran Allah idan kun dauka sannan kuma kada ku rika warware alkawari bayan kun sanya Allah ya zama wakili a tsakanin akan haka, lallai Allah yana sane da abunda kuke aikatawa(91)"[141].
Allah kuma yana cewa cikin hadisul kudsi: " yaku bayi na lallai na haramtawa kai na zalunci saboda haka kuma na haramta zalunci a tsakanin ku kada ku rika zalumtar juna…" muslim ne ya rawaito shi.
Hatta zalumtar mutumin da ba akidar ku day aba ko addini musulunci ya haramta haka sannan kuma yayi umurni da arika kyautata masu, Allah madaukaki yace: " Allah baya hanaku adalci da kyautatawa ga mutanen da basu yake ku ba cikin addini sannan kuma basu fitar daku ba daga cikin gidajen ku, lallai Allah yanason masu adalci (8)"[142].
- Musulunci ya hana zagin addini wasu da ibadunsu da allolin su saboda hakan yana haifar da zage zage tsakanin bangarori biyu da kuma haifar da kiyayya da gaba wanda zai hana mutum gane gaskiya, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " kada ku zagi abubuwan da suke bautama sa koma bayan Allah sais u zagi Allah suma saboda kiyayya da rashin sani"[143].
Sannan kuma ya sanya dokoki da ka'idoji na tattaunawa da mutanen da ba addinin ku day aba ko kuma akida wanda hakan zai sa su gane gaskiya, Allah madaukaki yace: " kace yaku ma'abota littafi ku zo mu hadu akan wata kalma tsakanin mu daku cewa bazamu bautawa kowa ba sai Allah sannan kuma bazamu mashi tarayya ba da wani cikin bauta, kuma sashin mu bazasu riki sashi ba alloli koma bayan Allah, idan sun juya baya kuce mun shaida mu musulmai ne (64)"[144].
- Muslunci ya haramta fasadi baki dayan sa, Allah madaukaki yace: " kada kuyi barna a doron kasa bayan gyaruwanta ku kirashi kuna masu kwadayi da tsoron, lallai rahamar Allah yana kusa da masu kyautatawa (56)"[145].
- Ya hana tilastawa wani yin addini da canza mutane akan akidar su da karfi, Allah madaukaki yace: " da Allah yaso da mutanen duniya sunyi imani baki dayan su, shin zaka zama me tilastawa mutane ne sai sun zama muminai (99)"[146].
Wannan bayana nufin abar da'awa bane da kira zuwa ga Allah da isar ma mutane sakon Allah ta hanyar amfani da dabaru da kalamai masu kyau domin su san hakikanin muslunci, saboda daga cikin abunda musuluci ya kebanta dasu shine wajabcin isar da wannan addini da bayyanar dashi ga mutane baki dayan su, duk wanda da'awar muslunci ingantacce ya isar masa to shiriyan sa yana hannun Allah ba hannun mutum ba.
- Yayi umurni da yin shawara sannan kuma ya sanya haka cikin ka'idoji wanda musulunci ya ginu akai cikin dukkanin matsalar da babu nassi akai cikin alkur'ani ko kuma hadisin manzon Allah s.a.w mai tsarki), musulunci yayi haka ne saboda kowa cikin al'ummar musulmi ya mure hakkokin sa wanda shari'a ta bashi, Allah madaukaki yace: " al'amarin su na sharawa ne a tsakanin su"[147].
Sannan kuma Allah ya zaburar da annabin sa akan aiwatar da wannan ka'ida domin ta zama tafarki wanda yan bayan sa zasuyi aiki dashi. Allah madaukaki yace: " karika neman shawaran su cikin al'amura"[148].
- Yayi umurni da yabar da hakkoki ga masu shi da kuma tsaida adalci a tsakanin mutane, Allah madaukaki yace: " Allah yana umurtan ku da ku mayar da amana ga masu shi sannan kuma idan zakuyi hukunci a tsakanin mutane kuyi adalci, lallai madalla da abunda Allah yake maku wa'azi dashi, lallai Allah ya kasance me ji ne kuma me gani (58)".
- Yayi umurni da taimakon wanda aka zalumta koda kuwa hakan yakai asa karfi ne, Allah madaukaki yace: " me yasa bazakuyi yaki ba domin daukaka Kalmar allah alhali masu raunin cikinku mazaje da mata da kananan yara suna cewa ya ubangijin mu ka fitar damu daga cikin wannan al'umma azzalumai….."[149]
Kuma saboda kasance akwai wasu mutane wanda lalama baya dacewa dasu dole sai an sa masu karfi kamar yadda muka fada abaya an samu wasu dokoki a musulunci masu karfin iko wanda yaba shugaba na aiwatar da hukunci me tsauri domin ya kiyaye ma mutane wannan hakkoki nasu cikin al'umma da kuma sanya ido akan aiwatar dasu yadda ya kamata da kuma rashin ta'adi akan su, yanke hukunci na ukuba akan duk wanda yayi ta'adi akan hakkokin mutane yana faruwa na karkashin wannan tsari kamar haka:
Tsarin hukuncin kotu:
Shine tsari wanda ya kebanta da wani yanke a hukumance wanda ake zuwa wurin su domin raba fada da sabani a tsakanin mutane da kuma mayar da hakki zuwa ga masu shi da tabbabar da adalci da hana zalumci da hukunta masu laifi ta hanyar amfani da hukuncin Allah akan da alkur'ani da hadisan manzon allah s.a.w, saboda kasancewar su littafai ginshikai na shari'a a cikin musulunci, zama alkali yana da sharudda a musulunci da dokoki, daga cikin wannan sharudda da dokoki muhimmai akwai:
- Mutum ya kasance me hankali, balagagge.
- Ya ksance me cikakken lafiyar jiki sannan kuma yana da damar daukan gajiya da wahalhalun alkalanci.
- Ya kasance masanin hukunce hukuncen musulunci, me banbancewa tsakanin halal da haram matsani hukunce hukunce masu shubuhohi a cikin musulunci kuma yanada ikon yin kiyasi da fitar da hukunci cikin nassi , kuma zai iya bayar da fatawa cikin dukkanin al'amuran da suka shafi addini da duniya.
- Ya kasance kamuli me dabi'u kyawawa da kuma siffar me kyau kuma mutane suna sonshi domin su rika amsar hukuncin sa da yarda da hakan.
Ko wani mutum cikin al'umma yanada hakkin shigar da kara kotu idan an zalumce sa ba tare da duba addinin sa ba ko akidar sa.
Sannan kuma wanda me kara da wanda ake karansa yana kowa yanada hakkin dai-daita su wurin yi masu adalci agaban alkali, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " duk wanda aka jarabe shi da alkalanci cikin musulmai to yayi adalci a tsakanin su cikin irin kallon da zai ma me kara da wanda ake kara a gabansa, da duka adalci cikin nunin sa da zayyi da hannu wurin hukunci, da kuma wurin da zai zauna da majalisin shi, kada ya rika daga muryan sa akan daya cikin masu kara ya rika kankantar da muryan sa akan dayan" sunan albaihaqi, hadisi ne me rauni.
Da kuma fadin sa manzon Allah s.a.w ga Aliyu dan Abi dalib lokacin da zai nada shi alkalinci: " llalai Allah zai shiryar da zuciyar ka sannan kuma zai tabbatar da harshen ka, idan musu sabani suka zauna a gabanka kada kayi hukunci har sai kaji daga bakin kowa domin da hakan ne zaka gane gaskiya" hadisi ne ingantacce, Ahmad ne da abu dawud suka rawaito shi.
Asali a muslunci shine barrantan wanda ake tuhuma har sai tuhumar ya tabbata, saboda fadin manzon Alla s.a.w: " da ace za'a ba mutane duk abunda suka tuhuma a basu gakiya akai da mutane sun rika ikirari da kai kara akan jinin mutane yan uwan su da dukiyoyin su, sai dai dole sai me kara ya tabbatar da shaidu shi kuma wanda ake kara idan ya musa faruwan haka sai yayi rantsuwa". Buhari da muslim ne suka rawaito hadisin.
Wanda ake tuhuma yana da hakkoki a musulunci, ba yana nufin hutamar da aka masa ya kwace masa hakkokin sa bane, baya halatta a tilasta mashi ko kuma azabtar dashi da tsoratar dashi ko kuma yi masa mu'amala kamar dabba domin sanya shi yayi yarda da wannan tuhuma da ake mashi, saboda fadin manzon Allah s.a.w: " lallai Allah zai azabtar da masu azabtar da mutane a duniya" muslim ne ya rawaito shi.
An rawaito daga Umar dan kaddab Allah yakara masa yarda yace: babu tabbas nagaskiyarikirarin mutumin da aka tilasta masa da yunwa ko kuma tsoratar dashi ko kulle shi akan sai ya yarda da tuhumar da ake masa"[150].
Daukan nauyin laifin abun da mutum ya aikata a muslunci, ba'a daurawa wani laifin wani a musulunci baya halatta a zabatar da dan uwan mutumin da ake zargi ko kuma tuhumar sa, saboda fadin Allah madaukaki: " duk wanda ya aikata aiki na kwarai zai ga sakamakon kayan sawanda kuma ya aikata mummunan aiki zai ga sakamakon kayan sa shima, ubangijin ka baya zalumtar bawansa ko kadan"[151].
Da kuma fadin manzon Allah s.a.w: " ku saurara kuji kada wata rai tadau nauyin laifin wata rai" hadisi ne ingantacce, Nasa'I ne ya rawaito shi.
Alkalanci tsakanin mutane a musulunci yana da sharudda da ladubba wacce sakon da kalifa na biyu sarkin shugan muminai Umar dan Kaddab ya aikawa wani alkali zai bayyana mana yadda musulunci ya himmatu da wannan bangare wanda shine mataki na farko na kiyaye hakkokin mutane:
(daga bawan Allah Umar, shugaban muminai zuwa ga Abdullahi dan Kais, amincin Allah ya tabbata a gareka, bayan haka alkalanci wajibi ne wanda aka hukunta kuma sunnar manzon Allah ce abun koyi, ka tsaya ka fahimta idan aka kawo maka hukunci, babu amfanin ka fadi hukunci da gaskiyar da ka fahimta baka zartar dashi, ka dai-daita tsakanin mutane a wurin majalisinka da fuskar ka saboda kada wani me mulki yayi tunanin ka bashi gaskiya saboda mulkin sa, sannan kuma kada talaka me rauni ya cire tsammani daga adalcin ka saboda shi talaka ne, hujja tana kan wanda yake kara wani, sannan kuma rantsuwa akan wanda wanda ya musunta abunda ake zargin sa dashi, sulhu ya halatta tsakanin mutane sai dai sulhun da zai halatta haramun ko kuma haramta halal, kada hukunci da ka yanke a jiya abisa kukskure sai yau aka shiryar dakai zuwa gakiya kaki komama gaskiya, domin kuwa gaskiya babu abunda yake bata shi, ka sani komama gaskiya idan ka fahimce hakan yafiye maka alheri da kaci gaba da tafiya akan bata, kayi ijtiha cikin abunda kake kokwantan sa a zuciyar ka cikin hukuncin da babu nassi akai daga ayar alkur'ani ko kuma sunnar manzon Allah, kasan abubuwan da suke da kamanceceniya masu kusa da juna wurin kama, sannan kayi kiyasn ka akansu bayan haka, sa'annan ka dogara ga Allah cikin kiyasin da kayi wanda kake ganin shine gaskiya, ka sanyawa wanda yake tuhumar mutumin da bayanan wani madogari wanda zaka gina hukunci akai, idan yazo maka da hujja ka bashi hakkin sa idan kuma be zo maka da wata hujja ba to kamayar da abun shari'a sai an masu alkalanci akai, musulmai adalai ne a kan shaidar su sai dai mutumin da aka taba yi masa bulala akan wani hakki ko kuma wanda ya saba bayar da shedar karya ko kuma wanda ake zargin sa cikin addinin sa akan masoyan sa ko kuma yan uwan sa, lallai Allah ya isar maku da abubuwan da suke boye sannan kuma ya taimaka maku da hujjoji da dalilai, kashedin ka da tsawatarwa da tsoratar wa ko kuma azabtar da wanda kakeyima shari'a a wurin hukuncin gaskiya wanda Allah ya tanadar masa da dunbin lada kuma yana kawo yarda, saboda duk mutumin da yayi gyara cikin abunda ya bayyana ko kuma wanda be bayyana ba Allah zai gyara tsakanin sa da mutane. Hadisi e ingantacce daru kudniy da baihaki suka rawaito shi, kuma albani ya ingantashi cikin littafin al'irwa'I 2619.
Maganan akan alkalanci a muslunci yana da tsayi, akwai littattafai da suke Magana musamman akai duk wanda yake son kara sani akai sai yaje ya duba su.
Tsarin Hisba:
Tsarin Hisba tsari ne a msulunci na lada wanda hadafin sa shine a sanya ido wurin garin mutane sun tsayu akan aikata dokokin Allah da shari'ar sa ta hanyar masu umurni da kyakyawan aiki da kuma hanasu aikata mummunan aiki ta hanyar aiwatar da shari'ar musulunci da bibiyan da kuma hukunta duk wanda ya aikata wani mummunan aiki wanda ya sabama shari'a, da kuma sa ido akan abubuwan da suka shafi rayuwan mutane kamar ha'inci cikin kasuwanci da siyar da abubuwan da aka haramta ko kuma boye kaya domin suyi tsada a kasuwa, da kuma sa ido ga hakkokin jama'a kamar rusa wani gine gine wanda zai fado akan mutane, wannan ayyukan dukan sun a lada ne ba wajibi bane wanda tsarin Hisba ke aikatarwa saboda da riko da fadin Allah madaukaki: " kun kasance mafificiyar Allah a doron kada cikin mutane, kuna umurni da kyakyawan aiki da kuma yin hani da mummunan aiki" suratu al'imran ayata 110.
Da kuma tsoron azabar Allah wanda yafi cewa: " an tsinewa wanda suka kafirta cikin bani isra'il ta baki annabi dawud da Isa dan Maryam, saboda abunda suka kasance suna aikatawa na sabo da ta'addanci (78)"[152].
Ya wajaba akan ko wani musulmi cikin al'umma daya rika yin umurni da kyakyawan aiki da kuma hani da mummunan aiki gwargwadon yadda zai iya saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " duk wanda yaga wani mummunan aiki a cikinku to ya hanashi da hannun sa idan kuma bazai iya hanawa ba da hannun sa to ya hana da bakin sa idan bazai iya hanawa ba da baki shima to ya kyamaci abun a zuciyar sa hakan shine matakin imani ta karshe" muslim ne ya rawaito shi.
Ka sani hana mummunan aiki yanada sharadi cewa kada hanawar ya haifar da wani mummunan aiki wanda yafi wanda za'a hana saboda tabbatar da maslaha babba a tsakanin su.
Hakika addinin musulunci da Allah ya aiko Muhammad dashi s.a.w wanda aka tattara masa hikima na Magana ya tanadi hakkoki na dan adam wanda ya dunkule su wuri daya a killace, manzon Allah s.a.w yace: " lallai jinin ku da dukiyoyin ku da mutuncin ku haramun ne a kanku kamar haramcin wannan rana taku cikin wannan wata me haramci a cikin gari me haramci…" buhari ne ya rawaito shi.
A karkashin wannan karmar ta kunshi hakkiki na dan adam masu tarin yawa wanda musulunci yazo dasu domin kiyaye su da kuma yin hukunci me radadi ga mutumin da ya aikata su, zamu kawo bayanin da aka tabbatar dashi a garin alkahira akan hakkokin dan adam a muslunci, ya kamata muyi ishara da cewa wannan hakkoki da aka ambata cikin wannan bayani an kawo ka'idoji game gari wanda suka kunshi dukkanin hakkokin dan adam a musulunci, ka'idoji ne wanda suka kunshi dukkanin hakkoki kanana wanda idan mukace zamu rubuta su to zai dauki lokaci dayawa, ya ishemu muyi ishara zuwa ga manyan ka'idoji duk wanda yake son Karin sani akan kananan sai ya koma zuwa ga wannan littafi, ta tabbata ban wuce gona da iri ba idan nace lallai musulunci yazo ne domin kiyaye hakkokin dan adam baki dayan su domin mutane suyi tsira duniyar su da lahiaran su.
Shelar muslunci ga hakkokin dan Adam[153]
Da sunan Allah me rahma me jin kai.
Allah madaukaki yace: " yaku mutane lallai mun halicce ku daga namiji d mace sannan kuma muka sanya ku kuma zama jama'a da kibilu domin ku samu sanayya a tsakanin junan ku, lallai wanda yafi wani a cikin ku a wurin Allah shin ewanda yafiku takawa"[154].
Lallai kasashen da suke wakilai cikin shirya taron bita na musulunci saboda imanin su da allah ubangijin talikai wanda ya halicci komai kuma me bayar bayar da dukkanin ni'ima wanda ya halicci dan adam cikin sura me kyau ya kuma karrama shi sannan ya sanya shi ya zama kalifa da wakilin sa domin raya kasa da gayra ta ya kuma daura masa wani amana ta iabadar allah ya kuma hore masa abubuwan da suke sama da kasa baki daya.
Da kuma gasgatawa ga annabtar manzon Allah s.a.w wanda Allah ya aiko shi da shiriya da kuma addini na gaskiya domin rahama ga duniya baki daya, da kuma yantar da masu bautan dagutai da masu girman kai, ya kuma shelanta dai-daito tsakanin dan adam baki daya babu wani wanda yafi wani falala sai da tsoron Allah, ya kuma yi watsi da dukkanin banbance banbance da kiyayya tsakanin mutane wanda Allah ya halicce su daga uba daya.
Da kuma mayar da mutane zuwa ga akidar tauhida tsantsa wanda muslunci ya ginu akai wanda yake kiran mutane baki dayan su da cewa kada su bautawa kowa sai Allah shi kadai batare da hadashi da wani ba kuma kada su riki wasunsu su koma abun bautar su kom abayan Allah, wanda yaba mutum cikakken yancin sa da dawo masa da karamar sa sannan kuma yayi shelar yantar da mutum daga bautar mutum kamar sa.
Da kuma tabbatar da abunda muslunci dawwa marmiya yazo dashi na kiyaye addinin mutum da ran sa da hankalin sa da mutuncin sa da dukiyar sa da kuma dangantakar sa, da kuma abunda ya kebanta dashi na tattara dukkanin abubuwan rayuwa baki daya da kuma kasancewar sa tsaka tsaki cikin dukkanin hukunce hukuncen sa da dokokin sa , sai ya hada tsakanin ruhi da kudi da kuma tsakanin hankali da zuciya, ya kuma tabbatar da canjin zamani ga al'ummar musulunci wanda allah ya sanyata mafificiyar al'umma wacce take gadar ma mutum wayewar duniya madaidai ciya wacce ta hada duniya da lahira ta kuma hada tsakanin ilimi da imani wanda al'umma yau take bukatar su domin shiryiwa daga dimuwa da mazhabobi da suke yaduwa a tsakanin mutane, da kuma gabatar da nemo mafita akan matsalolin ababen rayuwa na zamani.
Da yin imani da cewa lallai hakkokin na muhimmai da yanci n agama gari cikin musulunci wani bangare ne na addinin musulunci wanda babu wani mutum daya mallaki damar share su ko kuma share wani bangare daga ciki ko kuma wace gona da iri akan su, ko kuma jahiltar hukunce hukuncen hukuncen Allah wanda yayi umuri dasu, Allah ya saukar da littattafansa dasu ya kuma aiko cika makon annabawa da shari'a wacce ta zama kariya ga ibada da kuma gusar da kiyayya da gaba da ita, ko wani mutum ya zama wajibi akan say a kiyaye su da al'umma baki dayanta. Lallai kasahen da suke da wakilci cikin kungiyar taron wayar da kai na musulunci sun shlanta abubuwa kamar haka:
Doka ta farko:
- Mutane yan gida daya wanda bautan Allah ya hadasu da uba annabi adam, sannan mutane baki dayan su dai-dai suke wurin karamar su ta dan adam wurin sauke nauyin bautan Allah ba tare da banabncin launin fata ba ko yare ko jinsi da makamantan haka na abubuwan da suke kawo banbanci, sanann kuma ikida ingantacciya itace wacce zata kiyaye cikar karamar mutum.
- Lalai halittu baki dayan su iyalai ne na Allah wanda shi yake jujjuya al'amuran su da basu abinci da abubuwar rayuwan su, sannan kuma wanda yafi soyuwa cikin mutane agun Allah shine wanda yafi amfanar da mutane, sannan kuma babu wani wanda yafi wani falala sai da tsoron allah da aiki na kwarai.
Doka ta biyu:
- Rayuwa wata kyauta ce daga Allah sannan kuma shine yaki kiyaye kowa, ya zama wajibi akan kowa da hukma kiyaye wannan hakki da kuma daukan mataki akan duk wanda zaiyi ta'adi akanta, sannan kuma baya halatta kasha rai haka kurum ba tare da wani hukuncin shari'a ba.
- Haramun ne haifar da duk wani hanya wacce zata kai ga rasa rayukan mutane.
- Kiyaye rayuwan dan adam har zuwa lokacin da Allah ya diban mata.
- Kar gangan jikin mutum baya halatta ta'adi a gareta, kamar yadda baya halatta wasa rayuwan mutane sannan kuma dole ne hukuma su dau nauyin kiyaye rayukan mutanen su.
Doka ta uku:
- a lokacin yaki baya halatta kasha duk mutumin da be dau makami wand aba ruwan shi cikin yakin kamar tsofaffi da mata da yara sannan kuma wanda akaji masu rauni da marasa dole ne a basu magani da kuma ciyar da fursinonin yaki da tufatar dasu sannan kuma haramun ne ayi masu gunduwa gunduwa wurin kasha su, sannan kuma ya zama wajibi ayi musayan iyalai wanda yakin yayi sandiyyar raba su da juna.
- Baya halatta yanke bishiya ko kuma lalata shuka ko rusa gidaje da kamfanoni na makiya dan mugunta ko kuma makamancin haka.
Doka ta hudu:
- Ko wani mutum yana da yancin sa da kuma kiyaye masa darajar a lokacin rayuwan sa da bayan mutuwar sa, ya zama wajibi akan hukuma ta tsare gawar sa da kabarin sa.
Doka ta biyar:
- Iyalai sune ginshiki na samar da al'umma, sannan aure shine yake karfafa hakan, sannan maza da mata sunada hakkin yin aure kada a juya masu wannan hakki nasu najin dadi da wani abu na banbancin gari ko fata ko jinsi.
- Wajibin hukuma ne ta kawar da duk wani tsadar aure da sawwake hanyoyin aure da kuma kare iyalai.
Doka ta shida:
- Mace dai dai take dana miji cikin darajar dan adam, tana da hakki irin na namiji na aikace aikace da kuma hakkin tara dukiya da wasu abubuwa mallakin ta cikin al'umma da kuma hakkin kiyaye mata suna da dangin ta.
- Ya wajaba akan namiji cdaukar nauyin ciyar da gida da sauran bukatun su.
Doka ta bakwai:
- Ko wani yaro yanada hakki akan iyayen sa da hukuma da al'umma na renon sa da tarbiyyar sa da kula dashi na hidindimun san a kudi da bashi ilimi kamar yadda ya wajaba bada kariya ga mahaifiya da jaririnta da basu kula na musamman.
- Iyaye da wanda nauyi ya rataya akansu suna da hakkin zabar irin tarbiyyan da suke son bawa yaransu tare da lura da maslahar su da kuma rayuwar sa ta gama ta hanyar basu kyawayan dabi'u da hukunce hukunce na addini.
- Iyaye sunada hakkoki akan yaran su, sannan yan uwa suna da hakkoki akan yan uwan su kamar yadda musulunci ya tanadar.
Doka ta takwas:
Ko wani mutum yana da yancin yin amfani da damar sa gwargwadon yadda musuluni yayi tanadi cikin al'umma idan kuma bayanan sai waliyyin say a gajeshi.
Doka ta tara:
- Neman ilim wajibi ne akan al'umma sannan kuma wajibi ne akan hukuma su samar da hanyoyi da sawwake hakan gwargwadon maslahar al'umma sannan kuma hukuma ta bude ma mutum hanyar ilimin addini da hakkokin kasa da kuma yin amfani dasu domin amfanin mutum.
- Daga cikin hakkin kowa ni mutum ne a bashi tarbiyya da nuna masa shawarwari na gari wanda zasu amfanesa akan iyaye da makarantu da jami'u da kafafen sadarwa da makamantar su su rika aiki wurin ba mutum tarbiyya ta addini da zaman takewar duniya wacce zata karfafa rayuwan mutum da kuma kara masa imani da Allah da daraja hakkoki da wajiban dake kansa da kuma kiyaye su.
Doka ta goma:
Bayan ya zama wajibi ga dan adam bin addinin musulunci addinin fidira baya halatta yin amfani da ko wace irin nau'i na tilastawa akan sa wurin yin addini kamar yadda baya halatta yayi amfani da talaucin sa ko kuma raunin sa ko jahilcin sa wurin canzawa daga addinin musulunci zuwa wani addini na daban ko kuma komawa mara addini.
Doka ta goma sha daya:
- Ana haifann ko wnai mutum da cikakken yanci babu wanda yake da iko bautar dashi ko kuma tilasta masa ko ya bautar dashi, babu wanda ake bauta masa koma bayan Allah madaukaki.
- Mulkin mallaka ta dukkanin nau'in sa yana daga cikin mafiya munin nau'i na bautarwa wanda haramun matuka, wanda ake mulka sunada hakkin neman yancin su sannan ya zama wajibi ga sauran kasashe su taimaka masu wurin samun yancin gashin kansu.
Doka ta goma sha biyu:
Ko wani mutum a matsanin me cikakken ikon bin shari'a da kuma kai komo da zabin wurin da zai zauna a cikin kasar sa ko kuma wajen kasar da aka haife sa, yanada damar komawa wata kasa idan aka tsangume shi a kasar sa kuma ya zama wajibi ga kasar daya koma su bashi kariya matukar be aika wani laifi ba na barna cikin addini.
Doka ta goma sha uku:
Aiki wajibin hukuma ne su samar dashi ga dukkanin wanda zai iya, sannan mutum yana da hakkin zabar irin aikin daya ke so wanda ya dace dashi wanda zai tabbatar da maslahar sa da maslahar al'umma, sannan kuma ma'aikaci yanada hakkin a kara masa lafiya da tsaro da sauran hakkoki na zaman takewa, baya halatta a sanya shi aikin daya fi karfin sa ko kuma tilasta masa ko amfani dashi da cutar dashi, sannan yana da hakkin ko tanada hakki na zuw akotu domin a kwatar masa ko mata hakkin sun a wannan aikin da sukayi, da kuma kara masa girma agun aiki idan lokacin hakan yayi ba tare da jinkiri ba, idan aka samu sabani tsakanin ma'aikata dame kamfani wajibi ne akan hukuma su shiga tsakani dan nemo gaskiya da kawar da zalumci da tabbatar da adalci ba tare cuta ba.
Doka ta goma sha hudu:
Mutum yana da hakkin neman kudi ta hanyar halal ba tare da yin ha'inci ba ko cutar da kansa ko wanin sa da riba wanda aka haramtata.
Doka ta sha biyar:
- Ko wani mutum yana da hakkin mallakar abu ta hanyar halaliyar sa da kuma amfani da wannan abu mallakin sa ta hanyar da bazai cutar dashi ba ko wanin sa, baya halatta hukuma ta kwace abu mallakin mutum a hannun sa sai dai lalura na amfanin mutane baki daya sannan kuma dole ne a biya sa akan haka.
- Haramun ne tara dukiya da boyeta sai dai ta hanyar da shari'a ta yarda dashi.
Doka ta sha shida:
Ko wani mutu yanada hakkin amfani da abunda yasamu ta hanyar aiki ko kuma hikimar sa da kimiyyar sa sannan kuma yanada hakkin kiyaye dukiyar sa daya samo daga hakan amma yakasance hanyar samun dukiyar be sabama addini ba.
Doka ta sha bakwai:
- Ko wnai mutum yana da hakkin rayuwa cikin yanani me tsabta wacce babu fasadin annoba a cikikin ta ko kuma munanan dabi'u wacce kuma zata taimaka masa wurin gina rayuwan sa, sannan kuma wajibi ne akan hukuma ta tabbatar masa da hakan ta hanayar kawar da duk wani abunda zai haifar da samuwar wannan fasadi.
- Ko wani mutum yanada hakkin kiyaye lafiyar sa akan hukuma ta hanyar samar da dukkanin kayayyikin more rayuwa n agama gari.
- Dole ne hukumar ta kiyayema mutum yancin rayuwa cikin karamar sa wanda zai bashi damar samun abunda zai dau nayin wanda suke karkashin sa na ciyar da su da tufatarwa da karantarwa da kuma sama masu magani da sauran bukatar su.
Doka ta sha takwas:
- Ko wani mutum yanada hakkin rayuwa na aminci cikin akan ransa da addinin da iyalan sa da mutuncin sa da dukiyar sa.
- Mutum yana da hakki na gudanar da al'amuran da suka shafi rayuwan sa ciki gidan sa da iyalan sa da kudiyar sa da zirga zirgan sai yadda yake so, baya halatta a rika bin diddigin laifukan sa ko kuma sanya masa ido ko munanawa dajarsa da kuma bashi kariya daga dukkanin wanda yayi masa ta'addanci da zalumci.
- Gidajen mutane yana da hurumi baya halatta kowa ya shigan masu gida sai da izinin su ko ta wani hanya wanda be halatta ba a shari'a, sannan kuma baya halatta rusa masu gida mallakesa ko Koran mutanen ciki.
Doka ta sha tara:
- Mutane daya suke a agaban shari'a shuwabannin su da wanda ake shugabanta.
- Hakkanin samar da kotu wacce zata rika kiyaye ma mutane hakkokin su.
- Mutum shike daukan nauyin laifin sa dakan sa.
- Babu wani laifi ko hukunci sai da hukuncin musulunci.
- Wanda ake tuhuma barrantacce ni har sai an tabbatar da tuhumar da akeyi masa a gabakan kotu na adalci wacce zata bashi lauya wanda zai kare sa.
Doka ta ashirin:
- Baya halatta kama mutum ko tuye masa yancin sa ko korar sa ko azabtar dashi bada dalili ban a addini, kuma baya halatta kalubalantar sa da azabtar da jikin sa ko kuma ransa ko kuma ko wani irin nau'i na mu'amala mara kyau mara imani da wulakantar wawacce taci karo da darajan mutum da kimarsa.
- Baya halatta jaraba wani magani ko wani aiki na tiyata da mutum sai da yardan sa da kuma sharadin hakan bazai maza sanadin haifar masa da rashin lafiya ba ko kuma hatsari ga rayuwan sa, kamar yadda baya halatta a kirkiri wani doka wacce zata bada damar haka.
Doka ta ashirin da daya:
Wulakanta mutum haramun ne ta ko wani hanya da kuma ko wani irin hadafi.
Doka ta ashirin da biyu:
- Ko wani mutum yanada yancin fadin ra'ayin sa ta hanyar da beci karo da karantarwan musulunci ba.
- Ko wani mutum yanada hakkin yin kira zuwa ga alheri da yin han da mummunan aiki gwargwadon karantarwan musulunci.
- Wayar da kan mutane dan gane da muhimmancin rayuwan dabbobi ga al'umma da kuma rashin amfani dasu ta hanyar wuce gona da iri ko kuma girmamasu ta hanyar bauta masu, da kuma kare karamar annabawa da kiyaye dakkuninan abunda zai katre darajar ko karamar al'umma daga fashewa da faduwa ko kuma cutar dasu ko lalata masu akidar su.
- Baya halatta ruruta kiyayyar a tsakanin mutane da ta'assubanci da mazhaba wanda zai haifar da kabilanci ta dukkanin bangarorinta.
Doka ta ashirin da uku:
- Shugabancin mutane amana ne haramun ne amfani da ita ta hanyar aikata abubuwan da sukaci karo da hakkokin yan adam na asali.
- Ko wani mutum yanada hakkin neman shugabancin kasar sa kamar yadda yake da hakkin yin aiki karkashin ma'aikatar kasa gwargwadon yadda addini ya shar'anta.
Doka ta ashirin da hudu:
Dukkanin hakkoki da yancin da aka ambace su cikin wannan sanarwan an kayyade su ne da hukunce hukuncen muslunci.
Doka ta ashirin da biyar:
Shari'ar musulunci itace madogara daya tilo domin bayani da fassara wannan dokoki wanda aka ambace su.
Birnin Alkahira: 12/ ga watan muharram/1411 ta hijira. Dai dai da 5/ ga watan ugusta/ 1990 miladiyya.
Lallai tabbatar da wannan hakkoki shine hanya ingantacce na samar da al'ummar musulunci ta hakika wacce ta siffantu da abubuwa masu zuwa:[155].
- Al'umma: wacce mutanen ta dai dai suke babu wani wanda yafi wani falala ko iko akan wani saboda banbancin fata ko kabila ko jinsi ko yare.
- Al'umma: waccce taba kowa dama da hakki na rayuwa da gudanar da wajiban sa wanda aka daura masa dai dai wa daidai babu banci a tsakanin su. Dai daito wacce ta samu asali daga asalin halittar mutum, Allah madaukaki yace:" yaku mutane lallai mun halicce ku daga namiji da mace". Da kuma abunda Allah ya hurewa mutum na karrama shi, allah madaukaki yace: " hakika mun karrama dan Adam sannan kuma mun daurashi a doron kasa da cikin ruwa sannan kuma muka azurta shi daga dadaden abubuwa muka kuma daukakashi akan halittun mu daukakawa (70)".
- Al'umma: wacce hakkin dan adam acikinta yayi dai dai da burin rayuwan dan adam wanda akehaifan sa da ita sannan kuma ya girma a karkashin inuwanta, waanda zai aminta daga tilastawa da kaskantarwa da wulkantarwa da kuma bautarwa.
- Al'umma: wacce take son haifar da iyalai wanda zasu zama yan kasa nagari da kokarin gina kasar su da kare da son ganin dawwamar ta.
- Al'umma: wacce babu bancin tsakanin su tsakanin me mulkin cikin su da wanda ake mulka wurin bin hukunce hukuncen da mahalicci ya sanya, tsarki ya tabbata a gare shi.
- Al'umma: wacce wanda shugabancin ta amana ne wanda ake daurawa shugaba domin ya tabbatar da abunda shari'a ke so na ganin ci gaba, da kuma amfani da tafarkin da wannan shari'a ta gindaya domin tabbatar da wannan buri.
- Al'umma: wacce ko wani mutum acikin yayi imani da Allah daya ne, shine mamallakin duniya baki daya…. Kuma duk abun duniya an halicce su ne domin amfanin mutane baki daya, kyauta daga Allah badan cancantan wani ba, sannan kuma hakkin kowa ne ya samu rabon san a adalci daga cikin wannan kyauta na Allah, Allah madaukaki yace: " ya kuma hore maku abunda suke sammai da kassai baki daya daga gare shi"[156].
- Al'umma: wacce take samar da siyasa wanda zai tsara al'amuran mutane da kuma yin shawarwari wurin zaitar wa da amfani da wannan tsari kamar yadda Allah ya fadi cewa: "al'amarin shawara ne a tsakanin su"[157].
- Al'umma: wacce take bawa koma dama domin sauke nauyin sa gwargwadon iyawan sa, wacce za'a saka masa akan haka anan duniya a gaban mutanen sa, sannan kuma a lahira agaban halittun Allah baki daya (dukkanin ku masu kiwo ne kuma za'a tambaye ku akan kiwon da aka baku) buhari da muslim ne suka rawaito shi.
- Al'umma: wacce shuganta da mabiyansa kowa yana tsayawa a gaban alkali da yanci iri data babu banbanci a tsakanin su, hatta wurin ayyukan shigar da kara babu babbanci wurin yin su a tsakin su.
- Al'umma: wacce kowa mutum wakili ne na kasar sa, yana jin cikin hakkin sa ne yakai karar ko wane wanda yayi barna cikin kasar sa, sannan kuma zai iya neman taimakon kowa cikin mutane su taimaka masa kuma bazasu kunyatar dashi akan matsalar sa ta adalci.
- Al'umma: wacce take yaki da dukkanin wani nau'I na barna daya shigo cikinta sannan kuma kowa yana da yancin da tsaro da karama wurin riko da abunda shari'ar musulunci ta tabbatar dashi na hakkin dan adam da kuma tukuru dan aiwatar da haka da kiyaye shi kuma.
Lallai wa'ainna hakkoki da bayanin su ya gabata an cirosu ne daga cikin alkur'ani da hadisan manzon Allah s.a.w masu daraja na Magana ne ko aikin sa ko kuma abunda ayi a gabansa ya tabbatar dashi, kuma kada amanta cewa wannan hakkoki wanda aka ambata hakkoki ne da ka'idoji manya wanda a karkashin su akwai dayawa na hakkoki kanana wanda bamu ambata ba saboda gudun tsawaitawa, sai dai kamar yadda aka fadi cikin doka ta ashirin da biyar cewa shari'ar musulunci itace madogaro daya tilo wanda zata fassara da yin bayanin dokokin da aka ambata a sama. Watan ana nufin fadada bayani da kuma ambatan hakkokin da suke karkashin kowani doka.
Abubuwan da hakkokin dam adam a cikin muslunci ya banbanta da su akan sauran:
- Hakkoki kyauta daga Allah ba daga mutum ba wanda yake da son zuciya da bin sha'awar zuciyar sa da maslahar sa cikin wannan kado wnannan hakkoki da aiwatar dasu ta dukkanin bangaroro.
- Hakkoki ne wanda yake hade da akidar muslunci wanda shari'ar Allah yake basu kariya, saboda haka ta'adi akn su ta'adi ne akan hukunce hukuncen Allah kafin ya zama ta'adi akan dan Adam wanda hakan yake gadar wa mutum azaba duniya da lahira.
- Hakkoki ne wanda suka kunshi dukkanin abunda dan adam ke bukata na rayuwa sannan kuma sun dace da dabi'ar sa kuma yana la'akari da raunin sa ko kuma karfin sa da buwayar sa da kuka kaskancin sa.
- Hakkoki ne ga kowa karkashin inuwar tsarin muslunci ba tare da la'akari da banbancin fata mutum ba ko jinsin sa ko yaren sa ko kasar sa wanda yake rayuwa a ciki.
- Hakkoki ne wanda suke tabbatattu basa canza wa ko kuma a shara wasu bangare a ciki ko kore wani bangare cikin wani zamani ko wuri saboda ya dace da muradin mutum ko kuma al'aumma baki dayanta.
- Hakkoki ne wacce take tabbatar da tsayuwar al'umma wanda kowa a cikinta zai ji dadin rayuwa me karamci da annashwa, saboda kasancewar ta rahama ce daga ubangijin talikai zuwa ga mutane baki dayan su, tana kiyaye masu hakkokin sun a siyaysa da tattalin arzikin su da zaman takewar su da dabi'un su.
- Hakkoki ne wanda suke kellace ba'a bar su kara zube ba, ta yazasu ci karo ba da asaloli na shari'ar muslunci ko kuma ta cutar da maslahar jama'a, misalai yancin fadin ra'ayin mutum na kowa ne cikin mutanen al'ummar musulmai wanda yake da hakki cikakke na fadin gaskiya da kuma tunkarar duk wata bata domin toshe ta da kuma damar yin nasiha ga kowa da abun da zai tabbatar da maslahar shin ta duniya da lahira sai dai wannan yancin yana da ka'ida saboda kada mutum ya munana amfani da ita, dan ahaka akwai iyaka da ka'idoji wanda baya halatta a ketare su saboda gudun kada hakan ya kawo hayanya da kuma taka iyakokin Allah sai jama'a su cutu da kuma karya tsarin zaman takewar su, wannan ka'idojin su ne:
- Fadin wannan ra'ayi ta hanyar ilimi cikin tattaunawa wacce akeyin ta da zammar gina al'umma da hakima dayin amfani da kalamai masu dadi da gujema amfani da karfi da kalmomi na zage zage wanda zasu haifar da fitina da tayar da jijiyar wuya wacce zata kawo cutar wa kuma bazata tabbatar da wani amfanar w aba, Allah madaukaki yace: " kayi kira zuwa ga tafarkin ubangijin ka da hikima da kuma yin amfani da kalamai masu dadi, ka kuma yi muharawa dasu da abunda yafi kyau, lallai ubangijin shi yafi sanin wanda ya bace daga hanyar sa kuma shine wanda yafi sanin wanda suka shiryu (125)"[158].
- Kada mutum ya rika Magana cikin abubuwan da musulmai sukayi imani dashi suka kumayi ittafakin akan haka kamar samuwar Allah da gaskiyar Annabi Muhammad da dukkanin abunda yake zama suka da muzantawa ga muslunci… dadai sauran su.
- Rashin yin amfani da wannan yanci cikin dukkanin abunda zai cutar da mutane cikin la'amarin duniyar su ko kuma addinin su, kamar kutsawa cikin mutuncin su da yada sirrin su da shiga cikin dukkanin abu da zai zama hanya na keta hurumin su da mjtuncin su da yada alfasha da munanan ayyuka, Allah madaukaki yace: " lallai wanda suke son yada alfasha cikin al'ummar muminai sunada azaba me radadi anan duniya da kuma lahira, Allah shine masani amma ku baku san haka ba (19)"[159].
Shubuhohin wanda aka haifar dasu aka cusa su cikin muslunci:
Shubaha ta farko:
Fadin cewa lallai shari'ar da aka saukar wa manzon Allah Muhammad s.a.w da ita tun karni goma sha hudu da suka wuce wai bata kunshi dukkanin hakkokin dan adam bas abo da kasancewar ta bata canzawa wai bata tafiya dai dai da zamani wanda duniya ke ciki yanzu saboda samun wasu bukatu na mutane na canjin zamani!
Raddi akan wannan shubuha:
Lallai musulunci ya banbanta da sauran addinai wanda Allah ya aiko a baya wacce ta kasance addini ta imani wacce take tsarawa da kulla alaka tsakanin mutum da ubangijin sa kadai, saboda kasancewar shari'ar musulunci shari'a ce cikakkiya kasance warta shari'a ce wacce ta kunshi addini da rayuwan duniya tare, ta zama shari'a ce wacce ta kunshi addini saboda tana kulla alakar mutum musulmi da ubangijin sa mahaliccin sa, sannan kuma shari'a ce wacce ta kunshi rayuwan duniya saboda kasancewar ta tana tsarwa da kulla alada takanin al'ummar musulmai, da kuma alakar su da wand aba musulmai ba na al'ummar wata kasa, sannan kuma wannan shari'a ba irin sauran shari'u bane wanda aka saukar dasu ga wani zamani kebantacce don wata al'umma su kadai kawai kamar addinin yahudanci da kiristanci, amma ita addinin musulunci an saukar da ita ne ga mutane baki dayan su Allah madakaki yace: " bamu aike ka face ka zama rahama ga talikai baki dayan su (107)"[160].
Saboda haka duk wanda ya bibiyi hukunce hukuncen shari'ar musulunci zai ga cewa ta kunshe bangare biyu kamar haka:
- Bangaren farko shine tsara alaka tsakanin bawa da ubangijin san a akida da imani da ibadu da gado, wannan suna da hukuncin su tabbatacce wanda babu wani kofar jin ijtihadi a cikin sa ko kuma canza shi ta hanyar yi masa kari ko kuma share wani abu cikin wani zamani ko wuri ko kuma dan cimma muradin wani mutum wannan hukunce sune wanda ake kira da suna hukunce tabbatattu wanda basa canzawa kamar sallah misali ginshikan ta da yawan raka'o'in ta basa canzawa haka shima zakkah yawan abun da za'a bayar baya canzawa shima, haka suma magada wanda aka ambata aka sansu da kuma abunda za'a ba kowa acikin su baya canzawa, haka abun yake cikin sauran ibadu.
- Bangare na biyu tsara alaka tsakanin mutane da junarsu na mu'amalar su wacce take tsara masu al'amuran rayuwan su da alakar su da wasu al'ummomin wanda hukunce hukunce hakan yazo cikin musulunci a dunkuke wanda ba'ayi bayanin komai ba saboda ya zama yana iya amsar canji na zamani ta hanyar ijtihadi da abunda zai tabbatar da maslahar al'umma da mutanen ta cikin ko wani zamani da wuri wanda halayen su da ci gaban su yake banbanta, wannan yana nuni akan cewa shari'ar muslunci ya kunshi komai sannan kuma ta dace da kowani zamani.
Shubuha ta biyu:
Duk mutumin da be san hakikanin musulunci ba ko kuma ya santa a wurin makiyan musulunci zai rika samun shubuhar cewa musulunci yana zalumtar hakkokin wand aba musulmai ba saboda haka basu da wani kima a wurin sa, wannan shubahar yana cin karo da hakkin dan adam wanda ya bashi yancin yin akidar sa ba tare da takura mas aba!!!
Raddi akan wannan shubuha:
Lallai matsayar shari'ar musulunci game da mutane da suka saba masa wurin akida a bayya ne yake wanda babu wani kokwanta ko duhu a cikin sa, a karkashin ayoyin alkur'ani da sunnar manzon Allah s.a.w zai bayyanar mana cewa lallai yancin addini cikin al'ummar musulunci an ba kowa wannan yanci, babu wata kasa wacce take tilastawa mutanen da suke cikinta wand aba muslmai ba da cewa dole sai sun zama musulmai saboda aiki da fadin Allah madaukaki cewa: " da ubangijin ka yaso da mutanen duniya baki dayan su sun yi imani, yanzu shin kana tilastawa mutane ne sai sun zama muminai? (99)"[161].
Mu'amala dasu halal ne da cin abincin ma'abota littafi halal ne shima, kai musulunci banan kawai ya tsaya bay a halatta abunda yafi wannan yadda ya halatta auren mace cikin ma'abota littafi, babu shakka aure da gina zuri'a yana cikin al'amuran da musulunci ya himmatu dashi da bashi kulawar daya dace amma duk da haka ya halatta auran su, saboda fadin Allah madaukaki: " abincin ma'abota littafi halal ne agare ku kuma abincin ku halal ne a garesu, da kuma mata kamulallu daga cikin muminai da na ma'abota littafi halal ne auren su"[162].
Sannan kuma Allah madaukaki yana cewa: " Allah be haku mu'amala ba da zama da mutanen da basu yake ku ba cikin addinin ku sannan kuma basu fitar daku ba daga cikin gidajen ku kuyi kyautata masu dayi masu adalci, lallai Allah yana son masu adalci (8)"[163].
Sai dai mutanen da suka adawa daku suna da irin tasu mu'amala da hukunce daban da wannan, Allah madaukaki yace: " Allah yana hanaku nuna soyayya ga mutanen da suka yake ku kuma suka fitar daku daga ciki gidajen ku sannan kuma suka himmatu da shelar fitar daku daga cikin gidanje da kujibince su, lallai duk wanda ya jibince su sune azzalumai (9)"[164].
Har wayau musulunci ya halatta abunda yafi wannan wanda ya halatta tattaunawa dasu na addini sannan ya umurci musulmi da riko da ladubban tattaunawa da wani musamman wanda suka saba masu wurin akida idan hadafin tattaunawan shine neman gane gaskiya da binta, Allah madaukaki yana cewa: " kada kuyi jayayya da ma'abota litta fi sai dai da abunda yafi kyau"[165].
Sannan Allah yana fada ta bakin manzon sa Muhammad s.a.w wanda yake Magana da ma'abota wani addini cewa: " kace masu kuna ganin cewa abubuwan da kuke kira koma bayan Allah, zaku iya nunamun abunda suka halitta cikin kasa ko kuma kuma sunada hannu wurin halittan sama, kuzo mun da wani littafi gabanin wannan littafi ko kuma wani dalili na ilimi akan haka idan kun kasance masu gaskiya (4)"[166].
Bari mu kawo hujja da hukuncin wani mutum kirista bature me suna (Sir Thomas Arnold) cikin littafin sa me suna kira zuwa ga muslunci inda yake ke cewa cikin shafi na (48):[167] ya dace muyi hukunce daga salla ta bankwana tsakanin musulmai da kiristoci na larabawa cewa lallai karfi baya cikin hanya ta canza mutane da shigar dasu mulunci, Muhammad kansa yayi yarjejeniya ta zaman lafiya tare da wasu kabilu na kiristoci, sannan kuma ya dau alkawarin kare su da basu yanci na yin addinin su, kamar yadda yaba mutanen coci tabbacin samar masu da tsaro wanda zai basu hakkokin su da yancin aiwatar da ibadun su cikin kwanciyar hankali.
Shubuha ta uku:
Lallai cikin aiwatar da hukunce hukuncen muslunci na haddi akwai rashin tausayi da bushewar zuciya da kuma ta'adi game da hakkin dan Adam!!!.
Raddi akan wannan shubuha:
Kafin mufara ya kamata mu bude maganar da fadin cewa laifuka a musulunci sun kasu gida biyu:
- Laifuka wanda suke da hukuncin su cikin shari'a wannan laifukan kuwa sune (kisa da zina da sata da shan giya da kazafi da karuwanci da ridda da yaki)
- Laifuka wanda basu da hukunce kebantacce a cikin shari'ar musulunci wanda yabar ma shugaba yabke hukuncin daya gay a dace akan su gwargwadon maslahar al'umma wanda ake kiran haka da suna tsawatarwa (ta'aziri)
Mu sani cewa laifuka wanda suke da ukuba kebantattu a musulunci sun kasu gida biyu ne suma:
- Ukuba na laifuka wanda suka shafi hakkin mutum wanda sune (kisa ko kuma ta'adi akan wani gabar jikin mutum, ko yi masa kazafi da aikata zina) wanann ukubar za'a iya saukaka su idan me hakkin ya yafe sai ya tashi daga ukuba babba ya koma ukuba me sauki (tsawatarwa) wanda shugaba zai yanke hukuncin gwargwadon hakkin al'umma.
- Kasha na biyu shine ukuba akan laifuka wanda suka shafi hakkin Allah kadai (kamar shan abun maye da zina da sata, wannan ukubar basa taba fadi akan mutum matukar hakan yakai wurin alkali amma amfison suturta irin wannan laifi musamman da mutumin da ba'asan sa da aikata hakan ba mai makon akai shi wurin alkali ya zartar masa da hukunci kai tsaye.
Bari mu fadi wasu abubuwa wanda zamuyi Magana akan su game da aiwatar za haddi a cikin shari'ar muslunci:
- Ba'a zartar da haddi a muslunci sai akan mutum balagagge me hankali.
- Haddi a musulunci yana fadi idan an samu wata shubuha akan haka shubuha wacce shari'a ta yarda da ita, an rawaito hadisi daga manzon Allah s.a.w yace: " ku kawar da haddi akan musulmai da shubuhohi gwargwadon iyawar ku, idan kun samu wata mafita ga musulmi ku kyaleshi, yafi ma alkali alheri yayi kuskure akan yin afuwa da yayi kuskure cikin yin ukuba"[168]. Hadisi ne me rauni.
- Ba'a zartar da haddi a muslunci sai akan mutumin da yayi ta'adi akan lalurorin rayuwa guda biyar.
- Haddi yayi tabbata da ikirarin mutum dukda yana da damar janyewa daga ikirarin sa, ko kuma da shaidu maza adilai, ba'a amsar shedan mata akan haddi.
- Lallai manufar zartar da haddi akan mutane a musulunci shine tsawatar wa da hana mutane aikata wani aiki ko kuma Magana wacce zata cucar da al'umma ko kuma yin ta'adi akan hakkin mutane, tana kamar matsayin rigakafin ne na kare hakkokin da amincin al'umma da zaman lafiyar su, zartar da haddi rayuwa ce ga mutane kuma Allah yayi gaskiya daya ce: " kunada rayuwa cikin zartar da kisasi yaku ma'abota hankula."[169].
Bayan tsoratarwa da musulunci yayi akan aikata laifi da tsawatar wag a duk wanda yayi kokarin aikata wani laifi na barna da azaba a lahira bai manta da azaba ta kudi ba watan biyan diyya akan mai laifi ko kuma wanda ya sabama umurnun sa saboda cikin mutane akwai wanda ba abunda ya dace dashi sai tsanani da karfi wajen tsawatar dashi da hanashi aikata laifi na barna wanda ya kunshi cutarwa ga al'umma wannan saboda ya nuna maka cewa shiriyar musulunci be bar komai ba face ya bada hukunci akai ko kuma ya tsara shi, shi yasa muke ganin cewa musulunci ya tanadamma ko wani irin laifi na barna ukuba wacce ta dace dashi gwargwadon girman laifin mutum.
- Sai ya sanya hukuncin laifin kisa da gangan kisasi watan akashe wanda yayi kisa saboda fadin Allah madaukaki " yaku wanda sukayi imani mun wajabta maku kisasi akanku akan laifin kisa"[170].
Sai dai idan yan uwan wanda aka kasha sun yafi jinin dan uwan su saboda fadin Allah madaukaki "duk wanda ya yafe jinin dan uwan sag a mutumin da ya kasha shi to sai acanza masa da sanannen abu kuma yabiya da kyautatawa"[171].
- Ya kuma sanya hukuncin laifin kisa bisa kuskure biyan diyya da kuma yin kaffara, Allah madaukaki yana cewa: " beya halatta ga mumini ya kasha wani mumina sai bias kuskure, duk wanda ya kasha wani mumini bias kuskure to yay anta wuya musulma da kuma biyan diyya ga iyalansa sai dai idan sun yafe masa, idan ya kasance tsakaninku da mutanen da kuke da adawa ne amma kuma mumini ne to sai yay anta wuya mumina, idan kuma tsakaninku da mutanen akwai alkawari na zaman lafiya to sai ya biya diyya zuwa ga iyalan sa kuma ya yanta wuya mumina, duk wanda kuma be samu ba sai yayi azumin wata biyu a jere tuba daga zuwa ga Allah, Allah ya kasance masani kuma me hikima (92)"[172].
- Ya kuma sanya hukuncin lafin sata yanke hannun barawo, Allah madaukaki yace: " barawo da barauniya ku yanke masu hannu sakamakon abunda suka aikata daga Allah, Allah ya kasance mabuwayi kuma me hikima (38)"[173].
Ba'a zartar da hukuncin yanke hannu a musulunci sai an cika sharudda da dokoki kamar haka:
- Sai idan abunda aka sata yakai nisabi.
- Dole abunda aka satay a kasance cikin kebantaccen wuri misali Kaman cikin gida, ko store, sannan kuma ya kasance an kama barawon ne a wajen wannan kebantaccen wuri, da za'a kamashi a cikin wannan wukebantaccen wuri baza'a yanke masa hannu ba.
- Baza'a yanke hannun bag a barawon gida saboda anyi masa izinin shiga wannan wuri da aka kebance wannan kudi a cikin sa, Kaman misalin ma'aikacin banki idan ya saci kudin ajiya wanda ake aikia aciki, musamman ma ace hakan ya faru ne sakamakon sakaci na me wurin aikin nan ko kuma manaja.
- Babu yanke hannu akan mutumin dayayi fincen fili ko gonan shuka, misali kamar ya kwace fili da fince yace wannan fili na ne, saboda ai me asalin filin zai iya kai karansa gun yan sanda ko kuma ya nemi taimakon mutane suzo su taya shi Koran wannan mutumin daya keson kwace masa fili.
- Babu yanke hannu ga barawon da yayi sata da shubuha, kamar misali ya kasance yunwa ce ta sashi wannan sata ko kuma makamancin lalura na rayuwa irin wannan wanda mutum zai iya mutuwa akan haka.
Laifin sata tana daya daga cikin laifi masu matukar hatsari wanda take haifar da cutarwa ga al'umma da kuma kai farmaki akan dukiyar mutane da mutuncin su da rayukan su,da haifar da rashin zaman lafiya da natsuwa wanda musulunci yake da burin samar dasu ga al'umma, saboda barawo ko da kuwa burin sa sata ne za'a iya samun wani dalili wanda zai sashi kasha duk wanda zai kawo masa cikasa akan haka, kamar yadda zai iyayin ta'adi akan mutuncin mutane kuma, wannan laifi ne me matukar hatsari wanda take bukata ukuba me tsauri domin hanata, idan barawo yasan cewa za'a yanke masa hannu idan yayi sata lallai zai fasa satar domin kada a yanke masa hannu sai dukiyan mutane ya tsira daga sata.
- Sannan kuma ya sanya hukuncin laifin dan fashi me tsoratar da mutane da makami haddin mayaki saboda fadin Allah madaukaki ; " lallai sakamakon wanda suke yaki da Allah da manzon sa sannan kuma suna masu yada fasadina da barna a doron kasa shine a kasha su, ko kuma a tsire su ko a yanke masu hannu da kafa daban daban ko kuma a koresu daga kasar baki daya, haka sunada kunyatar wa a duniya sannan kuma a lahira sunada azaba me girma (33) sai dai wanda suka tuba kafin a kama su, kusani cewa lallai Allah me gafara ne kuma me jin kai (34)"[174].
Ana aiwatar da hukunci ne akan me laifi gwargwadon girman laifin sa, an karbo hadisi daga Abdullahi dan Abbas Allah ya kara masu yarda yace: wannan ayar ta sauka ne akan masu yakin Allah da manzon sa idan suka tare hanya idan sun kashe sannan suka kwace kudi sai atsire su, idan kuma kashewa kawai sukayi basu kwace kudi ba sai kasha sui dan sun kwace kudi ne kawai basu yi kisa ba sai a yanke masu masu hannu da kafa ta sabani watan idan an yanke hannun dama sai ayanke kafar hagu, idan kuma sun gudu ba'a iya kamasu ba to wannan shine Koran nasu daga kasa. Baihaki da daru khudny ne suka rawaito shi.
- Sannan kuma yasanya wa laifin ta'adi akan mutuncin mutane na kazafi bulala, Allah madaukaki yace: " wanda suke jifan mata kamammu sannan kuma basuzo da shedu hudu ba akan abunda suke jefe su dashi to kuyi masu bulala tamanin…."[175].
Lallai hadafin musulunci akan aiwatar da wannan haddin shine kiyaye mutuncin mutane da halaye daga cin zarafin su da kuma kiyaye harsunan mutane daga fadin duk abunda suke so na tuhumar mutane da aikata munanan abubuwa ba tare da tabbatarwa ba, kamar yadda babu shakka jifan mutane da zargi akwai cutar wa aciki me yawa da yake samun wanda aka masa kazafin, saboda kofar da zai bude ma mutane na keta mutuncin sa da maganganu cikin abunda bai dace ba, saboda mutunci a muslunci abune me matukar daraja, musulunci be tsaya ba kawai akan yin haddi ga me kazafi wanda hakan ukuba ce kawai da ya shafi jiki ya tanadar da ukuba ta zuciya wacce za'a yima me kazafi domin ya dandani dacin ta wanda hakan yake cire kawar masa da siffa ta adala baza'a amshi shedar sa ba sannan kuma an siffata shi da cewa yana cikin fasikai sai dai idan ya tuba tuba ta gaske, wa'innan abubuwa da akayi duka anyi ne domin kiyaye hakkokin mutane daga wasa dasu da keta su da Magana ne ko aiki, Allah madaukaki yana cewa: " wanda suke jifan mata kamulallu sa'annan basu zo da shedu guda hudu ba kuyi masu bulala tamanin sannan kuma kada ku kara amsar shedar su har Abadan, kuma wa'innan sune fasikai (4) sai dai wanda suka tuba bayan haka suka gyara halin su to lallai Allah me gafara ne me rahama (5)"[176].
- Ya sanya akan laifin ta'adi akan mutuncin mutane na zina bulala ga wanda be tabayin aure ba ko bata taba yin aure ba, Allah madaukai yace: " mazinaci da mazinaciya ku yima kowa cikin su bulala dari"[177].
Amma idan aka tabbatar da aikata zina ga wanda ya taba aure hukuncin su shine jifa har sai sun mutu a cikin shari'ar musulunci da sauran shari'u wanda suke daga Allah kamar yahudanci da kiristanci, amma ba'a aiwatar da wannan hukunci a musulunci na jifa sai an samu cikan sharudda masu wuyan gaske a ciki su, ba'a jefe mazina ci ko mazinaciya wanda suka taba aure sai cikin dayan halin nan guda biyu:
Hali na farko: idan mutum yayi ikirarin aikiata zina da bakin sa ba antilasta mata bane, haka kuma ba'a aiwatar da hukuncin akan mutumin dayayi ikirari sau daya sai yayi ikirari sau hudu a lokata daban daban a gaban alkali kuma ko wani lokaci idan yayi ikirarin sai alkalin ya bayyana masu rashin kyaun haka, sanann ikirarin baya wajabta haddi, sannan kuma bayan haka sai anta kwaban su da masu uziri ana cewa kila rungume ta yayi ko sunbata ko kuma taba ta kodai zai janye ikirarin sa, an karbo hadisi daga dan Abbas Allah ya kara masu yarda yace: lokacin da Ma'iz dan Malik yazo gun manzon Allah s.a.w sai manzon Allah s.a.w yace masa: " ko dai rungume ta kayi ko kuma kamata kayi ko kallonta kayi" sai yace: a'a ya manzon Allah, sai yace masa: " saduwa kayi da ita irin na aure?" be sakaya bay a fada masa a bayya ne daganan ne sai yayi umurni da aje ajefe shi" sahihul buhari.
Sannan idan suka gudu kafin a zartar masu da hukuncin ko kuma bayan amfara jefe su din wannan guduwa nasu yana matsayin sun janye daga ikirarin su kenan sai a kyale su, ankarbo hadisi daga Abu huraira Allah ya kara masa yarda yace: ma'iz al'aslami yazo wurin manzon Allah s.a.w yace masa: nayi zina, sai manzon Allah ya kawar da kansa kamar be jishi ba, sai ya kara biyoshi ta bangaren da ya koma da fuskar sa ya kara ce masa: nayi zina sai manzon Allah s.a.w ya kara kawar da kansa yayi kamar beji shi ba sai da ya maimata haka sau hudu sannan yayi umurni aje ajefe shi, lokacin da aka fara jefan sa da duwatsu sai ya gudu suka bishi har sai da suka kasha shi bayan sun dawo sai suke ba manzon Allah labarin cewa ya gudu daya farajin duwatsu sai manzon Allah s.a.w yace: " kasha i da kun bar shi lokacin da ya gudu" sahihi ibn Hibban.
Hali na biyu: a samu shedu guda hudu adilai wanda ake amsan shedar su suyi sheda akan cewa lallai sun gansu idao da ido ko wane cikin shedu hudun nan sai ya bada sheda shi dakai sannan dole halin da suka fada sun gansu yayi dai dai idan aka samu sabani cikin halin da daya yafada na shedu hudun anan to wannan sheda ta ruguje, wannan bazai samu ba sai idan zina ta koma a bayyane idan an manta da dokar musulunci da kuma wurgi da karantar wansa kafin za'a iya samun shedu hudu su gansu lokaci daya, haka kuma ba'a zartar da hakki idan ya kaance akwai wani shubuha kamar yadda muka ambata a baya.
Laifin zina ba laifi bane wanda ya shafi mazinacin da mazinaciyar kawai ba, laifi ne wanda ya shafi al'umma baki daya da keta hakkokin su, abubuwan da zina suke haifar wa suna da yawan gaske daga cikin su akwai:
- Zina tana yada mummanan dabi'a da lallata dabi'ar mutane wanda zai haifar masu da cututta na annoba masu matukar hatsari wanda zai shafi har wanda bashi da laifin komai akanta, manzon Allah s.a.w yace: " yaku taron masu hijira ku sani abubuwa guda biyar bazasu riske ku ina mai neman tsarin Allah da ku riski haka: alfasha(zina) bazai taba bayyana cikin al'umma suna masu tunkaho da ita face annoba da cututtaka sun yadu acikin su wanda ba'a taba ganin irinta ba cikin mutanen da suka gabata, sannan mutane bazasu rika tuye ma'aini ba face an sanya masu fari na rashin abinci da matsanancin talauci da shugaba azzalumi, sannan mutane bazasu hana zakkar kudin su face an hana masu ruwan sama badan dabbobin sub a baza'a taba masu ruwa, sannan mutane bazasu warware alkawarin Allah ba da manzon sa face an sshugabantar masu da wasu mutane wanda ba'a cikin su suke ba su rika kwace masu dukiyoyin su, sannan mutane bazasu bar yin hukunci ba da abunda Allah ya saukar da neman alheri da da ci gaba dashi ba face ansanya masu yaki a tsakanin su, suta kasha juna da azabtar da juna" sahihu ibn Hibban.
- Cudayan zuria cikin al'umma mutum be san babanshi ba ko kuma mamanshi, kuma za'a iya jingina mutum zuwa mutumin da bashi bane mahaifin sawanda hakan zai iya bashi gado da kuma hana wani me hakkin cin gado abashi gado, da kuma samun waya ya auri kanwar sa cikin rashin sani.
- Samun yara kara zube wanda basu da tarbiyya saboda kasancewar su basu da iyaye ko dangin da zasu jingana zuwa gare su wanda hakan zai iya haifar da yaduwar cututtuka masu hatsarin gaske ko kuma hakan ya zama sanadiyyar canza addinin sus u koma arna da haifar da rashin zaman lafiya da natsuwa ga al'umma.
- Sannan kuma aka sanya hukuncin laifin shan giya ko kuma duk wani abu makamancin ta wacce take gusar da hankali bulala, a musulunci mutum bashi da yancin ci da shan duk abunda yaga dama, akwai wasu nau'uka na abinci wanda aka haramta masa cin su kamar mushe da jini da naman alade da duk wani abu da aka yankashi ga wani Allah, wannan abubuwan da aka hanashi cin su basu da wani ukuba akan wanda yaci su a cikin shari'ar musulunci sai dai tuba da wanda ya aikata su zayyi zuwa ga Allah amma kuma duk wanda ya bayyana aikata hakan za'a masa ukuba na tsawatarwa wanda shugaba zai zartar masa gwargwadon maslahar al'umma baki daya, haka kuma mutum yanada iyaka cikin abubuwan shansa an haramta masa shan abunda zai cutar da lafiyar jikin sa, sannan kuma kasancewar giya laifin ta bawai akan mutum bane kawai ya tsaya laifi ne wanda ya shafi al'umma baki dayan su (saboda haka ne musulunci ya kirashi da suna ummul kaba'isa) wanda ya sanya masa ukuba na bulala, saboda musulunci yana kokarin kare hankulan da tunanin mutane daga dukkanin abunda zai kawar masu da hankali ko tunani ya mayar dasu kamar dabbobi, kadan daga cikin abubuwan da gusar da hanlaki yake haifar wa sune Kaman haka:
- Mutumin da yake cikin maye zai iya kisa da zina da ikata abubuwan da aka haramta be sani ba, an karbo hadisi daga Usman dan Affan Allah ya kara masa yarda yace: ku nesanci ummul kaba'isa saboda akwai wani mutum cikin mutanen da suka gabaceku wanda ya kasance me yawan bautan Allah da kauracewa mutane sai wata mata ta shirya masa makirci ta aika masa wani yaronta da cewa tana neman shi dan allah yazo yayi mata sheda, bayan yazo ya shigo cikin gidan ta sai tasa a rufe duk wata kofa daya wuce na gidan har sai da yazo gun wata mata tsirara a zaune sannan agefen ta akwai wani yaro da kofi na giya, sai matan nan tace masa bawai na kira ka bane dan kamun sheda kuma bazan kyaleka ba sai ka aikata daya daga cikin abubuwa uku dinnan ko ka kasha wannan yaro ko kayi zina da wannan mata ko kuma kasha giyan nan sai yaki aikata abubuwan nan guda biyun farko sai ya dau wannan kofi na giya ya sha bayan ya bugu hankalin say a fita sai ya kasha wannan yaro da yin zina da wannan mata duka abubuwan ya aikata su, saboda haka ku nesanci giya saboda wallahi imani baya dawwama da shan giya a zuciyar mutum har Abadan dole dayan su ya fitar da daya"[178].
- Mashayin giya ko kuma me shan abunda yake gusar da hankula yana zama mutum mara amfani ga al'umma sai dai ya rika jawo mata rashin kwanciyar hankali da ci baya imam dai ya siyar da mutuncin sa ko kuma yayi sata domin samun kudin shan wannan kayan maye nashi.
- Cutar da lafiyar mutum me matukar hatsari dashan wannan kayan maye din kamar yadda binciken ilimin likitancin ya tabbatar da cewa yana lalata hantar mutum.
- Barnatar da dukiya da lokaci cikin abunda bashi da amfani sai cutar wa kawai ga duk wani me hankali.
- Hana al'umma mafanuwa da dama da kwakwalwan mashiyin giya wanda hakan ta'adi ne ga hakkokin al'umma.
- Tana zubar ma mutum kwarjinin sa da kimar sa saboda tana gusar da hankalin mutum sai ta mayar dashi kamar dabba wanda bashi da wani kima, irin wannan abune wanda musulunci bata yarda mutane su zama haka ba.
Musulunci ya tabbatar da hukuncin ukuba wanda za'a rika kaddara sauran ukuba akansa sai Allah madaukaki yace: " sakamakon mummunan aiki shine mummunan aikin irin sa"[179].
Da kuma fadin sa madaukaki " idan aka cutar daku to ku rama dai dai da cutarwan da aka maku"[180].
Mu sani cewa muslunci be wajabta aiwatar da ukuba ba akan me laifi dole, ya sanya kofa abude na afuwa da yafiya cikin laifin daya shafi hakkokin mutum, saboda fadin Allah madaukaki " su rika yafiya da yan afuwa"[181].
Da kuma fadin Allah madaukaki har wayau cewa " duk wanda ya yafe kuma yayi gyara to ladan sa yana ga Allah"[182].
Lalai musulunci lokacin daya sanya wannan hukunce hukunce na ukuba bawai yana da manufar yada kiyayya bane da mugunta manufar sa shine kiyaye hakkokin mutane da samar da tsaro da kwanciyar hankali cikin al'umma da rufe kofa ga duk wani abu da zai hafar da wasa da zaman lafiya da tsaron al'umma da kuma tsarkake su daga mayagun laifuka, idan mutum ysan cewa idan yayi kisa fa shima kasha shi za'ayi, barawo yasan cewa hannu fa za'a yanke masa, mazinaci yasan cewa bulala za'a masa, me kazafi shima yasan cewa bulala za'ayi masa lallai zasu fasa aikata abunda sukayi niyya sai ya kubutar da kansa da mutane baki daya. Allah yayi gaskiya cikin fadin sa cewa: " kunada rayuwa cikin kisasi yaky ba'a bota hankula".[183]
Mutum zai iya cewa hakika wannan hukuncin da musulunci ya sanya na wasu laifuka babu imani aciki!! Sai ace masa lallai kowa sunyi ittifakin cewa laifuka ne wanda suke cutarwan su ga al'umma baya boyuwa sannan ya zama dole a sanya masa hukunci wanda zai hana aikata haka saidai kawai inda aka samu sabani shine wurin kayyade irin ukubar da za'ayi, saboda haka kowa ya tambayi kansa cewa shin wannan hukuncin na ukubar da musulunci ya sanya shi yafi dacewa wurin yaka da hana aikata laifuka ko kuma takaita aikata su ko kuma hukuncin da dan adam ya sanya sune sukafi???
Lallai hukuncin musulunci gai mutum dayayi masu na son rai zai iya ganin cewa babu tausayi a cikin sai dai hukunci ne na adalci wacce ta dace da zamanta kewar al'umma da kuma hikama ga duk me hankali, saboda Allah shine wanda ya hukunta haka sabanin hukuncin mjutum wanda zai iya zalumtar me laifi wurin hukunta masa ukuba. Duk wata gurbatacciyar gaba ya wajaba a yanke shi domin kiyaye sauran jiki wanda ha wadatu dashi dan lafiyar sauran, lallai duk wanda yake dauko sani daga mtane makiya musulunci ko wanda zai rika ganin cewa lallai al'ummar musulunci al'umma ce wacce ta ginu akan ayyukan rashin imani irin na dabbobin daji da son zubar da jinni sannan mutanen sa basu da kima kaga wani anyanke masa hannu wani kuma anjefe shi, wani kuma an masa bulala, suna tsammanin cewa wannan hukunce hukunce kullum ake zartar dashi, ya ishe mu hujja cewa duniyar muslunci bata taba ganin hukuncin haddi na jefe mutum ba sai akan mutum biyu kacal wanda sukayi ikirarin aikata zina da kansu, da kisatsa sauran ukubar akan wannan misali.
Shubuha ta hudu:
Lallai cikin aiwatar da hukuncin me ridda akwai take hakkin mutum cikin muslunci wanda ta kunshi yanci nayin addinin da mutum keso acikin ta sannan kuma hakan yaci karo da fadin Alllah madaukaki cewa: " babu tilastawa a addini"[184].
Raddi akan wannan shubaha:
Musulunci ya sanya hukuncin kisa ne ga laifin ridda saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: " duk wanda ya canza addinin sa yayi ridda ku kasha shi"[185]. Buhari ne ya rawaito shi, anan ya kamata mu kawo wasu Magana biyu karkashin wannan Magana:
- Hukuncin kisa ga me ridda anayin sa sa ne ga mutumin daya bayyana riddan sa sannan kuma yana kira da asabawa karantar wan muslunci da dokokin sa da zaburar da wasu yin ridda ana wurin kisan da akace ayi masa saboda wannan aiki nasa ne bawai dan riddan ba, saboda haka daya takaita da riddan sa akansa shi kadai be bayyana hakan ba ga mutane wannan hukuncin yana ga Allah saboda musulunci yana hukunci ne akan laifuka na bayyane amma laifukan da suke asirce babu wanda yasan su sai Allah.
- Dole ne a nemi wanda yayi ridda ya tuba na tsawon kwan uku wanda kullum za'a aika masa manyan malamai su masa wa'azai da tattaunawa dashi idan ya dawo hakan musulunci yake so idan kuma ya doge akan haka sai a kasha shi domin kiyaye sharrin sag a al'umma.
Lallai ridda tana wasa da addini da kuma karantarwan sa saboda haka musulunci bata yarda dashi ba kuma tana daukansa akan cewa yafi kafurci tsanani, Allah madaukaki yace: " lallai wanda suka yi imani sannan suka kafurta sannan suka kara yin imani sannan suka kara kafurta sannan suka kara kafurci akan haka Allah bazai gafarta masu ba sannan kuma bazai shiryar dasu ba hanya (137)"[186].
Me yasa ake kasha me ridda?
- Lallai ridda hanya ce ta da'awa a fili me matukar tsari ga mutumin dayayi ridda wanda zai rikayi sabanin muslunci zai rika munanawa mutanen sa da kuma hana wanin sa yin tunanin shiga muslunci, saboda halin sa kamar nuna cewa yake ya shiga musulunci ya jaraba sai yaga cewa addinin da ya gabace shi ya fice dacewa, wannan shine manufa na makiyan muslunci wanda suke shiga muslunci sa'annan su fita. Abaya ya kasance yahudawa suna shiga musulunci da burin ruguza shi, suna shiga musulunci ne domin yaudaran musulmai da kuma hana wasu shigan sa, Allah mabuwayi yace: " wasu daga cikin mutane ma'abota littafi sunce kuyi imani da abunda da aka saukar masa da na rabin yini sannan ku kafirta a karashen yinin koda zasu dawo daga rakiyar sa (72)" suratu al'imran.
- Lallai musulunci yanason mutum idan zai shige shi ya shiga cikin zabin sa da tunanin sa da kyautat niyyar sa, sannan idan aka samu bayan bibiyan addinin musulnci da karanta shi ya gamsu yaji yanason shiga musulunci sai ya shiga, idan kuma be gamsu ba ba'ace ya shiga ba da niyyar fita daga baya domin wasa da imani da kuma hana wanin sa shiga musulunci.
- Musulunci baya daukan ridda akan matsalatr mutum ne shi kadai koda kuma hakan ne ya bayyana, saboda ridda daga musulunci bawai kawai canza akidar mutum bane a'a idan yayi ridda ya fita daga cikin tsarin ta sannan fitan nan nashi zai zama sababi na lalata wannan tsari, saboda haka cutar wan bawai akan mutum bane kadai zai tsaya zai shafi al'umma ne baki dayan su, saboda haka musulunci yana kallon laifin ridda ne a matsayin tarzomar cikin gida kamar yadda muka fada a baya, wannan abu musulunci baya yarda dashi kasancewar musulunci ba kamar sauran addinai bane wurin tsari, duk wanda ya sabawa dokokin sa sannan yayi kokarin canzata da juya ta da haifar mata da rudani acikinta sai a zartar masa da hukunci na kisa.
Shubuha na baiyar:
Haramtawar da musulunci yayi na wanda ba musulmi ba ya auri musulma akwai taka hakkin dan adam a ciki saboda an hanata yancin ta wanda zai bata damar auren wanda takeso!!
Raddi akan wannan shubuha:
Muslunce bawai ya hana hakan bane domin toye hakkin mutum na auren wanda yake so saboda sabanin addini ya yana haka ne saboda kare iyali daga samun matsala na zamantakewa saboda banbancin addini idan aka samu rashin girmama akidar matar tashi, saboda mace daya daga cikin shikashikan iyalai ne wacce tafi tasirantuwa da wannan yanani kasancewar ta me rauni akarkashin namiji.
A karkashin haka akwai hali guda uku wanda hukuncin su ya banbanta amma dai dukan su Magana day ace kamar yadda mukayi bayani a abaya, wannan hali sune:
Hali na farko: namiji musulmi ya aure mace arnina me bautar gumaka wacce batayi imani ba da Allah, musulunci ya haramta wannan aure saboda akidar mijin na musulunci bazai taba yiwuwa ba ya daraja akidar matar shi wanda hakan zai haifar da fada da tashin hankali tsakanin yalai, sannan musulunci yana daukan saki a amtsalan mafi munin ayyuka halal a wurin Allah saboda haka ne ma yasa baya karfafa aiwatar dashi, saboda hake ne sai ya haramta irin wannan aure wanda mijin bazai daraja akidar matar shi ba wanda hakan zai kare da rigama atsakanin su.
Hali na biyu: auren mace kirista ko kuma bayahudiya wanda musulunci ya halasta haka, saboda musulunci yana daraja annabtar annabi isah amincin Allah ya kara tabbata agareshi sannan kuma yana dajara annabtar annabawan bani isra'il saboda haka ne mace kirista ko kuma bayahudiya zata kiya tsayawa akan addininta batare da sun samu sabani ba da mijin akan haka, saboda musulunci ya yarda kuma yana daraja sauran annabawan da suka gabata daga Allah, shine wannan hali babu abunda zai haramta irin wannan aure a musulunci dukda kuma akwai banbancin addini.
Hali na uku: namiji kirista ko kuma bayahude ya auri mace musluma wanda muslunci ya haramta haka saboda auren namiji kirista ko kuma bayahude wanda be yarda da annabtar Muhammad ba s.a.w, yana me kyamar akidar matar da Magana me muni akai wanda zai hana mace musulma auren sa sannan kuma ya haifar da rikici tsakanin ma'aurata da rabuwa saboda haka ne musulunci ya haramta auren da zai kare da haka.
Shubuha na shida:
Samun bayi acikin muslunci yana cin karo da da'awar musulunci na samun dai-daiko tsakanin mutane wanda mutane zasu koma zuwa ga asali daya dukan su, a cikin haka akwai toye hakkin dan adam!
Raddi akan wannan shubuha:[187]
Yana da kyau mu bayya a farkn wannan wuri ba tare da tsawaita w aba cewa tabbatar da bayi cikin musulunci ya faru ne domin matsalar tattalin arziki da zaman takewa wanda ta jayo haka, dalili da cewa al'ummar da muslunci ya bayyana acikin su suna rayuwa ne da bayai cikin sawwake rayuwan mutane na tattalin arzikin su da zamanta kewar su bawai ga larabawa bane kawai akasan wannan abu duka duniya suke da bayi a lokaci, kuma dukkanin addinai suna amfani dashi kamar yadda yazo cikin tsohon alkawari bibiya na shirin: idan ka kusance wani gari domin yakar su ka fara kiran su zuwa ga sulhu idan sun amince da sulhun ka bude garin to dukkanin mutanen garin masu maka hidima ne da kuma bautar dasu, idan basu amince maka ba da yin sulhu sai dai yaki kayi masu kawanya idan ubangijin ka ya baka nasarar kama garin ka kasha dukkanin mazajen su da takobi, sauran matan su kuma da yara da dabbobi duk ganima ne a gare ka kayi amfani dasu kuma kaci ganimar makiyar ka da ubangijin ka ya baka, haka zaka aikata ga sauran garuruwa masu nisa daga gare ka, ba garuruwan mutanen nan ba, shi kuma garuruwan wannan mutane wanda ubangijin ka ya baka kyauta kada kabar wani abu acikinta ka haramta su haramtawa.
Muslunci yabi mataki mataki wurin hana bauta na baya kamar yadda yayi wurin hana shan giya domin sabon ta da mutane sai be haramtata ba lokaci daya ya haramtata mataki mataki, matakin farko shine fadin sa madaukaki: " suna tambayan ka game da giya da caca, kace masu suna da dan amfani ga mutane amma barnan su yafi amfanin su yawa"[188].
Bayan mutane sun amsa wannan kira da aka masu da yin karfi cikin muslunci sai aya ta sauka da cewa: " yaku wanda sukayi imani kada ku kusanci sallah alhali kuna cikin maye har sai kunsan abunda kuke fadi"
Sannan bayan haka imani yayi karfi a zukatan mutane da amsar kiran musulunci da karantarwan sa da bin umrnin Allah da manzon sa da gabatar dasu akan komai sai haramcin giya ya sauka baki daya, Allah madaukaki yace: " yaku wanda sukayi imani hakika giya da caca da dara da rantsuwa da gumaka datti ne cikin ayyukan shedan saboda haka ku nuisance su koda zaka rabauta (90)".
Musulunci yayi amfani da bin hanya irin ta giya wurin haramta shi, be hana ayyukan bauta ba kai tsaye lokaci guda ba yata bin hanyoyi ne na hikima daki bayan daki na rage masa karfi domin wani lokaci ya haramta shi baki daya, ta yadda ya fara da matakin farko: ya fara himmatuwa da nuna halin da suke ciki na rauni da tawayan yanci yadda ya fara dawo masu da martaba da yancin su na mutane ya kuma sanya su suka zama yan uwa ga iyayen gidan su, saboda bauta a musulunci baya cikin musulunci tun farko bijiro masa yayi sai manzon Allah s.a.w yace: " yan uwanku masu maku hidima wanda Allah yasanya su karkashin ku, saboda haka duk wanda dan uwansa ya kasance karkashin say a rika ciyar dashi daga irin abincin dayake ci ya kuma tufatar dashi da irin tufar daya ke sanyawa, kuma kada ya rika sanya shi aikin daya fi karfin sa, idan kuma yasashi aikin dayafi karfin sa to ya taimaka masa" bugari ne ya rawaito shi.
Sanan yayi umurni da kyautata masu da tausaya masu da kuma rangwanta masu cikin Magana da aiki, sai Allah madaukaki yace: " ku bautawa Allah kada ku hanada shi da wani cikin bauta kuma ku kyautata wa iyaye da yan uwanku da marayu da miskinai da makwabta cikin yan uwa da makwabta na wurin zama da aboki na kusa da matafiyi da abunda kuka mallaka na bayi, lallai Allah bayason marowata kuma masu wayan alfari (36)"[189].
Musulunce be tsaya nan ba yayi kokarin karrama matsayin su da halin da suke ciki, sai ya hana dukkanin abunda zai zam sanadin da zai tuna masu da haln da suke ciki inda manzon Allah s.a.w yace: " …. Kada dayan ku yace bawa ko kuma baiwata maimakon haka yace yaro na da yarin ya ta"[190]. Buhari ne ya rawaito shi.
Sannan kuma me karatu ka sani cewa bauta a musuluci fan a ganagan jiki ne kawai banda hankali da tunani domin kuma bawa yanada yancin tsayawa akan addinin daya ke so haka musulunci yabar misali babba wurin dai-daito a matsayin sun a yan adam da iyayen gidan su yasanya falalar wani akan wani a tsakanin su shine yawan tsoron Allah a lokacin daya kulla yan uwantaka tsakanin iyayen gidan su da su bayin, sannan kuma ga babban misali wanda yafi wannan shine manzon Allah s.a.w wanda yafi kowa daraja da matsayi ya auri yar baffansa Zainab diyar Jahshin daga wurin bawan sa me masa hidima Zaid, kamar yadda ya ayyana shi akan shugabancin sojojin yaki kuma akwai manyan sahabbai acikin rundunar.
Musulunci yayi amfani da hanya guda biyu wurin hana bauta ta hanyar da bazai harfar da damuwa ba ko dimuwa ko matsala da haifar da kiyayya da kuma haifar da cikas ga tattalin arziki da zamanta kewar mutane:
Hanya ta farko: ya takaita hanyoyin samun bawa bayan da sun kasance hanyoyi nasu tarin yawa daga cikin su akwai:
- Yaki ta dukkanin bangarorin ta ya kasance sojojin yaki wanda aka ci galaba akan su basa wuce daya cikin hali biyun nan kodai a kasha su ko kuma bautar dasu.
- Idan mutum ya kasa biyan bashin da ya amsa agun wani sai ya bautar dashi saboda wannan bashi.
- Ikon iyaye akan yaran su wanda ta basu damar sitar dasu maza ne ko mata.
- Mutum ya janye daga hakkin san a yanci wanda zai iya sayar da kansa da wani kudi sananne.
- Idan mutum ya aikata babban laifi kamar kisa ko zina ko sata sai a hukuntashi ta hanyar mayar dashi bawa ga wanda yama laifin ko yan uwan sa.
Wa'innan sune wasu daga cikin hanyoyin bautar da mutane wanda musulunci yazo ya tarar da mutane akan sa sai ya haramta su dukanku sai yabar guda daya kacal watan bayin da aka samu ta hanyar yaki na shari'a wanda imam ya bada izini da umurnin yenta, sannan kuma ka sani cewa fursinonin yaki basa zama bayi kai tsaye har sai idan shugaba ya bautar dasu, saboda ba dukanin fursinonin yaki bane a musulunci suke zama bayi domin akwai fursinan da za'a sake shi kyauta ba tare da ya biya komai ba ko kuma ayi masanyan sa da wani fursinan musulmai ko kuma su fanshi kan su da kudi bayan gama yaki, saboda fain Allah madaukaki cewa: " ko dai ku saki wasu daga cikin su ko kuma kuyi matsanya dasu da wasu fursinoni musulmai har yaki ya kare.."
Hikiman haka shine kada a saki fursinonin yaki na makiyan da aka kama alhali kuma fursinonin yakin musulmai na hannun su, saboda haka sai ayi masu mu'amala dai dai dana su.
Hanya ta biyu wanda musulunci yabi domin hana bauta da bayi shine: yawaita hanyoyin yanta bayi bayan ya takaita hanyar samun su ya koma hanya daya, da zarar ubangidan bawa yayi kwadayin yanta shi ya zama wajibi akan sa da iyalan sa har illa masha Allah, musulunci ya sanya rabuwa da bauta ya zama ta hanya biyu kodai ta hanyar yantawa ko kuma hanyar yarjejejiya.
- Yanta bawa: musulunci ya sanya kofofi dayawa na yanta bawa bayan da ya kasance hanya day ace kawai watan idan ubangida yayi kwadayin yanta bawan sa, daga cikin wannan kofofi nay anta bawa akwai:
- Kaffara na wasu zunubai, musulunci ya sanya kaffarar kisa bias kuskure biyan diyya ga iyalan wanda aka kasha da kuma yanta wuya mumina, saboda fadin Allah madaukaki: " baya halatta da mumini ya kasha wani mumini sai bisa kuskure, duk wanda ya kasha wani mumini bisa kuskure sai yay anta wuya mumina da kuma biyan diyya ga iyalan sa sai dai idan sun yafe masa"[191].
- Sannan ya sanya yanta bawa ya zama kaffaran zihari (zihari wani nau'i na na saki a gun larabawa kabanin zuwan muslunci yadda mutum yake yi domin jingine matar sa be sake ta bare taje tayi wani auren kuma baya kusantar ta a matsayin matar sa ta aure, sai musulunci ya haramta wannan zalumci ga mata), saboda fadin Allah madaukaki cewa: " wanda suke zihari ga matayen su sa'annan kuma basu yanje abunda suka fad aba, to su yanta wuya kafin su kusance su, da haka ne ake maku wa'azi dashi, Allah me bada labara ne game da abunda kuke aikata wa (3)"[192].
- Sannan kuma ya sanya yanta bawa kaffara na rantsuwa, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " Allah yaba kamaku da laifi akan rantsuwar kun a kubutan harshe ko kuma wanda kuka saba dashi, yan kamaku ne kawai akan rantsuwar da kukayi da gangan, kaffaran haka shine ku ciyar da miskinai goma daga matsakaicin irin abincin ku ko kuma ku tufatar dasu ko yanta bawa, duk wanda be samu daya daga cikin haka ba sai yayi azumin kwana uk, wannan shine kaffarar rantsuwar ku idan kun rantse, ku kiyaye rantsuwar ku"[193].
- Sannan kuma ya sanya yanta bawa ya zama kaffara yin jima'a cikin yinin Ramadan, saboda kisser sahabin daya zo gun manzon Allah s.a.w yace masa: ya manzon Allah na halaka! Sai yace masa me "yasameka haka" sai yace: nayi jima'I ne da matata cikin yinin azumi sai manzon Allah s.a.w yace masa: " kana da bawa?" sai yace: a'a bani dashi ya manzon Allah, sai manzon Allah s.a.w yace masa: " zaka iya azmunin wata biyu to a jere?" sai yace: a'a bazan iya ba, sai manzon Allah s.a.w yace masa: " to kanada abinci ka ciyar da miskinai sittin? " sai yace bani dashi ya manzon Allah, sai manzon Allah yayi shiru ya yaci gaba da zama sai aka kawo mashi kwarya na dabino sai yace ina wannan mutumi yake me tambaya?" sai yace ganinan ya manzon Allah, sai yace masa to dauki wannan kaje kayi sadaka dashi" sai yace yanzu ya manzon Allah har akwai wanda yafini bukatar sadaka ne kafaf fadin garin nan? Sai manzon Allah s.a.w yayi dariya har hakorin say a bayyana sai yace masa: "to dauka kaje ka ciyar da iyalanka!"[194]. buhari ne ya rwaito shi.
Musani cewa duk wanda daga daga cikin wannan kaffara ya wajaba akansa idan bashi da bawan yantawa amma yana da kudin siyan bawan dole ne yasiyo bawa yay anta shi.
- Muslunci ya sanya yanta bayi cikin manyan ayyukan neman kusanci a wurin musulmi zuwa ga ubangijin sa, Allah madaukaki yace: " fansar kai daga Akaba (11) me ya sanar dakai abun da ake cema akaba(12) shine yanta wuya (13) ko kuma ciyar wa cikin wani rana ga mabukaci (14)[195]
Maganganun manzon Allah s.a.w da ayyyukan sa suna tunatar da bayar da yanci ga bayi, shine wannan da yake dafin cewa s.a.w: " duk wanda yay anta bawa domin Allah, Allah zai yanta duk data gabar jikin sa da gabban jikin bawan daya yanta hatta farjin sa zai yanta shi da farjin sa"[196]. Buhari da muslim ne suka rawaito shi.
- Alkawari da barin wasiyyar cewa idan mutum ya mutu bawanshi ya zama yantacce, domin musulunci yak are hakkin bawa cikin wannan hali sai ya haramta siyar dashi ko kuma bayar dashi kyauta ga wani.
- Musulunci ya sanya cikin mutanen da ya halatta a basu zakka bawan da yayi yarjejeniyan bawa ubangidan wani kudi ya yanta shi, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " ita zakka ana bayar da ita ne ga fakirai da miskinai da masu aikin tattara ta, da wanda ake lallashin zukatan su, da bawan da yayi yarjejeniya da ubangidan sa akan wasu kudi yay anta shi da wanda ya daukan ma kansa biyan wani kudi domin raba fada tsakanin mutum biyu da me jihadi domin daukaka Kalmar Allah, da matafiyi, wannan wajibi ne daga Allah, Allah ya kasance masani kuma me hikima (60)"[197].
- Musulunci ya sanya dukan bawa ko kuma marin sa cikin sababin yanta shi, saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa: "duk wanda ya mari bawan sa ko kuma ya duke shi to kaffaran haka shine yay anta shi" muslim ne ya rawaito shi.
Shi kuma yarjejeniya domin yanta bawa (al mukataba): shine bawa ya nemi ubangidan sa daya siyar masa da yancin kansa akan wasu kudi wanda zasuyi ittifaki akai, duk lokacin da bawa ya nemi wannan yarjejeniya daga me gidan say a zama wajibi akan me gidan nasa daya yarda, danan kuma bawa yana da hakkin yin kasuwanci ko aikin karfi domin samun abunda zai biya wannan yarjejeniya, daganan aikin da zai ma me gidan sai ya biya shi, sannan kuma musulunci bugu da kari ya kwadaitar da musulmai da su taimakama irin wannan bawa da zakka da sadaka daga wurin ubangidan nashi da sauran muslumai domin ya samu ya biya kudin saboda fadin Allah madaukaki: " wanda suke nemi ku yanta su akan su biyaku wani kudi cikin bayin to ku yarda da haka idan kunga alheri a tattare dasu, kuma ku basu daga cikin dukiyar Allan daya baku"[198].
A takaice zamu iya cewa muslunci be hukunta bauta ba face zuwa yayi da dokoki da tsari wanda zasu takaita hanyoyin samun bayi.
Hakika ma'aikatar shari'a ta kasar saudiya ta tsara wani taron wayar da kai na kwana uku cikin watan safar na shekara 1392 na hijira, da yawan malamai da malaman jami'un cikin kasar da manyan malamai masana kundin tsarin mulki daga kasashen turawa guda hudu:
- Minister harkokin waje na kasar ire-land na wannan lokaci da sakataren kungiyar turawa masa tsara hukunce hukunce.
- Daga daga cikin masu ra'ayin yamma kuma daya daga cikin malai na bangaren karatun musulinci.
- Daga daga cikin malamai na kundun tsarin mulkin duniya kuma shugaban mujallar cikin kasa domin hare hakkokin dan adam wanda ake yinta a kasar faransa.
- Daga cikin manyan lauyoyi na kotun daukaka kara na kasar farisa.
Malaman kasar saudiya sunyi bayanin akan addinin musulunci a wurin musulmai da wand aba musulmai ba sannan kuma suka yi bayi dalla dalla acikin san a dokoki da ka'idoji na shari'ar musulunci gama gari wanda basa canzawa da kuma hukunce hukunce kanana sannan kuma sukayi bayanin cewa shari'ar musulunci tazo ne domin kare maslahar ta hakika ga mutane cikin dokokinta da bayanin hukunce hukuncen ukuba na cikin shari'ar musulunci wanda aka sanya su akan aikawa wasu laifi masu hatsari siyasa ce domin kiyaye rayukan mutane da han yaduwar kasha kasha da kiyaye mutuncin mutane da dukiyoyin su, kuma hakika bakin d aka gayyato daga kasashen turawa sun bayyana mamakin su akan abubuwan da sukaji akan shari'ar musulunci yadda hakkokin dan yake yake aciki, sai shugaban tawagar me suna Mark Brayid yace: daga nan wurin cikin wannan gari na muslunci ya wajaba a shelanta hakkokin dan adam bawai daga wani kasa ba sannan kuma ya wajaba akan malaman musulmai su shelanta wannan hakkoki wanda duniya ta jahilci haka kuma jahiltan su ya zama sababin muzanta kawun musulunci da musulmai da kuma hukunci da musulunci.[199]
JAWABIN KARSHEN LITTAFI:
A karshen wannan dan karamin littafi zany a fadi cewa ban kaucewa gaskiya ba idan nace dukkanin abun da yake cikin wannan littafi na bayani akan hakkokin dan adam soman tabi ne kawai cikin musulunci, sannan kuma zasu zama mabudi da kuma kwadaitar da neman Karin sani ga duk wanda ya karanta wannan littafi akan girman musulunci wanda aka bata masa suna da siffa daga wurin mutane dayawa makiyan sa wanda suka shiga musulunci domin bata masa suna, sannan kuma wannan kira ne ga duk wand aba musulmi ba wanda ya karanta wannan littafi da yasanya wani bangare da lokaci nasa na karatu game da addinin musulunci, sannan wannan littafi ya zaman masa hujja daga biani sai ya kwatanta abunda ya karanta cikin wannan littafi da wanda yaji yagani wane ne yake shiga zuciya ya kuma canza karya, kuma ya sani cewa bamu da wani manufa ta kashin kai ko amfanin kai ko kuma neman wani abun duniya wurin kiran mutane zuwa ga wannan addini na muslunci sai kawai don son alheri ga mutane. Hakika addinin musulunci tun lokacin daya bayyana bazai gushe ba ana yaki dashi har zuwa wannan zamani namu daga bangaren mutanen da suka saba masa da kuma hassada wanda suka sha alwashin ganin sunyi duk abun iyawa da kudin da lokacin sun a yakan sa amma tattare da haka basu iya kawo wani shubuha ba akansa wanda zasu sashi yayi rauni warin duk wani me hankali me lafiya da zuciya me gani, sannan mutanen da ba musulmai masu hankali da banbancewa tsakanin karya da gasjiya bazasu gushe ba suna shiga cikin wannan addini hadda manya manyan malaman wasu addinai, duk wannan be isa zama hujja ba akan girman wannan addini da cewa kuma shine addini na gaskiya kuma daga wurin Allah yake wanda yayi alkawarin kareshi? Cikin fadin sa cewa: " lallai mu muka saukar maka da alkur'ani kuma mune zamu kare shi (9)" zamu rufe maganar mu cikin wannan littafi da maganar manzon Allah s.a.w wanda ya bayyana son alheri ga mutane: " mafi soyuwan mutane a wurin Allah shine wanda yafi amfanar dasu, sannan kuma mafi soyuwan aiki agun Allah shine sanya farin ciki a fuskar mutum musulmi ko kuma ka yaye mashi damuwar sa ko kuma ka biya masa bashin sa ko ka kore masa yunwa, kuma yafi soyuwa a wurina na fita wurin biyan bukatar dan uwana musulmi sama da inyi ittikafin wata daya cikin wannan masallaci nawa, duk wanda ya kame fushin Allah zai rufa masa asiri, kuma duk wanda ya hadiye fushin sa wanda daya ga dama zai aiwatar dashi Allah zai cika zuciyar sa da yarda ranan alkiyama, duk wanda ya fita wurin biyan bukatar dan uwan sa har hakan ya tabbata Allah zai tabbatar da duga dugan sa ranan da duga dugai suke girgiza, kuma lallai mummunan mu'amala yana lallata ayyukan bawa kamar yadda madaci ko kal yake bata zuma"[200].
www.islamland.com
[1] Suratul isra'I ayata 70
[2] Suratul an'am ayata 165
[3] Sunan abi dawud, mujalladi na 3, shafi na 210, lambar hadisi na 3199
[4] Sahihu m uslim, juzi'I na biyu, shafi na 667, lambar hadisi na 971
[5] Sunan abi dawud, mujalladi na 4, shafi na 275, lambar hadisi na 4900
[6] Sunan abi dawud , mujalladi na 4, shafi na 336, lambar hadisi na 5142
[7] Bidaya wannihaya na ibn kasir, mujalladi na 8, shafi na 64
[8] Suratun nisa'I ayata 75
[9] Sunan albaihaqi, mujalladi na 9, shafi na 205, lambar hadisi na 18511
[10] Sahihul buhari, juzi'I na 10, fathul bari, shafi na 568, lambar hadisi na 6043
[11] Suratun nisa'I ayata 29
Suratul an'am ayata 151[13]
Sahihu muslim, mujalladi na 3, shafi na 1588, lambar hadisi na 2003[14]
Dabari ya rawaito shi cikin targib da tarhib[15]
[16] Sahihul buhari, mujalladi na 6, shafi na 2592, lambar hadisi na 6661
[17] Sahihul buhari, mujalladi na2, shafi na 535, lambar hadisi na 1402
[18] Sahihul buhari, mujalladi na2, shafi na 505, lambar hadisi na 1331
[19] Suratul mujadala ayata 11
[20] Sunan ibn majjah, juzi'I na 1, shafi na 81, lambar hadisi na 224
[21] Sahihu muslim, mujalladi na 4, shafi na 2074, lambar hadisi na 2699
[22] Sahihu ibn hibban, mujalladi na1, shafi na 298, lambar hadisi na 96
[23] Suratul ma'ida ayata 90
[24] Suratul ma'ida ayata 3
[25] Suratul isra'I ayata 32
[26] Sahihul buhari, mujalladi na 5, shafi na 2163, lambar hadisi na 5396
[27] Sahihul buhari, mujalladi na 5, shafi na 2177, lambar hadisi na 5437
[28] Sunan altirmizi, juzi'I na 4, shafi na 574, lambar hadisi na 2346
[29] Suratun nisa'I ayata 1
[30] Musnad na imam Ahmad, mujalladi na 5, shafi na 411, lambar hadisin na 23536
[31] Sunan altirmizi mujalladi na 5, shafi na 389, lambar hadisi na 3270
[32] Suratul ma'ida ayata 18
Wata mata daga cikin manyan kabilar kuraishawa [33]
[34] Sahihul buhari, mujalladi na 3, shafi na 1282, lambar hadisin na 3288
[35] Ahkamul sultaniyya na abu ya'ala, shafi na 222
[36] Suratu tabarak ayata 15
[37] Suratul an'am ayata 132
[38] Sunan annisa'I, mujalladi na 7, shafi na 82, lambar hadisi na 3986
[39] Suratul bakara ayata 179
[40] Suratn nisa'I yata 93
[41] Suratun nisa'I ayata 29
[42] Suratul a'araf ayata 32
[43] Suratul a'araf ayata 31
[44] Sahihul buhari, mujalladi na 5, shafi na 1949, lambar hadisi na 4776
[45] Suratul ma'ida ayata 90-91
[46] Sunan ibn majjah, mujalladi na 2, shafi na 1121, lambatr hadisi na 3380
[47] Suratul isra'I ayata 32
[48] Sahihu ibn hibban, mujalladi na 10, shafi na 269, lambar hadisi na 4422
[49] Sahihul buhari, mujalladi na 5, shafi na 2005, lambar hadisi na 4935
[51] Suratul hujurat ayata 11-12
[52] Suratul ma'ida ayata 38
[53] Suratul bakara ayata 188
[54] Musnad na imam Ahmad, mujalladi na 1, shafi na 416, lambar hadisin na 3946
[55] Sahihul buhari, mujalladi na 2, shafi na 877, lambar hadisi na 2348
[56] Suratul bakara ayata 205
Sahihu ibn hibban, mujalladi na 9, shafi na 338, lambar hadisi na 4028[57]
[58] mustadrak ala sihihain, mujalladi na 4, shafi na 178, lambar hadisi na 7284
[59] Suratul ahazab ayata 4-5
[60] Sahihul buhari, mujalladi na 2, shafi na 852, lambar hadisi na 2289
[61] Sahihu muslim, mujalladi na 1, shafi na 82, lambar hadisi na 2609
[62] Sunan ibn majjah, mujalladi na 2, shafi na 870, lambar hadisi na 2609
[63] Mustadrak ala sahihain, mujalladi na 3, shafi na 287, lambar hadisi na 5117
[64] Suratul isra'I ayata 26-27
[65] Suratu duha ayata 10
[66] Mustadrak ala sahihain, mujalladi na 4, shafi na 197, lambar hadisi na 7353
[67] Sahihul buhari, mujalladi na 1, shafi na 418, lambar hadisi na 1183
[69] Suratul an'am ayata 151
[70] Suratul jasiya ayata 12-13
[71] Suratun nisa'I ayata 1
[72] Sahihu muslim, mujalladi na 4, shafi na 1986
[73] Suratul a'araf ayata 54
[74] Suratul a'araf ayata 180
[75] Suratu shura ayata 11
[76] Suratul anbiya'I ayata 25
[77] Suratu gafir ayata 60
[78] Suratul ankabut ayata 45
[79] Suratu taubah ayata 103
[80] Suratul bakara ayata 183
[81] Suratul hajji ayata 28
[82] Suratul bakara ayata 185
[83] Sahihu muslim, juzi'I na 4, shafi na 1830, lambar hadisi na 1337
[84] Suratu al'imran ayata 97
[85] Suratul bakara ayata 172
[86] Suratun nisa'I ayata 80
[87] Suratun najmi ayata 3
[88] Suratul hashri ayata 7
[89] Sahihi muslim, mujalladi na 3, shafi na 1343, lambar hadisi na 1718
[90] Suratun nisa'I ayata 150-151
[91] Suratu saba'I ayata 28
[92] Suratul bakara ayata 256
Suratul isra'I aata 23[93]
Sahihu ibn hibban, mujalladi na 2, shafi na 172, lambar hadisin na 429[94]
Sahihu muslim, mujalladi na 2, shafi na 696, lambar hadisi na 1003[95]
Sahihu muslim , mujalladi na 4, shafi na 1974, lambar hadisi na 2548[96]
Suratu ahkaf ayata 15[97]
Suratun nisa'I ayata 34[98]
Sunan ibn majjah, mujalladi na 1, shafi na 594, lambar hadisi na 1851[99]
[101] Sunan abi dawud, mujalladi na 2, shafi na 242, lambar hadisi na 2133
Suratu dalak ayata 7[102]
Sahihul buhari mujalladi na 3, shafi na 1431, lambar hadisi na 3721[103]
Sahihul buhari, mujalladi na 5, shafi na 2052, lambar hadisi na 5049[104]
[105] Sahihul buhari, mujalladi na 5, shafi na 2347, lambar hadisi na 6024
[106] Sahihu muslim, mujalladi na 2, shafi na 1060, lambar hadisi na 476
[107] Sahihu ibn hibban, mujalladi na 9, shafi na 483, lambar hadisi na 4176
[108] Sahihu muslim, mujalladi na 2, shafi na 1-91, lambar hadisi na 1469
[109] Suratut tahrim ayata 6
[110] Sahihi ibn hibban, mujalladi na 10, shafi na 51, lambar hadisi na 4240
[111] Sahihu ibn hibban, mujalladi na 13, shafi na 135, lambar hadisi na 5818
[112] Sahihul buhari, mujalladi na 2, shafi na 902, lambar hadisi na 2419
[113] Sahihu muslim ,mujalladi na 4, shafi na 2304, lambar hadisi na 3009
[114] Sahihu muslim, mujalladi na 3, shafi na 1241, lambar hadisi na 1623
[115] Suratun nisa'I ayata 1
[116] Sahihul buhari, mujalladi na 5, shafi na 2233, lambar hadisi na 5645
[117] Sahiul buhari, mujalladi na 6, shafi na 2725, lambar hadisi na 7063
[118] Suratun nisa'I ayata 59
[119] Suratu daha ayata 14
[120] Sahihu muslim, mujalladi na 3, shafi na 1480, lambar hadisi na 1852
[121] Sahihu muslim, mujalladi na 1, shafi na 125, lambar hadisi na 142
[122] Suratu al'imran ayata 159
[123] Al mustadraka ala sahihain, mujalladi na 4, shafi na 105, lambar hadisi na 5668
[124] Sahihu muslim, mujalladi na 3, shafi na 1458, lambar hadisi na 1828
[125] Suratun nisa'I ayata 36
[126] Al mustadrak ala sahihain, mujalladi na 4, shafi na 184, lambar hadisi na 7305
[127] Sahihul buhari, mujalladi na 5, shafi na 2239, lambar hadisi na 5668
[128] Suratu zariyat ayata 19
[129] Suratul bakara ayata 177
[130] Suratu tauba ayata 34
Suratu tauba ayata 60[131]
Suratu al'imran ayata 180[132]
Sahihul buhari,mujalladi na 1, shafi na 20, lambar hadisi na 30[133]
Sunan abi dawud, mujalladi na 2, shafi na 817, lambar hadisi na 2443[134]
Sahihu muslim, mujalladi na 3, shafi na 155o, lambar hadisi na 1958[135]
Sahihu ibn hibban, mujalladi na 12, shafi na 434, lambar hadisi na 5617[136]
Suratul isra'I ayata 70[137]
Suratul ma'ida ayata 72[138]
Suratul ahzab ayata 58[139]
Suratun nur ayata 27-28[140]
Suratun nahli ayata 90-91[141]
Suratu mumtahana ayata 8[142]
Suratul an'am ayata 108[143]
Suratu al'imrana ayata 64[144]
Suratul a'araf ayata 56[145]
Surat yunus ayata 99[146]
Suratu shura ayata 38[147]
Suratu al'imran ayata 159[148]
Suratun nisa'I ayata 75[149]
Alkharaj li abi yusuf, shafi na 175[150]
Suratu fussilat ayata 46[151]
Suratu ma'ida ayata 78-79[152]
Hukukul insan fil islam, dakta Muhammad azzuhaili, shafi na 400[153]
Suratul hujurat ayata 13[154]
[155] Muktabis minal bayanil islamy al'ilmy li hukuk al'insan
[156] Suratul jasiya ayata 13
[157] Suratu shura ayata 38
[158] Suratun nahli ayata 125
[159] Suratun nur ayata 19
Suratul anbiya'I ayata 107[160]
Suratu yunus ayata 99[161]
Suratul ma'ida ayata 5[162]
Suratul mumtaha ayata 8[163]
Suratul mumtahana ayata 9[164]
Suratul ankabut ayata 46[165]
Suratul ahkaf ayata 4 [166]
Tarjamatu Husain Ibrahim wa abdul majid abid wa isma'il al nahrawy[167]
Al mustadrak ala sahihain, mujalladi na 4, shafi na 426 [168]
Suratul bakara ayata 178 [169]
Suratul bakara ayata 178 [170]
Suratul bakara ayata 178 [171]
Suratun nisa'I ayata 92 [172]
Suratul ma'ida ayata 38 [173]
Suratul ma'ida ayata 33 [174]
Suratun nur ayata 4-5 [176]
Suratun nur ayata 2 [177]
[178] Sahihu ibn hibban, mujalladi na 12, shafi na 168, lambar hadisi na 5348
Suratu shura ayata 21 [179]
Suraun nahli ayata 126 [180]
Suratun nur ayata 22 [181]
Suratu shura ayata 20 [182]
Suratul bakara ayata 256 [183]
Sahihul buhari, mujalladi na 6, shafi na 2537, lambar hadisi na 6524 [184]
Suratun nisa'I ayata 137 [185]
Suraun nisa'I ayata 137 [186]
Nadwat ilmiyya haula shari'atul islamiyya wa hukukul insan fil islam, bairut darul kutub al lubnani 1973 miladiyya[187]
Suratun nisa'I ayata 219 [188]
Suratun nisa'I ayata 36 [189]
Sahihul buhari, juzu'I na 2, shafi na 901, lambar hadisi na 2414 [190]
Suratun nisa'I ayata 92 [191]
Suratul mujadala ayata 3 [192]
Suratul ma'ida ayata 89[193]
Sahihul buhari, mujalladi na 2, shafi na 684, lambar hadisin na 1834 [194]
Suratul balad ayata 14-11 [195]
Sahihu muslim, mujalladi na 2, shafi na 1147, lambar hadisi na 1509 [196]
Suratu tauba ayata 60 [197]
Suratun nur ayata 32 [198]
Kotabul islam wa hukukul insan, na dakta Abdullahi bn Abdul muhsin al turky [199]
Dabarani da abun dunya ne suka rawaito shi kuma Albany ya inganta shi cikin littafin sahihul jami'u[200]